কুরআনুল কারীমের অর্থসমূহের অনুবাদ - হাউসা ভাষায় অনুবাদ- আবূ বকর জুমী * - অনুবাদসমূহের সূচী

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

অর্থসমূহের অনুবাদ সূরা: সূরা আন-নিসা   আয়াত:

Suratu Al'nisaa

يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَخَلَقَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَبَثَّ مِنۡهُمَا رِجَالٗا كَثِيرٗا وَنِسَآءٗۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِي تَسَآءَلُونَ بِهِۦ وَٱلۡأَرۡحَامَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَيۡكُمۡ رَقِيبٗا
Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta.* Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.
* Bin Allah Wanda Ya halitta ku, kira ga tabbatar da tauhidin Ulũhiyya ne da Rubũbiyya. Fitar mutãne daga asali guda, wanda bãbu wani surki a cikinsa yana wajabtar da girman jinsin mutum, kõwane iri ne, kowane launi, kuma kõwace halitta yake ɗauke da ita.Tsõron Allah da tsaronSa a kan mutãne yana wajabtar da tsayãwa a cikin haddõdin sharĩ'arSa. Tsõron zumunta ko rantsuwa da ita yana wajabtar da tausayi da rahama a kan halittar Allah na kusa da na nesa. Hadĩsi ya nũna ba a yin rantsuwa da wanin Allah sabõda haka ma'anar aya itace, 'Ku ji tsõron Allah ku tsare mahaifa da zumunta!'.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَءَاتُواْ ٱلۡيَتَٰمَىٰٓ أَمۡوَٰلَهُمۡۖ وَلَا تَتَبَدَّلُواْ ٱلۡخَبِيثَ بِٱلطَّيِّبِۖ وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَهُمۡ إِلَىٰٓ أَمۡوَٰلِكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حُوبٗا كَبِيرٗا
Kuma ku bai wa marãyu dũkiyõyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau. Kuma kada ku ci dũkiyõyinsu zuwa ga dũkiyõyinku. Lalle shi, yã kasance zunubi ne mai girma.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا تُقۡسِطُواْ فِي ٱلۡيَتَٰمَىٰ فَٱنكِحُواْ مَا طَابَ لَكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ مَثۡنَىٰ وَثُلَٰثَ وَرُبَٰعَۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا تَعۡدِلُواْ فَوَٰحِدَةً أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَعُولُواْ
Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu,* to, (akwai yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.
* Asalin marãya shĩ ne yãron da bai balaga ba, kuma ubansa ya mutu. Amma a cikin ãya-Allah Yã sani-anã nufin dukkan mai rauni a cikin al'umma, wanda yake neman a tsare haƙƙin sa da Allah Ya ɗõra wa Musulmi su tsare. Sabõda haka Ya shãfe jawãbin sharaɗin kuma Ya fãra da hukunce-hukunce, a kan tafsĩlin yadda zã a tsare mãsu rauni a cikin al'umma. Ya fãra da mãta a wajen aure, adadinsu daga ɗaya zuwa huɗu, gwargwadon ƙarfin mutum da iyãwarsa ga tsaida ãdalci a gare su, kõ a tsakãninsu. Ãdalci na kwãna da ciyarwa da tufãtarwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَءَاتُواْ ٱلنِّسَآءَ صَدُقَٰتِهِنَّ نِحۡلَةٗۚ فَإِن طِبۡنَ لَكُمۡ عَن شَيۡءٖ مِّنۡهُ نَفۡسٗا فَكُلُوهُ هَنِيٓـٔٗا مَّرِيٓـٔٗا
Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin haɗiya.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَا تُؤۡتُواْ ٱلسُّفَهَآءَ أَمۡوَٰلَكُمُ ٱلَّتِي جَعَلَ ٱللَّهُ لَكُمۡ قِيَٰمٗا وَٱرۡزُقُوهُمۡ فِيهَا وَٱكۡسُوهُمۡ وَقُولُواْ لَهُمۡ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا
Kada ku bai wa wãwãye* dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu tsayuwa (ga gyãranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.
* Sa'an nan yadda ake riƙon dũkiyar wãwã wanda bai san yadda ake riƙon dũkiya ba, ko dã shĩ bãligi ne, yã yi aure, kuma ko da shĩ ne yake neman dũkiyarsa da kansa; kamar da ijãra. Wannan wata hanyace ta tsaron haƙƙin mãsu rauni.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱبۡتَلُواْ ٱلۡيَتَٰمَىٰ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغُواْ ٱلنِّكَاحَ فَإِنۡ ءَانَسۡتُم مِّنۡهُمۡ رُشۡدٗا فَٱدۡفَعُوٓاْ إِلَيۡهِمۡ أَمۡوَٰلَهُمۡۖ وَلَا تَأۡكُلُوهَآ إِسۡرَافٗا وَبِدَارًا أَن يَكۡبَرُواْۚ وَمَن كَانَ غَنِيّٗا فَلۡيَسۡتَعۡفِفۡۖ وَمَن كَانَ فَقِيرٗا فَلۡيَأۡكُلۡ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِذَا دَفَعۡتُمۡ إِلَيۡهِمۡ أَمۡوَٰلَهُمۡ فَأَشۡهِدُواْ عَلَيۡهِمۡۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ حَسِيبٗا
Kuma ku jarraba marãyu, har a lõkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyõyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma da gaggawa kãfin su girma. Kuma wanda yake wadãtacce, to, ya kãma kãnsa, kuma wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu dũkiyõyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike.
আরবি তাফসীরসমূহ:
لِّلرِّجَالِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ وَلِلنِّسَآءِ نَصِيبٞ مِّمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَ مِمَّا قَلَّ مِنۡهُ أَوۡ كَثُرَۚ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا
Maza suna da rabo* daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke.
* Hukunce-hukuncen rabon gãdo, hanya ce ta tsaron haƙƙin mãsu rauni.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِذَا حَضَرَ ٱلۡقِسۡمَةَ أُوْلُواْ ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينُ فَٱرۡزُقُوهُم مِّنۡهُ وَقُولُواْ لَهُمۡ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا
Kuma idan ma'abũta zumunta da marãyu da matalauta suka halarci rabon, to, ku azurta su daga gare shi, kuma ku faɗa musu magana sananniya ta alhẽri.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلۡيَخۡشَ ٱلَّذِينَ لَوۡ تَرَكُواْ مِنۡ خَلۡفِهِمۡ ذُرِّيَّةٗ ضِعَٰفًا خَافُواْ عَلَيۡهِمۡ فَلۡيَتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلۡيَقُولُواْ قَوۡلٗا سَدِيدًا
Kuma waɗanda suke dã sun bar* zuriyya mãsu rauni a bãyansu, zã su ji tsõro a kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana madaidaiciya.
* Watau yadda mutum mai ƙanãnan 'ya'ya yake tsõron ya mutu ya bar su bãbu wata dũkiya da zã ta taimake su, haka kuma su Musulmi waɗanda aka sanya aikin rabon gãdo a hannunsu, su yi tunani, dã su ne suka mutu suka bar 'ya'yansu haka. Sabõda haka wannan zai karya zũciyar mai son ya yi zãlunci daga dũkiyar marãyu.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلۡيَتَٰمَىٰ ظُلۡمًا إِنَّمَا يَأۡكُلُونَ فِي بُطُونِهِمۡ نَارٗاۖ وَسَيَصۡلَوۡنَ سَعِيرٗا
Lalle ne, waɗanda suke cĩn dũkiyar marãyu da zãlunci, to, wuta kawai suke ci a cikin jikkunansu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يُوصِيكُمُ ٱللَّهُ فِيٓ أَوۡلَٰدِكُمۡۖ لِلذَّكَرِ مِثۡلُ حَظِّ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۚ فَإِن كُنَّ نِسَآءٗ فَوۡقَ ٱثۡنَتَيۡنِ فَلَهُنَّ ثُلُثَا مَا تَرَكَۖ وَإِن كَانَتۡ وَٰحِدَةٗ فَلَهَا ٱلنِّصۡفُۚ وَلِأَبَوَيۡهِ لِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُ مِمَّا تَرَكَ إِن كَانَ لَهُۥ وَلَدٞۚ فَإِن لَّمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلَدٞ وَوَرِثَهُۥٓ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ ٱلثُّلُثُۚ فَإِن كَانَ لَهُۥٓ إِخۡوَةٞ فَلِأُمِّهِ ٱلسُّدُسُۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصِي بِهَآ أَوۡ دَيۡنٍۗ ءَابَآؤُكُمۡ وَأَبۡنَآؤُكُمۡ لَا تَدۡرُونَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ لَكُمۡ نَفۡعٗاۚ فَرِيضَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu. Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi (ɗaya daga cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ وَلَكُمۡ نِصۡفُ مَا تَرَكَ أَزۡوَٰجُكُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهُنَّ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَهُنَّ وَلَدٞ فَلَكُمُ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡنَۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصِينَ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٖۚ وَلَهُنَّ ٱلرُّبُعُ مِمَّا تَرَكۡتُمۡ إِن لَّمۡ يَكُن لَّكُمۡ وَلَدٞۚ فَإِن كَانَ لَكُمۡ وَلَدٞ فَلَهُنَّ ٱلثُّمُنُ مِمَّا تَرَكۡتُمۚ مِّنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ تُوصُونَ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٖۗ وَإِن كَانَ رَجُلٞ يُورَثُ كَلَٰلَةً أَوِ ٱمۡرَأَةٞ وَلَهُۥٓ أَخٌ أَوۡ أُخۡتٞ فَلِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُۚ فَإِن كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِن ذَٰلِكَ فَهُمۡ شُرَكَآءُ فِي ٱلثُّلُثِۚ مِنۢ بَعۡدِ وَصِيَّةٖ يُوصَىٰ بِهَآ أَوۡ دَيۡنٍ غَيۡرَ مُضَآرّٖۚ وَصِيَّةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَلِيمٞ
Kuma kunã da rabin abin da mãtanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kunã da rubu'i (ɗaya daga cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bãyan wasiyya wadda suka yi kõ kuma bãshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sunã da sumuni (ɗaya daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bãyan wasiyya wadda kuka yi kõ kuwa bãshi. Idan wani namiji ya kasance ana gãdon sa bisa kalãla, ko kuwa wata mace alhãli kuwa yana da ɗan'uwa kõ 'yar'uwa* to, kõwane ɗaya daga cikinsu yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa daga wannan, to, sũ abõkan tãrayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bãyan wasiyya wadda aka yi kõ kuma bãshi. Bã da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri.
* Ɗan'uwa kõ 'yar'uwa, a nan,ana nufin li'ummi kõ li'ummiya, kõwane ɗayansu yana da sudusi; idan sunã da yawa, watau sun kai biyu kõ abin da ya fi biyu, to, suna da sulusi. Babu bambanci tsakanin namiji da mace gare su, dõmin jihar gadonsu mace ce,watau uwar mamacin.
আরবি তাফসীরসমূহ:
تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Waɗancan iyãkõkin Allah ne. Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da Manzon Sa, (Allah) zai shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُۥ يُدۡخِلۡهُ نَارًا خَٰلِدٗا فِيهَا وَلَهُۥ عَذَابٞ مُّهِينٞ
Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da Manzon Sa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkin Sa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱلَّٰتِي يَأۡتِينَ ٱلۡفَٰحِشَةَ مِن نِّسَآئِكُمۡ فَٱسۡتَشۡهِدُواْ عَلَيۡهِنَّ أَرۡبَعَةٗ مِّنكُمۡۖ فَإِن شَهِدُواْ فَأَمۡسِكُوهُنَّ فِي ٱلۡبُيُوتِ حَتَّىٰ يَتَوَفَّىٰهُنَّ ٱلۡمَوۡتُ أَوۡ يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلٗا
Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nẽmi Shaidar mutãne huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su.*
* Ãyõyi na 15 da l6 an shãfe hukuncinsu wajen haddi da ãyar sũratun Nũr ta biya da Hadisin Rajami ga zawari da zawara waɗanda suka yi zina, kuma da bũlãla ɗari dakõrar babane namiji, da kuma bũlãla ɗari ga budurwa. Kuma ana jefe mai liwãɗi da wanda ake yi a kansa idan sun balaga, ko dã su banãwa ne. Ana ladabi ga mailiwãɗi da matãrsa, amma ba a kashe shi. Liwãɗi da wata mace kamar zina yake ga namijin.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱلَّذَانِ يَأۡتِيَٰنِهَا مِنكُمۡ فَـَٔاذُوهُمَاۖ فَإِن تَابَا وَأَصۡلَحَا فَأَعۡرِضُواْ عَنۡهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ تَوَّابٗا رَّحِيمًا
Kuma waɗanda (mazã biyu) suka je mata* daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan idan sun tũba kuma suka kyautata hãlãyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu. Lalle ne Allah Yã kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai
* Maza biyu mãsu je wa alfasha su ne mãsu yin liwãɗi da jũnansu.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّمَا ٱلتَّوۡبَةُ عَلَى ٱللَّهِ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ يَتُوبُونَ مِن قَرِيبٖ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَتُوبُ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatãwar mugun aiki da jãhilci sa'an nan su tũba nan kusa* to, waɗannan Allah Yanã karɓar tũ barsu kuma Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
* Nan kusa, watau a gabãnin mutuwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَيۡسَتِ ٱلتَّوۡبَةُ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ حَتَّىٰٓ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ إِنِّي تُبۡتُ ٱلۡـَٰٔنَ وَلَا ٱلَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمۡ كُفَّارٌۚ أُوْلَٰٓئِكَ أَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا
Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tũba yanzu," kuma bã tũba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَرِثُواْ ٱلنِّسَآءَ كَرۡهٗاۖ وَلَا تَعۡضُلُوهُنَّ لِتَذۡهَبُواْ بِبَعۡضِ مَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَعَاشِرُوهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ فَإِن كَرِهۡتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰٓ أَن تَكۡرَهُواْ شَيۡـٔٗا وَيَجۡعَلَ ٱللَّهُ فِيهِ خَيۡرٗا كَثِيرٗا
Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da wata alfãsha* bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa.
* Mugun halin da sharĩ'a ba ta yarda da shi ba kamar ƙiyokõ yãwon banza, a nan bãbu laifi ku hana su aure sai sun yi muku hul'i, kuma Allah Yã hana gãdon mãta kamar dũkiya. Sun kasance sunã yin haka, ba da sãke bayar da sadaki ba, domin dogara da wanda ubansa ya bãyar, sai su aurar da ita a kan haka ga wani ɗan'uwan mamacin, kõ kuma wanda suke so ya aure ta.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِنۡ أَرَدتُّمُ ٱسۡتِبۡدَالَ زَوۡجٖ مَّكَانَ زَوۡجٖ وَءَاتَيۡتُمۡ إِحۡدَىٰهُنَّ قِنطَارٗا فَلَا تَأۡخُذُواْ مِنۡهُ شَيۡـًٔاۚ أَتَأۡخُذُونَهُۥ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا
Kuma idan kun yi nufin musanya mãta a matsayin wata mãta, alhãli kuwa kun bai wa ɗayarsu ƙinɗari* to kada ku karɓi kõme daga gare, shi, shin, zã ku karɓe shi da ƙarya da zunubi bãyyananne?
* Ƙinɗãri, shi ne dũkiya mai yawa; ũƙiyya dubu gõma sha biyu, na azurfa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَكَيۡفَ تَأۡخُذُونَهُۥ وَقَدۡ أَفۡضَىٰ بَعۡضُكُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ وَأَخَذۡنَ مِنكُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا
Kuma yãyã zã ku karɓe shi alhãli kuwa, haƙĩƙa, sãshenku yã sãdu zuwa ga sãshe, kuma sun riƙi alkawari* mai kauri daga gare ku?
* Alkawarin riƙonsu da alheri ko kuma sallamarsu da kyautatãwa. Baƙara Ãya ta 231.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَا تَنكِحُواْ مَا نَكَحَ ءَابَآؤُكُم مِّنَ ٱلنِّسَآءِ إِلَّا مَا قَدۡ سَلَفَۚ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَمَقۡتٗا وَسَآءَ سَبِيلًا
Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfãsha da abin ƙyãma. Kuma ya mũnana ya zama hanya.
আরবি তাফসীরসমূহ:
حُرِّمَتۡ عَلَيۡكُمۡ أُمَّهَٰتُكُمۡ وَبَنَاتُكُمۡ وَأَخَوَٰتُكُمۡ وَعَمَّٰتُكُمۡ وَخَٰلَٰتُكُمۡ وَبَنَاتُ ٱلۡأَخِ وَبَنَاتُ ٱلۡأُخۡتِ وَأُمَّهَٰتُكُمُ ٱلَّٰتِيٓ أَرۡضَعۡنَكُمۡ وَأَخَوَٰتُكُم مِّنَ ٱلرَّضَٰعَةِ وَأُمَّهَٰتُ نِسَآئِكُمۡ وَرَبَٰٓئِبُكُمُ ٱلَّٰتِي فِي حُجُورِكُم مِّن نِّسَآئِكُمُ ٱلَّٰتِي دَخَلۡتُم بِهِنَّ فَإِن لَّمۡ تَكُونُواْ دَخَلۡتُم بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ وَحَلَٰٓئِلُ أَبۡنَآئِكُمُ ٱلَّذِينَ مِنۡ أَصۡلَٰبِكُمۡ وَأَن تَجۡمَعُواْ بَيۡنَ ٱلۡأُخۡتَيۡنِ إِلَّا مَا قَدۡ سَلَفَۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mãtã, da goggonninku, da innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma, da 'yan'uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi* a kanku, da mãtan 'yã'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
* Ɗaurin aure a kan ɗiya yana haramta uwarta, amma ɗaurin aure a kan uwa,bã ya haramta ɗiyar sai in an yi duhũli da ita, kõ kuma an yi tamattu'i da ita.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ وَٱلۡمُحۡصَنَٰتُ مِنَ ٱلنِّسَآءِ إِلَّا مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۖ كِتَٰبَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ وَأُحِلَّ لَكُم مَّا وَرَآءَ ذَٰلِكُمۡ أَن تَبۡتَغُواْ بِأَمۡوَٰلِكُم مُّحۡصِنِينَ غَيۡرَ مُسَٰفِحِينَۚ فَمَا ٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِهِۦ مِنۡهُنَّ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةٗۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا تَرَٰضَيۡتُم بِهِۦ مِنۢ بَعۡدِ ٱلۡفَرِيضَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Da tsararrun auren* wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya** da shi a bãyan farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
* An haramta muku matan auren wasu maza, matuƙar mazansu ba su sake su ba, Musulmi ne kõ kuwa Kitãbãwa, sai fa idan kun kãmo su ne daga ƙasar da take ta abõkan gaba, a nan kunã iya tãkinsu haka, dõmin kãmu yã warware aurensu. Idan kun yi tamattu'ida wasu mãtã a kan kuskure, ba da aure ba, sai ku biya su sadãki a kan haka. An hana auren tamattu'i, watau yin aure zuwa ga ajali. Abdullahi bn Abbas ya ce yin sa yã fi zina. ** Bãyan sadãkin da aka yanka bãbu laifi ĩdan kun yi yardatayya da ƙãra wani abu a kan farilla, kuma bãbu laifi idan ita matar tã yarda da kãyar da ƙarin kõ kuwa shĩ mijin ya yarda da biyan ƙãrin.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن لَّمۡ يَسۡتَطِعۡ مِنكُمۡ طَوۡلًا أَن يَنكِحَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ فَمِن مَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُم مِّن فَتَيَٰتِكُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۚ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِإِيمَٰنِكُمۚ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۚ فَٱنكِحُوهُنَّ بِإِذۡنِ أَهۡلِهِنَّ وَءَاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِ مُحۡصَنَٰتٍ غَيۡرَ مُسَٰفِحَٰتٖ وَلَا مُتَّخِذَٰتِ أَخۡدَانٖۚ فَإِذَآ أُحۡصِنَّ فَإِنۡ أَتَيۡنَ بِفَٰحِشَةٖ فَعَلَيۡهِنَّ نِصۡفُ مَا عَلَى ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ مِنَ ٱلۡعَذَابِۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَشِيَ ٱلۡعَنَتَ مِنكُمۡۚ وَأَن تَصۡبِرُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Kuma wanda* bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya aura) daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga** sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
* Hukunce-hukuncen auren kuyanga ga wanda bai sãmi ĩkon auren'ya ba. Aibin auren kuyangi shi ne bautar da zuriya, domin bauta daga uwa take. Saboda haka bã ya halatta ga Musulmi ya auri baiwar kafiri, kome larurar da take ciki,sai dai ya saye ta daga gare shi. . **Ku duka daidai kukewajen ĩmãni da Musulunci. Dubi kuma Ãli'Imrãna 195.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُبَيِّنَ لَكُمۡ وَيَهۡدِيَكُمۡ سُنَنَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَيَتُوبَ عَلَيۡكُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Allah Yanã nufin Ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyõyin waɗanda suke a gabãninku kuma Ya karɓi tũbanku. Kuma Allah Masani ne Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱللَّهُ يُرِيدُ أَن يَتُوبَ عَلَيۡكُمۡ وَيُرِيدُ ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلشَّهَوَٰتِ أَن تَمِيلُواْ مَيۡلًا عَظِيمٗا
Kuma Allah Yanã nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha'awõyi suna nufin ku karkata, karkata mai girma.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُخَفِّفَ عَنكُمۡۚ وَخُلِقَ ٱلۡإِنسَٰنُ ضَعِيفٗا
Allah Yana nufin Ya yi muku sauƙi, kuma an halitta mutum yana mai rauni.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً عَن تَرَاضٖ مِّنكُمۡۚ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara*, fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne.
* Hukuncin cin dukiyar mutane da ƙarya ko yaudara, haramun ne, domin yana kai ga mutane su kashe kansu.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ عُدۡوَٰنٗا وَظُلۡمٗا فَسَوۡفَ نُصۡلِيهِ نَارٗاۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرًا
Wanda ya aikata wancan bisa ta'adi da zãlunci, to, zã Mu ƙõne shi da Wuta. Kuma wannan yã kasance ga Allah (abu ne) mai sauƙi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِن تَجۡتَنِبُواْ كَبَآئِرَ مَا تُنۡهَوۡنَ عَنۡهُ نُكَفِّرۡ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَنُدۡخِلۡكُم مُّدۡخَلٗا كَرِيمٗا
Idan kuka nĩsanci manyan abubuwan da ake hana ku aikatãwa, to, zã Mu kankare mũnanan ayyukanku daga gare ku, kuma Mu shigar da ku mashiga ta karimci.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَا تَتَمَنَّوۡاْ مَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بِهِۦ بَعۡضَكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ لِّلرِّجَالِ نَصِيبٞ مِّمَّا ٱكۡتَسَبُواْۖ وَلِلنِّسَآءِ نَصِيبٞ مِّمَّا ٱكۡتَسَبۡنَۚ وَسۡـَٔلُواْ ٱللَّهَ مِن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا
Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sãshenku da shi a kan sãshe; maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mãtã suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku rõƙi Allah daga falalar Sa. Lalle ne Allah Yã kasance ga dukkan kõme, Masani.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلِكُلّٖ جَعَلۡنَا مَوَٰلِيَ مِمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَۚ وَٱلَّذِينَ عَقَدَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ فَـَٔاتُوهُمۡ نَصِيبَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدًا
Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla* ku bã su rabonsu. Lalle ne, Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci.
* A zãmanin Jahiliyya ana ƙullin amana a tsakanin ƙabilu ko a tsakanin mutum da wani mutum. Wannan ƙullin amãnar yakan haɗa har da sudusin dukiyar wanda ya mutu daga cikinsu. Wasu Musulmi sun shiga Musulunci a bãyan sun ƙulla irin wannan amãnar sabõda haka Allah Ya yi umurni da cika wannan alkawarin, kuma Ya kashe al'adar, Ya musanya ta da hukunce-hukuncen Musulunci. Kuma ana fassara masu ƙullin rantsuwa da masu gudãnar da aikin rabon dũkiyar gãdo. Ana biyan su ijãrar wahalarsu daga kãwunan magãda kamar yadda ya kamata.
আরবি তাফসীরসমূহ:
ٱلرِّجَالُ قَوَّٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ وَبِمَآ أَنفَقُواْ مِنۡ أَمۡوَٰلِهِمۡۚ فَٱلصَّٰلِحَٰتُ قَٰنِتَٰتٌ حَٰفِظَٰتٞ لِّلۡغَيۡبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُۚ وَٱلَّٰتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهۡجُرُوهُنَّ فِي ٱلۡمَضَاجِعِ وَٱضۡرِبُوهُنَّۖ فَإِنۡ أَطَعۡنَكُمۡ فَلَا تَبۡغُواْ عَلَيۡهِنَّ سَبِيلًاۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيّٗا كَبِيرٗا
Maza mãsu tsayuwa ne* a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.
* Allah Ya sanya shugabancin gida da gudanar da tasarrufinsa a hannuwan maza domin ginar jikinsu, da hankalinsu da kuma dukiyarsu da suke ciyarwa ga sadãki da kuma nafaƙar (ciyarwar) gidan. Kuma Allah Ya aza wa mãta ɗa'a ga maza da kuma tsare farjojinsu domin kada su kawo wani baƙon da ba ɗan gida ba, a cikin gidan.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِنۡ خِفۡتُمۡ شِقَاقَ بَيۡنِهِمَا فَٱبۡعَثُواْ حَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهِۦ وَحَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهَآ إِن يُرِيدَآ إِصۡلَٰحٗا يُوَفِّقِ ٱللَّهُ بَيۡنَهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرٗا
Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta*. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.
* Hakamãni, ko masu sulhu biyu, su tafi su yi binciken abin da ya hana auren kyau, su tsawaci maras gaskiya daga cikin ma'auran, ko kuma su hukunta rabuwa da hul'i, ko ba da hul'i ba. Abin da suka hukunta alƙãlĩ ya zartar da shi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ وَٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗا وَبِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱلۡجَارِ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡجَارِ ٱلۡجُنُبِ وَٱلصَّاحِبِ بِٱلۡجَنۢبِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ وَمَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ مُخۡتَالٗا فَخُورًا
Kuma ku bauta wa *Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta, da maƙwabci ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin da hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance mai tãƙama, mai yawan alfahari.
* Bauta wa Allah shi ne a bi umurninsa, a bar haninsa a kome. Sa'an nan ya biyar da nau'ukan mutane waɗanda mutum zai yi ihsani zuwa gare su gwargwadon darajarsu kuma da halinsa. Sa'an nan zargi a kan marowaci da sakamakonsa, da mai ciyarwa amma ba a bisa hanyar bauta wa Allah ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ وَيَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبُخۡلِ وَيَكۡتُمُونَ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا
Waɗanda suke yin rõwa, kuma sunã umurnin mutãne da yin rõwa, kuma suna ɓõyewar abin da Allah Ya bã su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, sabõda kãfirai, azãba mai walãkantarwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَا بِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ وَمَن يَكُنِ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَهُۥ قَرِينٗا فَسَآءَ قَرِينٗا
Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu dõmin nũna wa mutãne, kuma bã su yin ĩmãni da Allah, kuma bã su yin ĩmãnida Rãnar Lãhira kuma wanda Shaiɗan ya kasance abõkin haɗi a gare shi, to, yã mũnana ga abõkinhaɗi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَاذَا عَلَيۡهِمۡ لَوۡ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقَهُمُ ٱللَّهُۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِهِمۡ عَلِيمًا
Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmãni da Allah, kumada Rãnar Lãhira, kuma sun ciyar da abin da Allah Yã azurtã su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani?
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظۡلِمُ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖۖ وَإِن تَكُ حَسَنَةٗ يُضَٰعِفۡهَا وَيُؤۡتِ مِن لَّدُنۡهُ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Lalle ne, Allah bã Ya zãluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alhẽri ce, zai riɓanya ta, kuma Ya kãwo daga gunsa ijãra mai girma.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَكَيۡفَ إِذَا جِئۡنَا مِن كُلِّ أُمَّةِۭ بِشَهِيدٖ وَجِئۡنَا بِكَ عَلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِ شَهِيدٗا
To, yãyã, idan Mun zo da shaidu daga dukkan al'umma, kuma Muka zo da kai a kan waɗannan, kana mai shaida!
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَوۡمَئِذٖ يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَعَصَوُاْ ٱلرَّسُولَ لَوۡ تُسَوَّىٰ بِهِمُ ٱلۡأَرۡضُ وَلَا يَكۡتُمُونَ ٱللَّهَ حَدِيثٗا
A rãnar nan, waɗanda suka kãfirta kuma suka sãɓã wa Manzo, sunã gũrin dã an baje ƙasa dasu, kuma bã su ɓõye wa Allah wani labãri.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡرَبُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنتُمۡ سُكَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَعۡلَمُواْ مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغۡتَسِلُواْۚ وَإِن كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوۡ جَآءَ أَحَدٞ مِّنكُم مِّنَ ٱلۡغَآئِطِ أَوۡ لَٰمَسۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمۡ تَجِدُواْ مَآءٗ فَتَيَمَّمُواْ صَعِيدٗا طَيِّبٗا فَٱمۡسَحُواْ بِوُجُوهِكُمۡ وَأَيۡدِيكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye*, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku.** Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.
* A lokacin ba a hana shan giya ba. Sa'an nan aka hana ta da ayar Suratul Ma'idah ta 90. Mai janaba kuma ba ya yin salla kuma ba ya shiga masallaci sai ya yi wanka ko taimama, sai dai yana iya shiga da niyyar wucewa daga ƙõfa zuwa ga wata, ko kuwa ya shiga ya ɗebo ruwa ya fita. Ana yin taimama saboda rashin ruwa haƙiƙatan, ko ma'anan, kamar mai rashin lafiya. Shafar mace na karya alwala, amma ba ya sabbaba wanka idan an yi shafar da niyyar jin dãɗi ko kuma an sami jin dãɗin ba da nufi ba. Mai shafar da wanda aka shafa duka ɗaya suke.** Wãtau ku yi taimama sabõda rashin ruwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ نَصِيبٗا مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ يَشۡتَرُونَ ٱلضَّلَٰلَةَ وَيُرِيدُونَ أَن تَضِلُّواْ ٱلسَّبِيلَ
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo daga Littafi, suna sayen ɓata, kuma suna nẽman ku ɓace daga hanya?
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِأَعۡدَآئِكُمۡۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَلِيّٗا وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ نَصِيرٗا
Kuma Allah ne Mafi sani ga maƙiyanku, kuma Allah Yã isa Ya zama Majibinci, kuma Yã isa Ya zama Mataimaki.
আরবি তাফসীরসমূহ:
مِّنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْ يُحَرِّفُونَ ٱلۡكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِۦ وَيَقُولُونَ سَمِعۡنَا وَعَصَيۡنَا وَٱسۡمَعۡ غَيۡرَ مُسۡمَعٖ وَرَٰعِنَا لَيَّۢا بِأَلۡسِنَتِهِمۡ وَطَعۡنٗا فِي ٱلدِّينِۚ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ قَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَا وَٱسۡمَعۡ وَٱنظُرۡنَا لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡ وَأَقۡوَمَ وَلَٰكِن لَّعَنَهُمُ ٱللَّهُ بِكُفۡرِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُونَ إِلَّا قَلِيلٗا
Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sunã karkatar da magana daga wurãrenta suna cẽwa: "Munjiya* kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa, kuma rã'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," dõmin karkatarwa da harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: "Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana," haƙĩƙa, dã ya kasance mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan.
* Yahudu, ana kiran su da maganar Mũsa da ya ce wa Ubangiji, ‘Mun tuba zuwa gare Ka, yã Allah,’ (A’ãrãf, ãyã ta 155) dõmin izgili da suke yi na ƙin bin haddõdin Allah. Sunã karkatar da magana da asalin ma’anarta zuwa ga wata ma’ana ta izgili, sunã céwa ‘Mun ji’ amma aikinsu yanã nuna céwa, ‘Sun ƙi’ suke nufi. Kuma ‘Ka jiya a wanin wurin jiyãwa’ addu’a ce mai ɗaukar ma’anar alhẽri da ma’anar sharri, su kuwa sunã nufin ta sharrin. Haka kalmar ‘rã‘ina’ tanã da ma’anar ‘tsãre mu’ ko ‘saurãra mana’, kuma tanã da ma’anar ‘Yã ruɓaɓɓe'. Sunã nufin ma’anar ƙarshen. Wannan bayãni’ shi ma taimako ne ga Musulmi mãsu raunin hankali dõmin a tsare musu addininsu kamar yadda ake tsaron dũkiyarsu. An cũsa irin wannan mãkirci a wata addu’a da suke cewa ‘Jauharatul Kamãli’ inda suka sifanta wanda suke yi wa salãti da “asƙam” mafi cũta. Wannan tã yi daidai da kalmar rã’ina, ko ma ta fi mũni, dõmin rã’ina tanã da wata ma’ana ta yabo, amma asƙam bã ta da wata ma'ana sai ta zãgi kawai. Allah Ya tsare mu daga sharrin maƙiyan addini.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ ءَامِنُواْ بِمَا نَزَّلۡنَا مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَكُم مِّن قَبۡلِ أَن نَّطۡمِسَ وُجُوهٗا فَنَرُدَّهَا عَلَىٰٓ أَدۡبَارِهَآ أَوۡ نَلۡعَنَهُمۡ كَمَا لَعَنَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلسَّبۡتِۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ مَفۡعُولًا
Yã kũ waɗanda aka bai wa Littãfi! Ku yi ĩmãni da abinda Muka saukar, yana mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, tun gabanin Mu shãfe wasu fuskõki, sa'an nan Mu mayar da su a kan bãyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatãwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱفۡتَرَىٰٓ إِثۡمًا عَظِيمًا
Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يُزَكُّونَ أَنفُسَهُمۚ بَلِ ٱللَّهُ يُزَكِّي مَن يَشَآءُ وَلَا يُظۡلَمُونَ فَتِيلًا
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ã'a, Allah ne Yake tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
ٱنظُرۡ كَيۡفَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۖ وَكَفَىٰ بِهِۦٓ إِثۡمٗا مُّبِينًا
Ka dũba yadda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah! Kuma shi ya isa ga zama zunubi bayyananne.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ نَصِيبٗا مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡجِبۡتِ وَٱلطَّٰغُوتِ وَيَقُولُونَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ هَٰٓؤُلَآءِ أَهۡدَىٰ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ سَبِيلًا
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabõ da ga Littafi suna ĩmãni da gunki da Shaiɗan* kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kãfirta: "Waɗannan ne mafiya shiriya daga waɗanda suka yi ĩmãni ga hanya"?
* Jibti sunan kowane gunki ne.Ɗãgũtu sunan Shaiɗan ne mai ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, sheɗãnin da yake zama tare da gumãka ko waninsu, mutum ne ko aljani, dõmin ya ɓatar da mãsu raunin hankali, a cikin Yahũdu ko a cikin Musulmi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُۖ وَمَن يَلۡعَنِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ نَصِيرًا
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bã zã ka sãmi mataimaki a gare shi ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَمۡ لَهُمۡ نَصِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُلۡكِ فَإِذٗا لَّا يُؤۡتُونَ ٱلنَّاسَ نَقِيرًا
Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa'an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin gurtsun dabino ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَمۡ يَحۡسُدُونَ ٱلنَّاسَ عَلَىٰ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۖ فَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ ءَالَ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَءَاتَيۡنَٰهُم مُّلۡكًا عَظِيمٗا
Ko suna hãsadar mutãne* ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalar Sa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.
* Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah sun tabbata agare shi. An ce masa ɗan gidan Ibrahim domin Yahũdu su san shi ba kasasshe ba ne ga dangantaka, daga gare su. Kuma bai fita ba daga tsãrin cewa Annabãwa mãsu Littãfi a bãyan Ibrãhĩm, daga zuriyarsa za su fito. Kuma sun san wannan a cikin littãfinsu, watau Attaura.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَمِنۡهُم مَّنۡ ءَامَنَ بِهِۦ وَمِنۡهُم مَّن صَدَّ عَنۡهُۚ وَكَفَىٰ بِجَهَنَّمَ سَعِيرًا
To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا سَوۡفَ نُصۡلِيهِمۡ نَارٗا كُلَّمَا نَضِجَتۡ جُلُودُهُم بَدَّلۡنَٰهُمۡ جُلُودًا غَيۡرَهَا لِيَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَزِيزًا حَكِيمٗا
Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ سَنُدۡخِلُهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَنُدۡخِلُهُمۡ ظِلّٗا ظَلِيلًا
Kuma waɗanda suka ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تُؤَدُّواْ ٱلۡأَمَٰنَٰتِ إِلَىٰٓ أَهۡلِهَا وَإِذَا حَكَمۡتُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ أَن تَحۡكُمُواْ بِٱلۡعَدۡلِۚ إِنَّ ٱللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِۦٓۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا
Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ.* Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani.
* Talakãwa mutãne ne mãsu rauni a cikin hannuwan shugabanninsu. Su da dukiyarsu amãnõni ne na Allah a cikin hannuwan shugabanni, saboda haka tsaronsu da dukiyarsu, gwargwadon shari'a, da yin hukunci a tsakaninsu da ãdalci, bãyar da amãna ne ga mãsu ita.Wanda ya bi son zuciyarsa duka ga ɗayan waɗannan abũbuwa, to, yã yi yaudara ga Allah ke nan. Allah kuma zai kama shi da hukuncin mayaudari.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا
Yã kũ waɗanda suka ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku.* Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzon Sa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
* Haka su kuma mutãne talakãwa, amãna ce a kansu su yarda da hukuncin Allah da Manzonsa, a kome na al'amurransu da mu'ãmalõlinsu. Kuma wãjibi ne a kansu su yarda da abin da aka hukunta a kansu daidai da sharĩ'ar Allah. Su kuma idan sun sãɓa, to, sun yaudari amãnar Allah ke nan.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يَزۡعُمُونَ أَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوٓاْ إِلَى ٱلطَّٰغُوتِ وَقَدۡ أُمِرُوٓاْ أَن يَكۡفُرُواْ بِهِۦۖ وَيُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُضِلَّهُمۡ ضَلَٰلَۢا بَعِيدٗا
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra zuwa ga ¦ãgũtu* alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.
* Ɗãgũtu shi ne dukan mai yin dõkõki waɗanda ba dõkõkin Allah ba. Dukan wanda ya bi dõka wadda ba ta Allah ba a cikin ibãda, ko wadda ta saɓa wa haddin Allah a cikin mu'ãmalõli na haƙƙõƙi ko na laifuka, to, ya shiga cikin wannan tarkon.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَإِلَى ٱلرَّسُولِ رَأَيۡتَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ يَصُدُّونَ عَنكَ صُدُودٗا
Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo" zã ka ga munãfukai* sunã kange mutãne daga gare ka, kangẽwa.
* Miyãgun shugabanni mãsu karkatar da mũminai daga hukuncin Allah da hujjar wai suna nufin su daidaita domin a haɗa Musulmi da kãfirai ga hukunci; ta haka har kãfiri ya kasance mai yin hukunci a kan Musulmi. Su waɗannan masu yin haka ba Musulmi ba ne, munãfukan Musulmi ne. Musuluncinsu na bãki ne kawai, dã yã kai ga zũciya dã ba su yi ko tunãnin yarda da haka ba. Allah Ya tsare mu daga sharrin Shaiɗan,.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَكَيۡفَ إِذَآ أَصَٰبَتۡهُم مُّصِيبَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ ثُمَّ جَآءُوكَ يَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ إِنۡ أَرَدۡنَآ إِلَّآ إِحۡسَٰنٗا وَتَوۡفِيقًا
To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, "Ba mu yi nufin kõme ba sai kyautatawa da daidaitãwa."?
আরবি তাফসীরসমূহ:
أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُ ٱللَّهُ مَا فِي قُلُوبِهِمۡ فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَعِظۡهُمۡ وَقُل لَّهُمۡ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ قَوۡلَۢا بَلِيغٗا
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ إِذ ظَّلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ جَآءُوكَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ ٱللَّهَ وَٱسۡتَغۡفَرَ لَهُمُ ٱلرَّسُولُ لَوَجَدُواْ ٱللَّهَ تَوَّابٗا رَّحِيمٗا
Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu,* sun zo maka sa'an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.
* Wanda ya ƙi hukuncin Allah, ya yi laifi biyu, domin sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wannan ya nũna rashin ĩmãninsa da Allah da Manzon Sa. Saboda haka ne ãyã mai bin wannan ta ce Musulmi bã su da ĩmãni sai sun yarda da Hukuncin Allah ga kome daga al'amurransu, kuma su yarda da hukuncinsa, bã da jin wani ƙunci a cikin zukatansu ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَرَجٗا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُواْ تَسۡلِيمٗا
To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَوۡ أَنَّا كَتَبۡنَا عَلَيۡهِمۡ أَنِ ٱقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ أَوِ ٱخۡرُجُواْ مِن دِيَٰرِكُم مَّا فَعَلُوهُ إِلَّا قَلِيلٞ مِّنۡهُمۡۖ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ فَعَلُواْ مَا يُوعَظُونَ بِهِۦ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡ وَأَشَدَّ تَثۡبِيتٗا
Kuma dã dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, "Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita daga gidãjenku," dã ba su aikata shi ba, fãce kaɗan daga gare su. Kuma dã dai lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِذٗا لَّأٓتَيۡنَٰهُم مِّن لَّدُنَّآ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Kuma a sa'an nan, haƙĩƙa, dã Mun bã su, lãda mai girma, daga gun Mu.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَهَدَيۡنَٰهُمۡ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا
Kuma lalle ne, dã Mun shiryar da su hanya madaidaiciya.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَٰٓئِكَ رَفِيقٗا
Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da masu shahãda* da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya.
* Darajar ɗaukaka ga addini shi ne zama Annabi sa'an nan siddĩƙ, watau manyan sahabban kowane Annabi. Waɗannan darajõji biyu yanzu an rufe su daga kõwa, dõmin bãbu sauran Annabci wanda yake tãre da siddĩƙanci. Ta uku ita ce shahãda watau a kashe mutum a wurin yãƙi dõmin ɗaukaka kalmar Allah da tsare haƙƙõƙin Musulmi. Wannan ita ce maƙasudin abin faɗa a nan, dõmin abin da sũrar ke karantarwa, kuma dõmin ya zama shimfiɗar magana a kan darajar jihãdi da amfanõninsa. Ta huɗu zama sãlihi mai son abin da Allah Yake so kuma mai ƙin abin da Allah Yake ƙi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
ذَٰلِكَ ٱلۡفَضۡلُ مِنَ ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ عَلِيمٗا
Waccan falalar daga Allah take, kuma Allah Yã isa zama Masani.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ خُذُواْ حِذۡرَكُمۡ فَٱنفِرُواْ ثُبَاتٍ أَوِ ٱنفِرُواْ جَمِيعٗا
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku riƙi shirinku* sa'an nan ku fitar da hari jama'a, jama'a ko ku fitar da yaƙi gaba ɗaya.
* Bã ya halatta Musulmi su zauna bãbu tattalin yãƙi da fitar da yãki ko hari a kan maƙiyansu, saboda abin da ke cikin wannan ãyar ta 71.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِنَّ مِنكُمۡ لَمَن لَّيُبَطِّئَنَّ فَإِنۡ أَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةٞ قَالَ قَدۡ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيَّ إِذۡ لَمۡ أَكُن مَّعَهُمۡ شَهِيدٗا
Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fãsarwa*. To idan wata masĩfa ta sãme ku, sai ya ce: "Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dõmin ban kasance mahalarci tãre da su ba."
* Siffar munãfuki ita ce ya ƙi fita zuwa yãƙi, kuma ya fãsar da waninsa, ya yi murnar hasãrar Musulmi, kuma ya yi baƙin cikin nasararsu, ya so a raba ganĩma da shi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَئِنۡ أَصَٰبَكُمۡ فَضۡلٞ مِّنَ ٱللَّهِ لَيَقُولَنَّ كَأَن لَّمۡ تَكُنۢ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُۥ مَوَدَّةٞ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ مَعَهُمۡ فَأَفُوزَ فَوۡزًا عَظِيمٗا
Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta sãme ku haƙĩƙa, tabbas, yanã cẽwa, kamar wata sõyayya ba ta kasance a tsakãninku da shi ba: "Yã kaitona! Dã na zama tãre da su dai, dõmin in rabonta da rabõ mai girma!"
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ فَلۡيُقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ يَشۡرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا بِٱلۡأٓخِرَةِۚ وَمَن يُقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَيُقۡتَلۡ أَوۡ يَغۡلِبۡ فَسَوۡفَ نُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lãhira su yi yãƙi, a cikin hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yãki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa ya rinjãya, sa'an nan zã Mu ba shi ijãra mai girma.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَا لَكُمۡ لَا تُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلۡمُسۡتَضۡعَفِينَ مِنَ ٱلرِّجَالِ وَٱلنِّسَآءِ وَٱلۡوِلۡدَٰنِ ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَآ أَخۡرِجۡنَا مِنۡ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلظَّالِمِ أَهۡلُهَا وَٱجۡعَل لَّنَا مِن لَّدُنكَ وَلِيّٗا وَٱجۡعَل لَّنَا مِن لَّدُنكَ نَصِيرًا
Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa."?
আরবি তাফসীরসমূহ:
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱلطَّٰغُوتِ فَقَٰتِلُوٓاْ أَوۡلِيَآءَ ٱلشَّيۡطَٰنِۖ إِنَّ كَيۡدَ ٱلشَّيۡطَٰنِ كَانَ ضَعِيفًا
Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta sunã yãƙi a cikin hanyar ¦ãgũtu (Shaiɗan). To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ قِيلَ لَهُمۡ كُفُّوٓاْ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُمۡ يَخۡشَوۡنَ ٱلنَّاسَ كَخَشۡيَةِ ٱللَّهِ أَوۡ أَشَدَّ خَشۡيَةٗۚ وَقَالُواْ رَبَّنَا لِمَ كَتَبۡتَ عَلَيۡنَا ٱلۡقِتَالَ لَوۡلَآ أَخَّرۡتَنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖۗ قُلۡ مَتَٰعُ ٱلدُّنۡيَا قَلِيلٞ وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّمَنِ ٱتَّقَىٰ وَلَا تُظۡلَمُونَ فَتِيلًا
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَيۡنَمَا تَكُونُواْ يُدۡرِككُّمُ ٱلۡمَوۡتُ وَلَوۡ كُنتُمۡ فِي بُرُوجٖ مُّشَيَّدَةٖۗ وَإِن تُصِبۡهُمۡ حَسَنَةٞ يَقُولُواْ هَٰذِهِۦ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةٞ يَقُولُواْ هَٰذِهِۦ مِنۡ عِندِكَۚ قُلۡ كُلّٞ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ فَمَالِ هَٰٓؤُلَآءِ ٱلۡقَوۡمِ لَا يَكَادُونَ يَفۡقَهُونَ حَدِيثٗا
"Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin gãnuwõyi ingãtattu!" Kuma idan wani alhẽri ya sãme su sai su ce: "Wannan daga wurin Allah ne," kuma idan wata cũta ta sãme su, sai su ce: "Wannan daga gare ka ne."Ka ce: "Dukkansu daga Allah ne." To, me ya sãmi waɗannan mutãne, bã su kusantar fahimtar magana?
আরবি তাফসীরসমূহ:
مَّآ أَصَابَكَ مِنۡ حَسَنَةٖ فَمِنَ ٱللَّهِۖ وَمَآ أَصَابَكَ مِن سَيِّئَةٖ فَمِن نَّفۡسِكَۚ وَأَرۡسَلۡنَٰكَ لِلنَّاسِ رَسُولٗاۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدٗا
Abin da ya sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutãne, (kana) Manzo, kuma Allah Yã isa ga zama shaida.
আরবি তাফসীরসমূহ:
مَّن يُطِعِ ٱلرَّسُولَ فَقَدۡ أَطَاعَ ٱللَّهَۖ وَمَن تَوَلَّىٰ فَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظٗا
Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah. Kuma wanda ya jũya bãya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَيَقُولُونَ طَاعَةٞ فَإِذَا بَرَزُواْ مِنۡ عِندِكَ بَيَّتَ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ غَيۡرَ ٱلَّذِي تَقُولُۖ وَٱللَّهُ يَكۡتُبُ مَا يُبَيِّتُونَۖ فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلًا
Kuma sunã cẽwa, "Dã'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwãna da niyyar wanin abin da take faɗa, alhãli kuwa Allah na rubũta abin da suke kwãna da niyyarsa. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dõgara ga Allah, kuma Allah Yã isa ya zama wakĩli.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلۡقُرۡءَانَۚ وَلَوۡ كَانَ مِنۡ عِندِ غَيۡرِ ٱللَّهِ لَوَجَدُواْ فِيهِ ٱخۡتِلَٰفٗا كَثِيرٗا
Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũnamai yawa?
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِذَا جَآءَهُمۡ أَمۡرٞ مِّنَ ٱلۡأَمۡنِ أَوِ ٱلۡخَوۡفِ أَذَاعُواْ بِهِۦۖ وَلَوۡ رَدُّوهُ إِلَى ٱلرَّسُولِ وَإِلَىٰٓ أُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنۡهُمۡ لَعَلِمَهُ ٱلَّذِينَ يَسۡتَنۢبِطُونَهُۥ مِنۡهُمۡۗ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَٱتَّبَعۡتُمُ ٱلشَّيۡطَٰنَ إِلَّا قَلِيلٗا
Kuma idan wani al'amari* daga aminci ko tsõro ya je musu, sai su wãtsa shi. Dã sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, zã su san shi. Kuma bã dõmin falalar Allah bã a kanku da rahamar Sa, haƙĩƙa, dã kun bi Shaiɗan fãce kaɗan.
* Umurnin al'umma da cewa idan sun ga wani al'amari daba su san kansa ba kõ kuwa idan wani abu na ban tsõro ya auku, to, haram ne su yi ta bãrãrarsa domin su firgitar da mutãne. Abin da yake wãjibi a kansu sa'an nan, shi ne su kai rahõtonsa ga shugabanni mãsu sanyãwa a bincika asan yadda abin yake, da kuma yadda zã a yi mãganinsa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا تُكَلَّفُ إِلَّا نَفۡسَكَۚ وَحَرِّضِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَكُفَّ بَأۡسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ وَٱللَّهُ أَشَدُّ بَأۡسٗا وَأَشَدُّ تَنكِيلٗا
Sabõda haka, ka* yi yãƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a kanka, kuma ka kwaɗaitar da mũminai. Akwai tsammãnin Allah Ya kange gãfin waɗanda suka kãfirta, kuma Allah ne Mafi tsananin gãfi, kuma Mafi tsananin azabtãwa.
* Umurni zuwa ga Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gareshi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
مَّن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةً حَسَنَةٗ يَكُن لَّهُۥ نَصِيبٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةٗ سَيِّئَةٗ يَكُن لَّهُۥ كِفۡلٞ مِّنۡهَاۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقِيتٗا
Wanda ya yi* cẽto, cẽto mai kyau, zai sãmi rabo daga gare shi, kuma wanda ya yi cẽto, cẽto mummũna, zai sãmi ma'aunidaga gare shi, Kuma Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mai ƙayyade lõkaci.
* Ma'anar ceto: watau wani ya yi wa wani hanya a kan biyan bukãtarsa ta kowace iri, saboda darajar mai yin ceton. Ya kamãta ya yi ceton domin Allah wanda Ya bã shi darajar, bã da ya bai wa Allah kome ba. Idan kuma sayar da ceton yake yi, Allah zai karɓe darajar daga gare shi. Ci da ceto harãmun ne. Sakamakonsa shi ne Allah Ya karɓe darajar ceton daga gare shi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِذَا حُيِّيتُم بِتَحِيَّةٖ فَحَيُّواْ بِأَحۡسَنَ مِنۡهَآ أَوۡ رُدُّوهَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَسِيبًا
Kuma idan an gaishe* ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, kõ kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yã kasance a kan dukkan kõme Mai lissãfi.
* A gaisuwa idan an ce muku: "Assalãmu alaikum" ku mayar da cewa, "Wa'alaikumus Salãmu wa rahamatul Lãhi wa barakãtuH." Kõ ku mayar kamar yadda aka yi muku. Watau kada ku naƙasa 'yan'uwanku kõ da ga gaisuwa ne. Faɗakarwa: Fara sallama mustahabbi ne, mayarwa kuma farilla ne, amma wanda ya fãra, ya fi lãda. Haka yin tsarki a gabãnin lokaci mustahabbi ne, amma a bayãn shigar lokaci ya zama wajibi. Wanda ya yi mustahabbi a nan yã fi lãda. Haka jinkirtar da biyan bãshi ga matsattse wãjibine, amma barrantar da shi mustahabbi ne. Yin mustahabbi a nan yã fi lada.
আরবি তাফসীরসমূহ:
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۗ وَمَنۡ أَصۡدَقُ مِنَ ٱللَّهِ حَدِيثٗا
Allah bãbu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙĩƙa Yana tãra* ku har zuwa ga Yinin ¡iyãma bãbu shakka a cikinsa. Kuma wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga ãbãri.
* Idan kun tsare hukunce-hukuncen da Allah, Wanda babu abin bautawa sai Shi, Ya umurce ku da su, to zai haɗa kalmarku ta tabbata guda har ya zuwa Rãnar Ƙiyãma.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ فَمَا لَكُمۡ فِي ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِئَتَيۡنِ وَٱللَّهُ أَرۡكَسَهُم بِمَا كَسَبُوٓاْۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَهۡدُواْ مَنۡ أَضَلَّ ٱللَّهُۖ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ سَبِيلٗا
To, mẽne ne ya sãme* ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi wata hanya ba zuwa gare shi.
* Hani ne kada mũminai su rarraba kansu domin jãyayya a cikin sha'anin kãfirai. Sai su bi abin da Allah Ya ce a yi da su, kamar yadda bayãninsa yake tafe a cikin wannan aya da ayoyin da suke a bãyanta. Yã yi bayãni da tafsĩli daki-daki.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَدُّواْ لَوۡ تَكۡفُرُونَ كَمَا كَفَرُواْ فَتَكُونُونَ سَوَآءٗۖ فَلَا تَتَّخِذُواْ مِنۡهُمۡ أَوۡلِيَآءَ حَتَّىٰ يُهَاجِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَخُذُوهُمۡ وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ وَجَدتُّمُوهُمۡۖ وَلَا تَتَّخِذُواْ مِنۡهُمۡ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرًا
Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar Allah. Sa'an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِلَّا ٱلَّذِينَ يَصِلُونَ إِلَىٰ قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٌ أَوۡ جَآءُوكُمۡ حَصِرَتۡ صُدُورُهُمۡ أَن يُقَٰتِلُوكُمۡ أَوۡ يُقَٰتِلُواْ قَوۡمَهُمۡۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَسَلَّطَهُمۡ عَلَيۡكُمۡ فَلَقَٰتَلُوكُمۡۚ فَإِنِ ٱعۡتَزَلُوكُمۡ فَلَمۡ يُقَٰتِلُوكُمۡ وَأَلۡقَوۡاْ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَمَ فَمَا جَعَلَ ٱللَّهُ لَكُمۡ عَلَيۡهِمۡ سَبِيلٗا
Fãce dai waɗanda suke sãduwa zuwa ga wasu mutãne waɗanda a tsakãninku da su akwai alkawari, kõ kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirãzansu sun yi ƙunci ga su yãke ku, kõ su yãƙi mutãnensu. Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yãke ku. To, idan sun nĩsance ku sa'an nan ba su yãƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu.
আরবি তাফসীরসমূহ:
سَتَجِدُونَ ءَاخَرِينَ يُرِيدُونَ أَن يَأۡمَنُوكُمۡ وَيَأۡمَنُواْ قَوۡمَهُمۡ كُلَّ مَا رُدُّوٓاْ إِلَى ٱلۡفِتۡنَةِ أُرۡكِسُواْ فِيهَاۚ فَإِن لَّمۡ يَعۡتَزِلُوكُمۡ وَيُلۡقُوٓاْ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَمَ وَيَكُفُّوٓاْ أَيۡدِيَهُمۡ فَخُذُوهُمۡ وَٱقۡتُلُوهُمۡ حَيۡثُ ثَقِفۡتُمُوهُمۡۚ وَأُوْلَٰٓئِكُمۡ جَعَلۡنَا لَكُمۡ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينٗا
Za ku sãmi wasu* sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu.
* Sun bayyana ĩmãninsu gare ku dõmin ku amince musu, kuma sun bayyana kãfirci a wurin mutãnensu kãfirai domin su amince musu watau suna ido ruwa ido tudu. Sũ kam kãfirai ne, ku yãƙe su, sai fa idan sun musulunta, ko kuma sun bayyana sulhunsu sosai a gare ku.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٍ أَن يَقۡتُلَ مُؤۡمِنًا إِلَّا خَطَـٔٗاۚ وَمَن قَتَلَ مُؤۡمِنًا خَطَـٔٗا فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖ وَدِيَةٞ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦٓ إِلَّآ أَن يَصَّدَّقُواْۚ فَإِن كَانَ مِن قَوۡمٍ عَدُوّٖ لَّكُمۡ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖۖ وَإِن كَانَ مِن قَوۡمِۭ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُم مِّيثَٰقٞ فَدِيَةٞ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ وَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مُّؤۡمِنَةٖۖ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ شَهۡرَيۡنِ مُتَتَابِعَيۡنِ تَوۡبَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Kuma bã ya kasancẽwa* ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutãnensa, ãce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutãne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutãne ne (waɗanda) a tsakãninku da tsakãninsu akwai alkawari, sai ya bãyar da diyya ga mutãnensa, tare da 'yanta wuya mũmina. To, wanda bai sãmi (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jẽre, dõmin tũba daga Allah. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
* Kisan kuskure bãbu ƙisãsi a cikinsa, sai dai biyan diyya da kuma kaffãra. Amma biyan diyya yana kan dukkan dangin mai kisan, gwargwadon ƙarfin su, shi ɗaya ne daga cikin su. Idan danginsa ba su isa ba, ko kuwa bãbu su, to, sai baitulmãli na Musulmi ya biya. Ana biyan diyya a cikin shekaru huɗu. Ana bãyar da ita ga magãdan wanda aka kashe. Amma kaffãra ita kam a kan mai kisan kawai take a kan tartĩbinta. Wanda ya kashe bãwa bisa kuskure zai biya ƙĩmarsa ga mai shi, kuma ana son ya yi kaffãra.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يَقۡتُلۡ مُؤۡمِنٗا مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآؤُهُۥ جَهَنَّمُ خَٰلِدٗا فِيهَا وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ وَلَعَنَهُۥ وَأَعَدَّ لَهُۥ عَذَابًا عَظِيمٗا
Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci,* to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Yã yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azãba mai girma.
* Wanda ya kashe mũminai da ganganci, kuma yana ƙudurcin halaccin kashe shi ɗin, to, shi kãfiri ne. Amma idan yana ƙudurcin haramcin kisa, amma duk da haka ya kashe shi domin wata fã'ida ta dũniya, ko domin adãwa, to yana nan mũmini, hukuncinsa ƙisãsi. Surar Baƙara, ãya ta179.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَتَبَيَّنُواْ وَلَا تَقُولُواْ لِمَنۡ أَلۡقَىٰٓ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَٰمَ لَسۡتَ مُؤۡمِنٗا تَبۡتَغُونَ عَرَضَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فَعِندَ ٱللَّهِ مَغَانِمُ كَثِيرَةٞۚ كَذَٰلِكَ كُنتُم مِّن قَبۡلُ فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ فَتَبَيَّنُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), dõmin jihãdi, to, ku nẽmi bãyani.* Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: "Bã Musulmi kake ba." Kunã nẽman hãjar rãyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai ganimõmi mãsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabãnin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Sabõda haka ku zan nẽman bayãni. Lalle ne Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.
* Bayãnin cewa ana ɗaukar wanda aka ji ya yi kalmar shahãda mumini, sai fa idan an ga ya yi wani aiki, ko aka ji ya yi wata magana wadda take warware ma'anar kalmar shahadar, bãbu kuma wani tãwĩli ko jãhilcin da yake iya zama uzuri ga mai shi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
لَّا يَسۡتَوِي ٱلۡقَٰعِدُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ غَيۡرُ أُوْلِي ٱلضَّرَرِ وَٱلۡمُجَٰهِدُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡۚ فَضَّلَ ٱللَّهُ ٱلۡمُجَٰهِدِينَ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ عَلَى ٱلۡقَٰعِدِينَ دَرَجَةٗۚ وَكُلّٗا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَفَضَّلَ ٱللَّهُ ٱلۡمُجَٰهِدِينَ عَلَى ٱلۡقَٰعِدِينَ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Mãsu zama* daga barin yãƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da mãsu jihãdi a cikin hanyar Allah da dũkiyõyinsu da rãyukansu, bã su zama daidai. Allah Yã fĩfĩta mãsu jihãdi da dũkiyoyinsu da rãyukansu a kan mãsu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Yã yi musu alkawari da abu mai kyau.** Kuma Allah yã fĩfĩta mãsu jihãdi a kan mãsu zama da lãda mai girma.
* Falalar mãsu jihãdi a kan waɗanda ba su jihãdi daga cikin muminai. Faɗar falalar tana ƙarfafa zukãta ga yin jihãdi domin tsaron addini da rãyukan mãsu rauni da dũkiyarsu. ** Aljanna.
আরবি তাফসীরসমূহ:
دَرَجَٰتٖ مِّنۡهُ وَمَغۡفِرَةٗ وَرَحۡمَةٗۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمًا
Darajõji daga gare Shi da gãfara da rahama. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ ظَالِمِيٓ أَنفُسِهِمۡ قَالُواْ فِيمَ كُنتُمۡۖ قَالُواْ كُنَّا مُسۡتَضۡعَفِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ قَالُوٓاْ أَلَمۡ تَكُنۡ أَرۡضُ ٱللَّهِ وَٰسِعَةٗ فَتُهَاجِرُواْ فِيهَاۚ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرًا
Lalle ne, waɗanda malã'ĩku* suka karɓi rãyukansu, (alhãli) sunã mãsu zãluntar kansu, sun ce (musu): "A cikin me kuka kasance?" (Su kuma) suka ce: "Mun kasance waɗanda aka raunana a cikin ƙasa." Suka ce: "Ashe ƙasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba, dõmin ku yi hijira a cikinta?" To, waɗannan makõmarsu Jahannama ce. Kuma tã mũnana ta zama makõma.
* Hukuncin rashin hijira zuwa wurin yardar Allah dõmin tsayar da haƙƙõƙin Allah. Hukuncin mai dogewa ne, idan an sãmi dalĩlin yin hijirar, kuma bãbu abin da ya hana ta na uzurori.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِلَّا ٱلۡمُسۡتَضۡعَفِينَ مِنَ ٱلرِّجَالِ وَٱلنِّسَآءِ وَٱلۡوِلۡدَٰنِ لَا يَسۡتَطِيعُونَ حِيلَةٗ وَلَا يَهۡتَدُونَ سَبِيلٗا
Fãce waɗanda aka raunana daga maza da mãtã da yãra waɗanda bã su iya yin wata dabãra, kuma bã su shiryuwa ga hanya.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَأُوْلَٰٓئِكَ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَعۡفُوَ عَنۡهُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَفُوًّا غَفُورٗا
To, waɗannan akwai tsammãnin Allah Ya yãfe laifi daga gare su, kuma Allah Yã kasance Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ وَمَن يُهَاجِرۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ يَجِدۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُرَٰغَمٗا كَثِيرٗا وَسَعَةٗۚ وَمَن يَخۡرُجۡ مِنۢ بَيۡتِهِۦ مُهَاجِرًا إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ يُدۡرِكۡهُ ٱلۡمَوۡتُ فَقَدۡ وَقَعَ أَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar* Allah, zai sãmu, a cikin ƙasa, wurãren jũyãwa mãsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lãdarsa tã auku ga Allah, Kuma Allah Yã kasance, a gare ku, Mai gãfara, Mai jin ƙai.
* Allah Yana kwaɗaitar da mũminai ga yin hijira zuwa wurin neman yardarsa. Hukuncin hijira yana nan a ko da yaushe hãli ya hukunta da a yi ta.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَقۡصُرُواْ مِنَ ٱلصَّلَوٰةِ إِنۡ خِفۡتُمۡ أَن يَفۡتِنَكُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْۚ إِنَّ ٱلۡكَٰفِرِينَ كَانُواْ لَكُمۡ عَدُوّٗا مُّبِينٗا
Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, bãbu laifi a kanku ku rage* daga salla idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku. Lalle ne kãfirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne.
* Rage salla a nan ba ana nufin sallar kasaru ta tafiya ba, wanda take ta tabbata da sunna. Wannan rage salla, shi ne sallar tsõro wadda ake yi gwargwadon hãlin da ake ciki na tsõro. Idan yana yiwuwa a yi ta da lĩmãmi, sai ya kasa jama'a kashi biyu, to, sai a yi kamar yadda ãya ta tafe zã ta yi bayãni, idan kuwa bã zai yiwu ba, sai a yi yadda hãli ya sauƙaƙa duka, kamar a ãyã ta 239 daga Suratul Baƙara.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِذَا كُنتَ فِيهِمۡ فَأَقَمۡتَ لَهُمُ ٱلصَّلَوٰةَ فَلۡتَقُمۡ طَآئِفَةٞ مِّنۡهُم مَّعَكَ وَلۡيَأۡخُذُوٓاْ أَسۡلِحَتَهُمۡۖ فَإِذَا سَجَدُواْ فَلۡيَكُونُواْ مِن وَرَآئِكُمۡ وَلۡتَأۡتِ طَآئِفَةٌ أُخۡرَىٰ لَمۡ يُصَلُّواْ فَلۡيُصَلُّواْ مَعَكَ وَلۡيَأۡخُذُواْ حِذۡرَهُمۡ وَأَسۡلِحَتَهُمۡۗ وَدَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ تَغۡفُلُونَ عَنۡ أَسۡلِحَتِكُمۡ وَأَمۡتِعَتِكُمۡ فَيَمِيلُونَ عَلَيۡكُم مَّيۡلَةٗ وَٰحِدَةٗۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِن كَانَ بِكُمۡ أَذٗى مِّن مَّطَرٍ أَوۡ كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَن تَضَعُوٓاْ أَسۡلِحَتَكُمۡۖ وَخُذُواْ حِذۡرَكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ أَعَدَّ لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا
Kuma idan kã kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tãre da kai, kuma sai su riƙe makãmansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bãyanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tãre da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makãmansu. Waɗanda suka kãfirta sun yi gũrin dã dai kuna shagala daga makamanku da kãyanku dõmin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma bãbu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, kõ kuwa kun kasance mãsu jinya ga ku ajiye makãmanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Yã yi tattali, ga kãfirai, azãba mai walakantarwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَإِذَا قَضَيۡتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ قِيَٰمٗا وَقُعُودٗا وَعَلَىٰ جُنُوبِكُمۡۚ فَإِذَا ٱطۡمَأۡنَنتُمۡ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۚ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ كَانَتۡ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ كِتَٰبٗا مَّوۡقُوتٗا
Sa'an nan idan kun ƙãre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan sãsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tã kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَا تَهِنُواْ فِي ٱبۡتِغَآءِ ٱلۡقَوۡمِۖ إِن تَكُونُواْ تَأۡلَمُونَ فَإِنَّهُمۡ يَأۡلَمُونَ كَمَا تَأۡلَمُونَۖ وَتَرۡجُونَ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا يَرۡجُونَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
Kuma kada ku sassauta a cikin nẽman mutãnen idankun kasance kuna jin zõgi, to, lalle sũ ma, suna jin zõgi kamar yadda kuke jin zõgi. Kuma kuna tsammãni, daga Allah, abin da bã su tsammãni. Kuma Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِتَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ بِمَآ أَرَىٰكَ ٱللَّهُۚ وَلَا تَكُن لِّلۡخَآئِنِينَ خَصِيمٗا
Lalle ne, Mũ, Mun saukar,* zuwa gare ka, Littãfi da gaskiya, dõmin ka yi hukunci a tsakãnin mutãne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma dõmin mãsu yaudara.
* Gudãnar da hukunci a cikin mahakama, kada mai shari'a ya taimaki kowane sãshe, duk yadda suke a gare shi, sai ya ɗauke su daidai a gabansa, kamar yadda ya auku a gaban Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi. Wani mutum Musulmi ana ce masa Mat'ama bn Ubairak ya yi sãtar sulke ya ɓõye shi a wurin wani Bayahũde. A lõkacin da aka gãne sulken a wurin Bayahũden, sai Mat'ama ya yi masa ƙazafi da sãtarsa, shi kuma yayi rantsuwa cewa bã shi ne ya sãtã ba. Kuma mutãnensa suka rõƙi Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, dõmin ya yi musu jãyayya yakuɓutar da mat'ama, Annabi kuwa bai yarda ba. Kamar yadda ãyõyin nan suka bayyana, domin ya zama abin kõyi. Wannan kuma ya nũna cewa, ga gudanar da sharĩ'a Annabi yana yin ijtihãdi gwargwadon abin da ya bayyana daga hujjoji ya yi hukunci, kamar wajen shãwara a wurin yãki. Ya zama abin kõyi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱسۡتَغۡفِرِ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Kuma ka nẽmi Allah gãfara. Lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَا تُجَٰدِلۡ عَنِ ٱلَّذِينَ يَخۡتَانُونَ أَنفُسَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ خَوَّانًا أَثِيمٗا
Kuma kada ka yi jãyayya dõmin tunkuɗe wa waɗanda suka yaudari kansu. Lalle ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai yawan hã'inci mai yawan zunubi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَسۡتَخۡفُونَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَلَا يَسۡتَخۡفُونَ مِنَ ٱللَّهِ وَهُوَ مَعَهُمۡ إِذۡ يُبَيِّتُونَ مَا لَا يَرۡضَىٰ مِنَ ٱلۡقَوۡلِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطًا
Suna nẽman ɓõyewa daga mutãne kuma bã su nẽmanɓõyewa daga Allah, alhãli kuwa Shi Yana tãre da su a lõkacin da suke kwãna da niyyar yin abin da bã Ya yarda da shi daga maganar. Kuma Allah Yã kasance ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
هَٰٓأَنتُمۡ هَٰٓؤُلَآءِ جَٰدَلۡتُمۡ عَنۡهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فَمَن يُجَٰدِلُ ٱللَّهَ عَنۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَم مَّن يَكُونُ عَلَيۡهِمۡ وَكِيلٗا
Gã ku, yã waɗannan*! Kun yi jidãli, dõmin tunkuɗe musu (kunya) a cikin rãyuwar dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rãnar ¡iyãma? Ko kuwa wãne ne zai kasance wakĩli a kansu?
* Wannan yana nũna aikin lauya (Lawyer) dõmin ya taimaki marasa gaskiya sabõda ya kuɓuta harãmun ne, har dai idan zã a mayar da laifi ga wani barrantacce ko kuwa za a karɓe hakkin mai hakki a bai wa wanda bai cancanta da shi ba. Amma wakĩlin sharĩ'a yana halatta idan bai zama dõmin ɓõye gaskiya ba. Wakĩlai irin na zãmanin nan mãsu sanã'a da wannan, sũ ne karnukan dũniya na farautar haram dõmin su sha jini.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يَعۡمَلۡ سُوٓءًا أَوۡ يَظۡلِمۡ نَفۡسَهُۥ ثُمَّ يَسۡتَغۡفِرِ ٱللَّهَ يَجِدِ ٱللَّهَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Kuma wanda ya aikata cũta kõ kuwa ya zãlunci kansa, sa'an nan kuma ya nẽmi Allah gãfara, zai sãmi Allah Mai gãfara, Mai jin ƙai.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يَكۡسِبۡ إِثۡمٗا فَإِنَّمَا يَكۡسِبُهُۥ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Kuma wanda ya yi tsirfanci zunubi, to yanã tsirfarsa ne a kan kansa kawai. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يَكۡسِبۡ خَطِيٓـَٔةً أَوۡ إِثۡمٗا ثُمَّ يَرۡمِ بِهِۦ بَرِيٓـٔٗا فَقَدِ ٱحۡتَمَلَ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا
Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi sa'an nan kuma ya jẽfi wani barrantacce da shi, to, lalle ne yã tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ وَرَحۡمَتُهُۥ لَهَمَّت طَّآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ أَن يُضِلُّوكَ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡۖ وَمَا يَضُرُّونَكَ مِن شَيۡءٖۚ وَأَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَكَ مَا لَمۡ تَكُن تَعۡلَمُۚ وَكَانَ فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ عَظِيمٗا
Kuma bã dõmin falalar Allah ba, a kanka, da rahamarSa, haƙĩƙa, dã wata ƙungiya daga gare su ta himmatu ga su ɓatar da kai. Kuma bã su ɓatarwa fãce kansu, kuma bã su cũtar ka daga kõme, Kuma Allah Yã saukar da Littãfi da hikima gare ka, kuma Ya sanar da kai abin da ba ka kasance kã sani ba. Kuma falalar Allah tã kasance mai girma a gare ka.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ لَّا خَيۡرَ فِي كَثِيرٖ مِّن نَّجۡوَىٰهُمۡ إِلَّا مَنۡ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوۡ مَعۡرُوفٍ أَوۡ إِصۡلَٰحِۭ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ ٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِ ٱللَّهِ فَسَوۡفَ نُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu* fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.
* Hukuncin gãnawa da Annabi ko wani shũgaban jama'a mai tsayuwa matsayin Annabi ga gyãran sha'aninsu, bã ya halatta sai idan akwai wani alheri a ciki wanda amfaninsa zai shãfi jama'a duka.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يُشَاقِقِ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ ٱلۡهُدَىٰ وَيَتَّبِعۡ غَيۡرَ سَبِيلِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ نُوَلِّهِۦ مَا تَوَلَّىٰ وَنُصۡلِهِۦ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرًا
Kuma wanda ya sãɓã wa* Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar mũminai, zã Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙõne shi da Jahannama. Kuma tã mũnana ta zama makõma.
* Hana fassarar Alƙur'ãni ko sunnar Annabi, ba a kan hanyar da Annabi ko Sahabbansa da waɗanda suka bi hanyarsu suka fassara ba. Da mutum ya yi tãwilin Alƙur'ãni, gãra ya ce bai sani ba. Tãwĩlin Alƙur'ãni ko Hadĩsi da hankali yana kai ga bũɗe ƙõfar kãfirci ɓõyayye da yin hukunci da abin da Allah bai saukar ba. Na'am ba a hana ijtihãdi ga abin da ba a sãmi nassi a kansa ba, ko kuma aka sãmi nassi wanda bã bayyananne ba. Jingina ijtihãdi ga ra'ayi ya fi tãwĩlin abin da bai bayyana ba daga Alƙur'ãni ko Hadĩsi, domin ra'ayi ba ya ɓatar da wasu, amma tãwĩli yana ɓatarwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا
Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nĩsa.*
* Bayãnin shirki da hukunce-hukuncensa da abin da yake ratayuwa da shi. Sanin ma'anar shirki wajibi ne, dõmin a kan tauhĩdi ne aka gina shikãshikan Musulunci.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِن يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ إِنَٰثٗا وَإِن يَدۡعُونَ إِلَّا شَيۡطَٰنٗا مَّرِيدٗا
Bã su kiran kõwa, baicin Shi, fãce mãtã kuma bã su kiran kõwa fãce Shaiɗan, mai tsaurin kai.
আরবি তাফসীরসমূহ:
لَّعَنَهُ ٱللَّهُۘ وَقَالَ لَأَتَّخِذَنَّ مِنۡ عِبَادِكَ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا
Allah Yã la'ane shi. Kuma ya ce: "Lalle ne, zã ni riƙi rabõ yankakke,* daga bãyinKa.
* Rabon Shaiɗan daga kõwane dubu, shi ne ɗari tara da cas'in da tara kamar yadda aka ruwaito a cikin Hadĩsi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَأُضِلَّنَّهُمۡ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمۡ وَلَأٓمُرَنَّهُمۡ فَلَيُبَتِّكُنَّ ءَاذَانَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ وَلَأٓمُرَنَّهُمۡ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلۡقَ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَّخِذِ ٱلشَّيۡطَٰنَ وَلِيّٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِ فَقَدۡ خَسِرَ خُسۡرَانٗا مُّبِينٗا
"Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dõmin su kãtse* kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su dõmin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya.
* Suna kãtse kunnuwan dabbõbi dõmin su nũna cewa na gumãkansu ne. Sunan mãtã shi ne ga duk abin da ba ya da rai, kamar watã itãtuwa duka mãtã ne. Canza halitta kamar tsãgen fuska da fãƙe haƙõra da karkarar gemu dõmin neman kyau, duka umurnin Shaiɗan ne.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَعِدُهُمۡ وَيُمَنِّيهِمۡۖ وَمَا يَعِدُهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ إِلَّا غُرُورًا
Yanã yi musu alkawari, kuma yanã sanya musu gũri, alhãli Shaiɗan bã ya yi musu wani wa'adĩn kõme face ruɗi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أُوْلَٰٓئِكَ مَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُ وَلَا يَجِدُونَ عَنۡهَا مَحِيصٗا
Waɗannan matattararsu Jahannama ce, kuma bã sãmun makarkata daga gare ta.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ سَنُدۡخِلُهُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٗاۚ وَمَنۡ أَصۡدَقُ مِنَ ٱللَّهِ قِيلٗا
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, zã mu shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?
আরবি তাফসীরসমূহ:
لَّيۡسَ بِأَمَانِيِّكُمۡ وَلَآ أَمَانِيِّ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِۗ مَن يَعۡمَلۡ سُوٓءٗا يُجۡزَ بِهِۦ وَلَا يَجِدۡ لَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا
(Al'amari) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma* ba gũrace- gũracen Mutãnen Littãfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki zã a sãka masa da shi kuma bã zai sãmi wani masõyi ba, baicin Allah, kuma bã zai sãmi mataimaki ba.
* Addini bã tatsuniyar baki bane, aiki ne, ko mutum ya yi mugu ya shĩga Wuta, ko kuma ya yi na ƙwarai ya shiga Aljanna.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ نَقِيرٗا
Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhãli kuwa Yanã mũmini, to, waɗannan sunã shiga Aljanna kuma bã zã a zãlunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَمَنۡ أَحۡسَنُ دِينٗا مِّمَّنۡ أَسۡلَمَ وَجۡهَهُۥ لِلَّهِ وَهُوَ مُحۡسِنٞ وَٱتَّبَعَ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۗ وَٱتَّخَذَ ٱللَّهُ إِبۡرَٰهِيمَ خَلِيلٗا
Kuma wãne ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yanã mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrãhĩm, Yanã mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Yã riƙi Ibrãhĩm badãɗayi.*
* Akwai kwaɗaitarwa ga cewa, wanda yake son Allah Ya so shi, to sai ya bi aƙĩda da aiki irin na Ibrãhĩma, sai Allah Ya so shi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٖ مُّحِيطٗا
Kuma Allah ke da* (mallakar) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã kasance, a dukkan, kõme, Mai kẽwayewa.
* Ko da yake Allah Yã riƙi Ibrãhĩma "Khalĩl" watau masõyi, amma bai hana Ibrahĩma ya zama a cikin bãyin Allah kuma mulkinSa ba, domin yana daga cikin abin da sama da ƙasa suka ƙunsa a cikin su.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَيَسۡتَفۡتُونَكَ فِي ٱلنِّسَآءِۖ قُلِ ٱللَّهُ يُفۡتِيكُمۡ فِيهِنَّ وَمَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ فِي يَتَٰمَى ٱلنِّسَآءِ ٱلَّٰتِي لَا تُؤۡتُونَهُنَّ مَا كُتِبَ لَهُنَّ وَتَرۡغَبُونَ أَن تَنكِحُوهُنَّ وَٱلۡمُسۡتَضۡعَفِينَ مِنَ ٱلۡوِلۡدَٰنِ وَأَن تَقُومُواْ لِلۡيَتَٰمَىٰ بِٱلۡقِسۡطِۚ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِهِۦ عَلِيمٗا
Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: "Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu* (na gãdo) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi."
* A cikin jahiliyya ba su bai wa yãra da mãtã gãdo. Musulunci ya sõke wannan al'ãda da ãyar gãdo, ãyã ta 11. Kuma idan akwai wata marainiya ga hannun wani tana da dũkiya, sai ya jefa mata mayafinsa domin ya hana ta auren wani namiji. Shi kuma ko ya aure ta ko kuma ya bar ta bãbu aure har ta mutu, su yi gãdon ta.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِنِ ٱمۡرَأَةٌ خَافَتۡ مِنۢ بَعۡلِهَا نُشُوزًا أَوۡ إِعۡرَاضٗا فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَآ أَن يُصۡلِحَا بَيۡنَهُمَا صُلۡحٗاۚ وَٱلصُّلۡحُ خَيۡرٞۗ وَأُحۡضِرَتِ ٱلۡأَنفُسُ ٱلشُّحَّۚ وَإِن تُحۡسِنُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا
Kuma idan wata mace ta ji tsõron ƙiyo daga mijinta kõ kuwa bijirẽwa to, bãbu laifi a kansu su yi sulhu a tsakãninsu, sulhu (mai kyau) Kuma yin sulhu ne mafi alhẽri. Kuma an halartar wa rayũka yin rõwa. Kuma idan kun kyautata, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne, Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلَن تَسۡتَطِيعُوٓاْ أَن تَعۡدِلُواْ بَيۡنَ ٱلنِّسَآءِ وَلَوۡ حَرَصۡتُمۡۖ فَلَا تَمِيلُواْ كُلَّ ٱلۡمَيۡلِ فَتَذَرُوهَا كَٱلۡمُعَلَّقَةِۚ وَإِن تُصۡلِحُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin* mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
* Wajen so, bã zã a iya daidaita su ba, sai a daidaita ga kwãna da ciyarwa da wurin kwãna da tufãfi gwargwadon hãlin kõwace.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِن يَتَفَرَّقَا يُغۡنِ ٱللَّهُ كُلّٗا مِّن سَعَتِهِۦۚ وَكَانَ ٱللَّهُ وَٰسِعًا حَكِيمٗا
Kuma idan sun rabu, Allah zai wadãtar da kõwanne daga yalwarSa. Kuma Allah Yã kasance Mayalwaci, Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ وَصَّيۡنَا ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَإِيَّاكُمۡ أَنِ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ وَإِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَنِيًّا حَمِيدٗا
Kuma Allah ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku, da kũ, cẽwa ku bi Allah da taƙawa, kuma idan kun kãfirta, to, lalle ne, Allah Yanã da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa. Kuma Allah Yã kasance wadãtacce, Gõdadde.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلًا
Kuma Allah ne da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa, kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ أَيُّهَا ٱلنَّاسُ وَيَأۡتِ بِـَٔاخَرِينَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ قَدِيرٗا
Idan Yã so, zã Ya tafi da ku, yã kũ mutãne! kuma Ya zo da wasu. Allah Yã kasance a kan haka, Mai ĩkon yi ne.
আরবি তাফসীরসমূহ:
مَّن كَانَ يُرِيدُ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا فَعِندَ ٱللَّهِ ثَوَابُ ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا
Wanda ya kasance* Yanã nufin sakamakon dũniya, to, a wurin Allah sakamakon dũniya da Lãhira yake. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Mai gani.
* Wannan shi ne ƙarshen wasiyya ga Yahũdu da Nasãra da kuma Musulmi kuma ma'anar wasiyya ĩta ce Allah Yã yi umurni da ku yi Masa ɗã'a amma bã domin Yana neman wani abu daga gare ku ba, domin bã zã ku ƙãra Masa mulki ba, dõmin shi ne da sammai da ƙasa da abin da ke tsakaninsu kũ kuma kuna cikinsu. Saboda haka neman ɗã'ar nan domin amfanin kanku ne.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُونُواْ قَوَّٰمِينَ بِٱلۡقِسۡطِ شُهَدَآءَ لِلَّهِ وَلَوۡ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ أَوِ ٱلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَۚ إِن يَكُنۡ غَنِيًّا أَوۡ فَقِيرٗا فَٱللَّهُ أَوۡلَىٰ بِهِمَاۖ فَلَا تَتَّبِعُواْ ٱلۡهَوَىٰٓ أَن تَعۡدِلُواْۚ وَإِن تَلۡوُۥٓاْ أَوۡ تُعۡرِضُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida* sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.
* Bãyar da shaida da hukunce-hukuncen da suka rãtayu da shi. Bãyar da shaida amãna ce ta Allah daidai da tsaron dũkiyar amãna, ko mã ta fi tsanani, domin takan kai ga rai. Karkatar da magana, watau a faɗe ta bã yadda take ba. Bijirewa ita ce a ƙi bãyar da shaida.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِي نَزَّلَ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِن قَبۡلُۚ وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni* da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa.
* ĩmãni da dukan rukunnan ĩmãni shida yana cikin tsaron amãna. Rukunnan ĩmãni su ne, ĩmãni da Allah da ManzanninSa, da malã'iku da LittattafanSa da Rãnar Lãhira da Ƙaddara.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ثُمَّ كَفَرُواْ ثُمَّ ءَامَنُواْ ثُمَّ كَفَرُواْ ثُمَّ ٱزۡدَادُواْ كُفۡرٗا لَّمۡ يَكُنِ ٱللَّهُ لِيَغۡفِرَ لَهُمۡ وَلَا لِيَهۡدِيَهُمۡ سَبِيلَۢا
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sa'an nan kuma suka yi ĩmani, sa'an nan kuma suka kãfirta sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci, Allah bai kasance Yanã gãfarta musu ba, kuma bã zai shiryar da su ga Hanya ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
بَشِّرِ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ بِأَنَّ لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمًا
Ka yi wa munãfukai bushãra da cẽwa lalle ne sunã da azãba mai raɗaɗi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
ٱلَّذِينَ يَتَّخِذُونَ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ أَيَبۡتَغُونَ عِندَهُمُ ٱلۡعِزَّةَ فَإِنَّ ٱلۡعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا
Waɗanda suke riƙon kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin sunã nẽman izza ne a wurinsu? To, lalle ne izza ga Allah take gabã ɗaya.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَقَدۡ نَزَّلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أَنۡ إِذَا سَمِعۡتُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ يُكۡفَرُ بِهَا وَيُسۡتَهۡزَأُ بِهَا فَلَا تَقۡعُدُواْ مَعَهُمۡ حَتَّىٰ يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيۡرِهِۦٓ إِنَّكُمۡ إِذٗا مِّثۡلُهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ جَامِعُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡكَٰفِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا
Kuma lalle ne Yã sassaukar* muku a cikin Littãfi cẽwa idan kun ji ãyõyin Allah, anã kãfirta da su, kuma anã izgili da su, to, kada ku zauna tãre da sũ, sai sun shiga cikin wani lãbãri. Lalle ne kũ, a lõkacin nan misãlinsu kuke. Lalle ne, Allah Mai tãra munãfukai da kãfirai ne a cikin Jahannama gabã ɗaya.
* A cikin Alƙur'ãni, sũratul An'ãm, ãyã ta 68.
আরবি তাফসীরসমূহ:
ٱلَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمۡ فَإِن كَانَ لَكُمۡ فَتۡحٞ مِّنَ ٱللَّهِ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَكُن مَّعَكُمۡ وَإِن كَانَ لِلۡكَٰفِرِينَ نَصِيبٞ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَسۡتَحۡوِذۡ عَلَيۡكُمۡ وَنَمۡنَعۡكُم مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَلَن يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لِلۡكَٰفِرِينَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ سَبِيلًا
Waɗanda suke jiran dãko game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: "Ashe, ba mu kasance tãre da kũ ba?" Kuma idan wani rabo ya sãmu ga kãfirai sai su ce: "Ashe ba mu rinjãye ku ba, kuma muka tsare ku daga mũminai?" To, Allah ne Yake yin hukunci tsakãninku a Rãnar ¡iyãma, kuma Allah bã zai sanya hanya ba ga kãfirai a kan mũminai.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ يُخَٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَهُوَ خَٰدِعُهُمۡ وَإِذَا قَامُوٓاْ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ قَامُواْ كُسَالَىٰ يُرَآءُونَ ٱلنَّاسَ وَلَا يَذۡكُرُونَ ٱللَّهَ إِلَّا قَلِيلٗا
Lalle ne munãfukai sunã yaudarẽwa da Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga salla, sai su tãshi sunã mãsu kasãla. Suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan.
আরবি তাফসীরসমূহ:
مُّذَبۡذَبِينَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ لَآ إِلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِ وَلَآ إِلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ سَبِيلٗا
Mãsu kai-kawo ne a tsakãnin wancan; bã zuwa ga waɗannan ba, kuma bã zuwa ga waɗannan ba. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã za ka sãmar masa wata Hanya ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ عَلَيۡكُمۡ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينًا
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin, kanã nufin ku sanyã wa Allah dalĩli bayyananne a kanku?
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِي ٱلدَّرۡكِ ٱلۡأَسۡفَلِ مِنَ ٱلنَّارِ وَلَن تَجِدَ لَهُمۡ نَصِيرًا
Lalle ne, manãfukai sunã a magangara mafi ƙasƙanci daga wuta. Kuma bã zã ka sãma musu mataimaki ba.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَٱعۡتَصَمُواْ بِٱللَّهِ وَأَخۡلَصُواْ دِينَهُمۡ لِلَّهِ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَعَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَسَوۡفَ يُؤۡتِ ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَجۡرًا عَظِيمٗا
Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka nẽmi fakuwa ga Allah, kuma suka tsarkake addininsu dõmin Allah, to, waɗannan sunã tãre da mũminai, kuma Allah zai bai wa mũminai lãda mai girma.
আরবি তাফসীরসমূহ:
مَّا يَفۡعَلُ ٱللَّهُ بِعَذَابِكُمۡ إِن شَكَرۡتُمۡ وَءَامَنتُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ شَاكِرًا عَلِيمٗا
Mẽne ne Allah zai amfãna da yi maku azãba idan kun gõde, kuma kun yi ĩmãni? Allah Yã ksance Mai gõdiya Masani.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ لَّا يُحِبُّ ٱللَّهُ ٱلۡجَهۡرَ بِٱلسُّوٓءِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ إِلَّا مَن ظُلِمَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعًا عَلِيمًا
Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana* fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani.
* Magana mummũna. Allah bã Ya son bayyana mugunyar magana, sai dai wanda aka zãlunta, yana iya kai ƙãra, kuma yana iya yin addu'a a kan wanda ya zãlunce shi. Sa'an nan ya shiga bayyanãwar abin da ake nufi da miyagun maganganu a cikin ãyõyin da suke bin wan nan.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِن تُبۡدُواْ خَيۡرًا أَوۡ تُخۡفُوهُ أَوۡ تَعۡفُواْ عَن سُوٓءٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوّٗا قَدِيرًا
Idan kun bayyana alhẽri, kõ kuwa kuka ɓõye shi, kõ kuwa kuka yãfe laifi daga cũta, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfewa, Mai ikon yi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيُرِيدُونَ أَن يُفَرِّقُواْ بَيۡنَ ٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيَقُولُونَ نُؤۡمِنُ بِبَعۡضٖ وَنَكۡفُرُ بِبَعۡضٖ وَيُرِيدُونَ أَن يَتَّخِذُواْ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا
Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe* a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: "Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe." Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan.
* Rarrabewa tsakãnin Allah da ManzanninSa, shi ne mutum ya ce ga misãli, "Na yarda Allah gaskiya ne, zan yi duka abin da yake mai kyau saboda Shi, amma bãbu ruwãna da wani Annabi kõ wani manzõ," ko kuma ya ce ai duk addĩnai ɗaya ne, ana nufin Allah da su, sai mutum ya bi abin da ya ga dama. Duka irin waɗannan maganganu bã su da kyau, kãfirci ne.
আরবি তাফসীরসমূহ:
أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ حَقّٗاۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا
Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَلَمۡ يُفَرِّقُواْ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ أُوْلَٰٓئِكَ سَوۡفَ يُؤۡتِيهِمۡ أُجُورَهُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma ba su rarrabe a tsakãnin kõwa ba daga gare su, waɗannan zã Mu bã su ijãrõrinsu, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَسۡـَٔلُكَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن تُنَزِّلَ عَلَيۡهِمۡ كِتَٰبٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِۚ فَقَدۡ سَأَلُواْ مُوسَىٰٓ أَكۡبَرَ مِن ذَٰلِكَ فَقَالُوٓاْ أَرِنَا ٱللَّهَ جَهۡرَةٗ فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّٰعِقَةُ بِظُلۡمِهِمۡۚ ثُمَّ ٱتَّخَذُواْ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ فَعَفَوۡنَا عَن ذَٰلِكَۚ وَءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينٗا
Mutãnen Littãfi sunã tambayar ka ka saukar da wani littãfi daga sama, a kansu, to, lalle ne sun tambayi Mũsã mũfã girma daga wannan, suka ce: "Ka nũna mana Allah bayyane." Sai tsãwa ta kãmã su sabõda zãluncinsu, sa'an nan kuma suka riƙi maraƙi (abin bautãwa) bãyan hujjoji bayyanannu sun je musu. Sa'an nan Muka yãfe laifi daga wancan. Kuma Mun bai wa Mũsã dalĩli bayyananne.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَرَفَعۡنَا فَوۡقَهُمُ ٱلطُّورَ بِمِيثَٰقِهِمۡ وَقُلۡنَا لَهُمُ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡبَابَ سُجَّدٗا وَقُلۡنَا لَهُمۡ لَا تَعۡدُواْ فِي ٱلسَّبۡتِ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا
Kuma Muka ɗaukaka dũtse sãma da su, sabõda alkawarinsu, kuma Muka ce musu: "Ku shiga ƙõfar kunã mãsu tawãli'u," Kuma Muka ce musu: "Kada ku ƙẽtare haddi a cikin Asabat," kuma Muka riƙi alkawari mai kauri daga gare su."
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَبِمَا نَقۡضِهِم مِّيثَٰقَهُمۡ وَكُفۡرِهِم بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَقَتۡلِهِمُ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَقَوۡلِهِمۡ قُلُوبُنَا غُلۡفُۢۚ بَلۡ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَيۡهَا بِكُفۡرِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُونَ إِلَّا قَلِيلٗا
To, sabõda warwarẽwarsu ga alkawarinsu, da kãfirtarsu da ãyõyin Allah, da kisansu ga Annabãwa, bã da hakki ba, da maganarsu: "Zukãtanmu sunã cikin rufi." Ã'a, Allah ne Ya yunƙe a kansu sabõda kãfircinsu, sabõda haka bã zã su yi ĩmãni ba fãce kaɗan.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَبِكُفۡرِهِمۡ وَقَوۡلِهِمۡ عَلَىٰ مَرۡيَمَ بُهۡتَٰنًا عَظِيمٗا
Kuma sabõda kãfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَقَوۡلِهِمۡ إِنَّا قَتَلۡنَا ٱلۡمَسِيحَ عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ رَسُولَ ٱللَّهِ وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَٰكِن شُبِّهَ لَهُمۡۚ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُۚ مَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍ إِلَّا ٱتِّبَاعَ ٱلظَّنِّۚ وَمَا قَتَلُوهُ يَقِينَۢا
Da faɗarsu:* "Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah," alhãli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka sãɓã wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare, shi, bã da wani ilmi fãce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni.
* Faɗarsu ta izgili watau suna cewa: "Mun kashe ĩsã ɗan Maryama wanda yake da'awar shi Manzon Allah ne." Asalin maganar Yahũdu suka karkatar da Dãwũda sarkin Dimashƙa, da cewa ga wani mutum nan yana ɓãta ƙasa da aƙĩdar mutãne a Baitil Maƙdis sabõda haka ya bãyar da õda ga hãkimansa a Baitil Maƙdis da a kashe ĩsã sai suka tafi suka tsare shi a cikin gida shi da sahabbansa, watau Hawãriyawa. ĩsã ya rõki waninsu da yarda da kisa a kan sakamakon Aljanna. Sai ƙaraminsu ya yarda, Allah Ya sanya masa sifar ĩsã, a bãyan haka Ya ɗauke ĩsã. Shi kuma aka kashe shi matsayin ĩsã. Daga nan,Yahũdu suna zaton sun kashe shi, kuma waɗanda suka halarci ƙissar, suka sãɓã wa jũna wajen sifar ĩsã da cewa Shi ne Allah, ko ɗan Allah, ko ɗayan uku, ko manzon Allah, kamar yadda ya gabãta a cikin Baƙara.
আরবি তাফসীরসমূহ:
بَل رَّفَعَهُ ٱللَّهُ إِلَيۡهِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا
Ã'a, Allah Ya ɗauke shi zuwa garẽ Shi, kuma Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَإِن مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ إِلَّا لَيُؤۡمِنَنَّ بِهِۦ قَبۡلَ مَوۡتِهِۦۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكُونُ عَلَيۡهِمۡ شَهِيدٗا
Kuma bãbu kõwa daga Mutãnen Littafi,* fãce lalle yanã ĩmãni da shi a gabãnin mutuwarsa, kuma a Rãnar ¡iyãma yana kasancẽwa mai shaida, a kansu.
* An ce Mutãnen Littafi na zamanin Annabi Isa lalle suna imani da shi gabanin mutuwarsa cewa shi ba Allah ne ba, kuma ba ɗan Allah ne ba; kowannensu kamin ya mutu yana imani da cewa Isa Manzon A1lah ne, a lokacin da imanin ba ya amfanin sa. Allah Ya fi sani.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَبِظُلۡمٖ مِّنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمۡنَا عَلَيۡهِمۡ طَيِّبَٰتٍ أُحِلَّتۡ لَهُمۡ وَبِصَدِّهِمۡ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ كَثِيرٗا
To, sabõda zãlunci daga waɗanda suka tũba (Yahũdu) Muka haramta musu abũbuwa masu dãɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma sabõda taushẽwarsu daga hanyar Allah da yawa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَأَخۡذِهِمُ ٱلرِّبَوٰاْ وَقَدۡ نُهُواْ عَنۡهُ وَأَكۡلِهِمۡ أَمۡوَٰلَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡبَٰطِلِۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ مِنۡهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا
Da karɓarsu ga riba, alhãli kuwa an hana su daga gare ta, da cin su ga dũkiyar mutãne daƙarya. Kuma Muka yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai raɗaɗi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
لَّٰكِنِ ٱلرَّٰسِخُونَ فِي ٱلۡعِلۡمِ مِنۡهُمۡ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَۚ وَٱلۡمُقِيمِينَ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَٱلۡمُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ أُوْلَٰٓئِكَ سَنُؤۡتِيهِمۡ أَجۡرًا عَظِيمًا
Amma tabbatattu* a cikin ilmi daga gare su, da mũminai, suna ĩmani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, madalla da masu tsai da salla, da mãsu bãyar da zakka, da mãsu ĩmãni daAllah da Rãnar Lãhira. Waɗannan zã Mu bã su lãda mai girma.
* Kabĩla mai asali tana lãlãcewa sabõda rashin bin addini, har ta zama mafi sharrin halittar Allah, kamar Yahũdu. Kuma a cikin haka wanda ya komawa gaskiya sai ya koma ga tsohon asalin, ya ƙãra daukaka da shi, kamar waɗanda suka musulunta daga cikinsu.
আরবি তাফসীরসমূহ:
۞ إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا
Lalle ne Mu, Mun* yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa. Kuma Mun yi wahayi zuwa ga Ibrãhĩma da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Yaƙũbu da jĩkõki da ĩsa da Ayũba da Yũnusa da Hãruna da Sulaimãn. Kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.
* Muhammadu bã shi ne farkon manzanni ba, kuma bã shi ne aka fãra yi wa wahayi ba, bã shi ne aka fãra bai wa Littãfi ba. Sai dai shi ne ƙarshensu ga dukkan waɗannan abũbuwa, kamar yadda bushãrarsu ta bayyana tun a gabãninsa. Kuma yawan Annabãwa da Manzanni bãbu wanda ya san shi sai Allah, wahayi shi ne ishãra ko yanda Allah ke aiko malã'iki da Manzanci zuwa ga wani Annabi ko Manzonsa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
وَرُسُلٗا قَدۡ قَصَصۡنَٰهُمۡ عَلَيۡكَ مِن قَبۡلُ وَرُسُلٗا لَّمۡ نَقۡصُصۡهُمۡ عَلَيۡكَۚ وَكَلَّمَ ٱللَّهُ مُوسَىٰ تَكۡلِيمٗا
Da wasu Manzanni, haƙĩ ƙa, Mun bã da lãbarinsu a gare ka daga gabãni, da wasu manzanni waɗanda ba Mu bã da lãbãrinsu ba a gare ka, kuma Allah Yã yi magana da Mũsã, magana sõsai.
আরবি তাফসীরসমূহ:
رُّسُلٗا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُۢ بَعۡدَ ٱلرُّسُلِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمٗا
Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin. Kuma Allah yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
لَّٰكِنِ ٱللَّهُ يَشۡهَدُ بِمَآ أَنزَلَ إِلَيۡكَۖ أَنزَلَهُۥ بِعِلۡمِهِۦۖ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَشۡهَدُونَۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًا
Amma Allah Yanã shaida da abin da Ya saukar zuwa gare ka. Yã saukar da shi da saninSa. Kuma malã'iku sunã shaida. Kuma Allah Yã isa Ya zama shaida.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ قَدۡ ضَلُّواْ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka kange (wasu mutãne) daga hanyar Allah, haƙĩƙa, sun ɓace, ɓata mai nĩsa.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَظَلَمُواْ لَمۡ يَكُنِ ٱللَّهُ لِيَغۡفِرَ لَهُمۡ وَلَا لِيَهۡدِيَهُمۡ طَرِيقًا
Lalle ne waɗanda suka kãfirta, kuma suka yi zãlunci, Allah bai kasance Yana yi musu gãfara ba, kuma bã Ya shiryar da su ga hanya.
আরবি তাফসীরসমূহ:
إِلَّا طَرِيقَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٗا
Fãce hanyar Jahannama, sunã mãsu dawwama a cikinta har abada, kuma wannan yã kasance, ga Allah, mai sauƙi.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُمُ ٱلرَّسُولُ بِٱلۡحَقِّ مِن رَّبِّكُمۡ فَـَٔامِنُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ وَإِن تَكۡفُرُواْ فَإِنَّ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا تَغۡلُواْ فِي دِينِكُمۡ وَلَا تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ إِنَّمَا ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ رَسُولُ ٱللَّهِ وَكَلِمَتُهُۥٓ أَلۡقَىٰهَآ إِلَىٰ مَرۡيَمَ وَرُوحٞ مِّنۡهُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۖ وَلَا تَقُولُواْ ثَلَٰثَةٌۚ ٱنتَهُواْ خَيۡرٗا لَّكُمۡۚ إِنَّمَا ٱللَّهُ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓ أَن يَكُونَ لَهُۥ وَلَدٞۘ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا
Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, "Uku". Ku hanu (daga faɗin haka) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli.
আরবি তাফসীরসমূহ:
لَّن يَسۡتَنكِفَ ٱلۡمَسِيحُ أَن يَكُونَ عَبۡدٗا لِّلَّهِ وَلَا ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ ٱلۡمُقَرَّبُونَۚ وَمَن يَسۡتَنكِفۡ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَيَسۡتَكۡبِرۡ فَسَيَحۡشُرُهُمۡ إِلَيۡهِ جَمِيعٗا
Masĩhu bã ya ƙyãmar ya kasance bãwa ga Allah, kuma haka malã'ikun nan makusanta. Kuma wanda ya yi ƙyãmar bautarSa kuma yi yi girman kai, to, zai tãra su zuwa gare shi gabã ɗaya.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمۡ أُجُورَهُمۡ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضۡلِهِۦۖ وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱسۡتَنكَفُواْ وَٱسۡتَكۡبَرُواْ فَيُعَذِّبُهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا وَلَا يَجِدُونَ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to zã Ya cika musu ijãrõrinsu, kuma Yanã ƙãra musu daga falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyãma, kuma suka yi girman kai, to, zã Ya yi musu azãba, azãba mai raɗɗi kuma bã su samun wani masõyi dõmin kansu, baicin Allah, kuma bã su samun mataimaki.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ قَدۡ جَآءَكُم بُرۡهَٰنٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ نُورٗا مُّبِينٗا
Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa wani dalĩli daga Ubangijinku yã je muku kuma Mun saukar da wani haske, bayyananne zuwa gare ku.
আরবি তাফসীরসমূহ:
فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَٱعۡتَصَمُواْ بِهِۦ فَسَيُدۡخِلُهُمۡ فِي رَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَفَضۡلٖ وَيَهۡدِيهِمۡ إِلَيۡهِ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah kuma suka faku a gare Shi, to, zai shigar da su cikin wata rahama daga gare Shi da wata falala, kuma Ya shiryar da su zuwa gare Shi ga tafarki madaidaici.
আরবি তাফসীরসমূহ:
يَسۡتَفۡتُونَكَ قُلِ ٱللَّهُ يُفۡتِيكُمۡ فِي ٱلۡكَلَٰلَةِۚ إِنِ ٱمۡرُؤٌاْ هَلَكَ لَيۡسَ لَهُۥ وَلَدٞ وَلَهُۥٓ أُخۡتٞ فَلَهَا نِصۡفُ مَا تَرَكَۚ وَهُوَ يَرِثُهَآ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهَا وَلَدٞۚ فَإِن كَانَتَا ٱثۡنَتَيۡنِ فَلَهُمَا ٱلثُّلُثَانِ مِمَّا تَرَكَۚ وَإِن كَانُوٓاْ إِخۡوَةٗ رِّجَالٗا وَنِسَآءٗ فَلِلذَّكَرِ مِثۡلُ حَظِّ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۗ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ أَن تَضِلُّواْۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمُۢ
Sunã yi maka fatawa.* Ka ce: "Allah Yanã bayyana muku fatawa a cikin 'Kalãla."' Idan mutum ya halaka, ba shi da, rẽshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gãdon ta, idan wani rẽshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ('yan'uwa mãtã) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mãtã to namiji yana da misãlin rabon mãtã biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, dõmin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kõme.
* Bãyan dõgon bayãni a kan tauhĩdin Allah, da kõrħwar shubhõhin yahũdu da nasãra a cikin addĩni, dõmin sai zũciya tã yarda da kaɗaitar Allah sa'annan zã ta ji ƙarfin riƙo da ƙarfin ɗauka ga hukunce-hukuncen da Allah Ya ke azã mata. To, yã kõma ne ga abin karantãwar sũrar na tsaron dũkiyã, ya rufe ta da shi. Ya yi magana akan mas'alar 'kalãla', watau, mutum ya mutu bai bar reshen sa ba, ko wani asali mai fukã-fukai kawai, watau 'yan uwa maza ko mãta waɗanda ba li'ummai ba. Maganã akan li'ummai kuwa tã gabãta a farkon sũra. Anã gabãtar da shaƙĩƙi a kan li'abi, kuma ana gabãtar da na kusa akan na nesa, mafi kusantar zumunta. Ana ƙiyasin baiwa 'yã'yã mãtã biyu, biyu daga uku na dũkiya akan 'yan uwa mãtã, dõmin su ba a ce fiye da biyu ba. Ɗiyar tsatso ta fi 'yar'uwa ƙarfin zumunta, kuma ta fi kusanci.
আরবি তাফসীরসমূহ:
 
অর্থসমূহের অনুবাদ সূরা: সূরা আন-নিসা
সূরাসমূহের সূচী পৃষ্ঠার নাম্বার
 
কুরআনুল কারীমের অর্থসমূহের অনুবাদ - হাউসা ভাষায় অনুবাদ- আবূ বকর জুমী - অনুবাদসমূহের সূচী

হাউসা ভাষায় আল-কুরআনুল কারীমের অর্থসমূহের অনুবাদ। আবূ বকর মাহমূদ জুমী অনূদিত। অতপর মারকাযু রুওয়াদুদ তরজমার তত্ত্বাবধানে সংশোধিত। মূল অনুবাদ দেখারও সুযোগ রয়েছে, যাতে পাঠক পরামর্শ, মূল্যায়ন এবং ক্রমাগত উন্নয়ন করতে পারে।

বন্ধ