Übersetzung der Bedeutungen von dem heiligen Quran - Hausa Sprache * - Übersetzungen

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Übersetzung der Bedeutungen Vers: (36) Surah / Kapitel: Muhammad
إِنَّمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا لَعِبٞ وَلَهۡوٞۚ وَإِن تُؤۡمِنُواْ وَتَتَّقُواْ يُؤۡتِكُمۡ أُجُورَكُمۡ وَلَا يَسۡـَٔلۡكُمۡ أَمۡوَٰلَكُمۡ
Rãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai* ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba.
* Wãsã, shi ne dukan aiki wanda aka yi bã da nufin wata fa'ida ta addini ba, watau anã yin sa ne dõmin a sãmi abin aikatãwa a ɓãta lõkaci. Dukan ayyukan da mutum ya yi da nufin rãyuwar dũniya kawai, to, ya zama wãsã kõ dã cin abinci ne da karãtu. Kuma duk abin da mutum ya yi da niyyar bin umurnin Allah, wãjibi to ya zama aikin Lãhira kõ da cin abinci ne da jima'insa da matarsa, kamar yadda yake a cikin Hadĩsin Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Arabische Interpretationen von dem heiligen Quran:
 
Übersetzung der Bedeutungen Vers: (36) Surah / Kapitel: Muhammad
Suren/ Kapiteln Liste Nummer der Seite
 
Übersetzung der Bedeutungen von dem heiligen Quran - Hausa Sprache - Übersetzungen

Übersetzung der Quran-Bedeutung in Hausa von Abu Bakr Mahmoud Jomy, veröffentlicht von König Fahd Complex für den Druck des Heiligen Qur'an in Medina, gedruckt in 1434 H. Hinweis: Einige übersetzte Verse, korrigiert von Ruwwad Translation Center. Die Originalübersetzung steht für Anregungen, kontinuierliche Auswertung und Entwicklung zur Verfügung

Schließen