Check out the new design

Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa - Abubakar Gumi * - Teburin Bayani kan wasu Fassarori

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Fassarar Ma'anoni Aya: (256) Sura: Al'bakara
لَآ إِكۡرَاهَ فِي ٱلدِّينِۖ قَد تَّبَيَّنَ ٱلرُّشۡدُ مِنَ ٱلۡغَيِّۚ فَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلطَّٰغُوتِ وَيُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱسۡتَمۡسَكَ بِٱلۡعُرۡوَةِ ٱلۡوُثۡقَىٰ لَا ٱنفِصَامَ لَهَاۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Bãbu tĩlastãwa[1] a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ¦ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
[1] Abũbuwan bautãwa, iri biyu ne; Ubangijin da Yã aiko Muhammadu da wannan gaskiya da shiriya Shĩ ne Allah, da sauran iyãyen giji mãsu dõkõkin kai da na son zũkãta kamar nafsu da Shaiɗan, na aljannu da mutãne, mãsu ƙãga abin da suke so, su ƙira mutane a kansa ana ce musu Ɗãgũtu. Ya yi bayãnin sakamakon mabiyin kõwane irin bautawar. Sa'an nan ya biyar da ƙissõshi uku dõmin bayãnin abin da wannan magana ta ƙunsa; ta farko Namarũzu tãre da Ibrãhĩm, tanã nũna cewa mai mulki anã umurtar sa da bin Allah da taƙawa, idan ya bi son zũciyarsa, to, ya zama Ɗãgũtu. Allah zai halakar da shi. Ta biyu ƙissar Uzairu, tanã nũna cewa bãbu abin da yake da wuya ga Allah. Ta uku ƙissar Ibrãhim da yadda Allah ke rãyar da matattu, tanã nũna cewa bãbu laifi ka roƙi Allah Ya gãnar da kai dukan abin da ya shige maka duhu dõmin ka ƙãrã ĩmãni.
Tafsiran larabci:
 
Fassarar Ma'anoni Aya: (256) Sura: Al'bakara
Teburin Jerin Sunayen Surori Lambar shafi
 
Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa - Abubakar Gumi - Teburin Bayani kan wasu Fassarori

Fassarar Abu Bakr Mahmud Gumi. An sabunta ta ƙarƙashin kulawar Cibiyar fassara ta Ruwad, an bada damar karanta fassarar ta asali dan manufar bayyanar da ra'ayi da daidaitata da kuma ci gaba mai ɗorewa.

Rufewa