Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa * - Teburin Bayani kan wasu Fassarori

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Fassarar Ma'anoni Aya: (64) Sura: Suratu Aal'Imran
قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ كَلِمَةٖ سَوَآءِۭ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ أَلَّا نَعۡبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشۡرِكَ بِهِۦ شَيۡـٔٗا وَلَا يَتَّخِذَ بَعۡضُنَا بَعۡضًا أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُولُواْ ٱشۡهَدُواْ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ
Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi!* Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa** a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne."
* Mutãnen Littãfi sũ ne Yahũdu da Nasãra kõ da yake an ƙãre magana ne a kan Ĩsã, dõmin kira zuwa ga addini mai aƙĩda sahĩhiya ya haɗa kõwanensu. ** Kalma mai daidaitãwa ita ce kalmar shahãda dõmin tã tabbatar da cewa bãbu abin bautãwa fãce Allah. Bauta ita ce bin wani ga hukunce-hukunce na wajabtãwa kõ haramtãwa kõ halattãwa ko sanya wasu sharuɗɗa waɗanda sharĩ'a ba ta zo da suba. Wannan ãyã ba ta tsaya ga Yahũdu da Nasãra waɗanɗa suka ɗauki Ahbãr da Ruhbãn da mãsu ƙirƙira wasu hukunce-hukunce ba. A'a tã kai har ga Musulmi mãsu raunin hankali da ĩmãni, waɗanda suke zaton waliyyai sunã iya cũtãrwa, kõ sunã iya amfãnin wani da zãtinsu, kuma sunã iya halattãwar abin da Allah Ya haramta, kuma sunã iya haramtãwar abinda Ya halatta, tãre da haka kuma sunã ƙãga bidiõ'ĩ mãsu girma waɗanda Allah bai saukar da wani dalĩli a kansu ba, sunã sanya waɗannan bidi'õ'ĩ su zama ɗarĩƙu ga waɗannan waliyyan. Sunã riya cewa sũ ne mãsu ceton mutum kõ da suke sunã sãɓã wa sharĩ'a, sunã zaton cewa sunã kan wani abu. To, sũ ne maƙaryata, Shaiɗan yã rinjãye su har ya mantar da su daga tuna Allah. Waɗannan sũ ne ƙungiyar Shaiɗan. (Dubi Sãwi).
Tafsiran larabci:
 
Fassarar Ma'anoni Aya: (64) Sura: Suratu Aal'Imran
Teburin Jerin Sunayen Surori Lambar shafi
 
Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa - Teburin Bayani kan wasu Fassarori

ترجمة معاني القرآن الكريم إلى اللغة الهوسا، ترجمها أبو بكر محمود جومي. تم تصويبها بإشراف مركز رواد الترجمة، ويتاح الإطلاع على الترجمة الأصلية لغرض إبداء الرأي والتقييم والتطوير المستمر.

Rufewa