Check out the new design

Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa - Abubakar Gumi * - Teburin Bayani kan wasu Fassarori

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Fassarar Ma'anoni Sura: Fussilat   Aya:
إِنَّ ٱلَّذِينَ قَالُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُ ثُمَّ ٱسۡتَقَٰمُواْ تَتَنَزَّلُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ أَلَّا تَخَافُواْ وَلَا تَحۡزَنُواْ وَأَبۡشِرُواْ بِٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي كُنتُمۡ تُوعَدُونَ
Lalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shĩ ne Allah," sa'an nan suka daidaitu, malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) "Kada ku ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun kasance anã yi muku wa'adi da ita."
Tafsiran larabci:
نَحۡنُ أَوۡلِيَآؤُكُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَشۡتَهِيٓ أَنفُسُكُمۡ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَدَّعُونَ
"Mũ ne majibintanku a cikin rãyuwar dũniya da kuma a cikin Lãhira, kuma a cikinta kunã da abin da rãyukanku ke sha'awa, kuma kunã da abin da kuke kira (akawo muku) a cikinta.
Tafsiran larabci:
نُزُلٗا مِّنۡ غَفُورٖ رَّحِيمٖ
"A kan liyãfa daga Mai gafara, Mai jin ƙai."
Tafsiran larabci:
وَمَنۡ أَحۡسَنُ قَوۡلٗا مِّمَّن دَعَآ إِلَى ٱللَّهِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا وَقَالَ إِنَّنِي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ
Kuma wãne ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na ƙwarai kuma ya ce: "Lalle nĩinã daga mãsu sallamãwar al'amari zuwa ga Allah?"
Tafsiran larabci:
وَلَا تَسۡتَوِي ٱلۡحَسَنَةُ وَلَا ٱلسَّيِّئَةُۚ ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ فَإِذَا ٱلَّذِي بَيۡنَكَ وَبَيۡنَهُۥ عَدَٰوَةٞ كَأَنَّهُۥ وَلِيٌّ حَمِيمٞ
Kuma kyautatãwa bã ta daidaita kuma haka mũnanãwa. Ka tunkuɗe cũta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibinci ne, masoyi.
Tafsiran larabci:
وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ذُو حَظٍّ عَظِيمٖ
Kuma bã za a cũsa wa kõwa wannan hãli ba fãce waɗanda suka yi haƙuri, kuma bã zã a cũsa shi ba fãce ga mai rabo mai gima.
Tafsiran larabci:
وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ نَزۡغٞ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Kuma idan wata fizga ta fizge ka daga Shaiɗan, to ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Masani.
Tafsiran larabci:
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيۡلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُۚ لَا تَسۡجُدُواْ لِلشَّمۡسِ وَلَا لِلۡقَمَرِ وَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ
Kuma akwai daga ãyõyin Sa, dare da yini, da rãnã da watã. Kada ku yi sujada ga rãnã, kuma kada ku yi ga watã. Kuma ku yi sujada ga Allah wanda Ya halitta su, idan kun kasance Shĩ ne kuke bauta wa.
Tafsiran larabci:
فَإِنِ ٱسۡتَكۡبَرُواْ فَٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ يُسَبِّحُونَ لَهُۥ بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَهُمۡ لَا يَسۡـَٔمُونَ۩
To, idan sun yi girman kai, to, waɗanda ke a wurin Ubangijinka, sunã tasbĩhi a gare Shi, a dare da rana, alhãli kuwa sũ, bã su ƙõsãwa.
Tafsiran larabci:
 
Fassarar Ma'anoni Sura: Fussilat
Teburin Jerin Sunayen Surori Lambar shafi
 
Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa - Abubakar Gumi - Teburin Bayani kan wasu Fassarori

Fassarar Abu Bakr Mahmud Gumi. An sabunta ta ƙarƙashin kulawar Cibiyar fassara ta Ruwad, an bada damar karanta fassarar ta asali dan manufar bayyanar da ra'ayi da daidaitata da kuma ci gaba mai ɗorewa.

Rufewa