A gabãni, suna shiryar da mutãne, kuma Ya saukar da littattafai mãsu rarrabẽwa. Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, suna da azãba mai tsanani. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azãbar rãmuwa.
Shi ne wanda ya saukar da Littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma waɗanda yake a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya san tãwĩlinsafãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: "Mun yi ĩmãni da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta hankula.
Kamar ɗabi'ar mutãnen Fir'auna da waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata ãyõyinMu, sai Allah Ya kãmã su sabõda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne.
"Lalle ne wata ãyã tã kasance a gare ku a cikin ƙungiyõyi biyu da suka haɗu; ƙungiya guda tana yãƙi a cikin hanyar Allah, da wata kãfira, suna ganin su ninki biyu nãsu, a ganin ido. Kuma Allah Yana ƙarfafa wanda Yake so da taimakonSa. Lalle ne a cikin wannan, hakĩƙa, akwai abin kula ga maabũta basĩra.
An ƙawata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da ɗiya da dũkiyõyi abũbuwan tãrãwa daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi ne dãɗin rãyuwar dũniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take.
Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alhẽri daga wannan? Akwai gidãjen Aljanna a wurin Ubangiji sabõda waɗanda suka bi Shi da taƙawa, kõguna suna gudãna daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da mãtan aure tsarkakakku, da yarda daga Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa.
Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce Shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face Shi, Mabuwãyi, Mai hikima.
Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci. Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓã ba, fãce a bãyan ilmi ya je musu, bisa zãlunci a tsakãninsu. Kuma wanda ya kãfirta da ãyõyin Allah, to, lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako ne.
To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: "Nã sallama fuskata ga Allah, kuma wanda ya bi ni (haka)." Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai:* "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa.
* Ummiyyi shi ne wanda bai iya karatu da rubutu ba. A cikin Alƙur'ãni anã nufin Lãrabawa da wannan sunan, dõmin bã su da wani littãfin sama da suke da shi a lõkacin nan. Amma ba ana nufin bã su da rubutu ba. Haruffan rubutun Alƙur'ãni tun a zamãnin Ismã'ila ɗan Ibrãhĩma aka san su. Kuma a cikin Lãrabãwa da yawa sun san su, har sunã rubuta ƙasĩdu mãsu kyau, suna rãtayewa a cikin Ka'aba. Jahiliyya ita ce lõkacin da bã a aiki da wani littãfi na sama kamar yadda mafi yawan mutãne suke a yanzu, ƙarnin ishirin shi ma ƙarnin wata Jahiliyya ne.
Lalle ne waɗanda suke kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Annabãwa bã da wani hakki ba, kuma suna kashe waɗanda ke umurni da yin ãdalci daga mutãne, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
Shin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata ƙungiya daga cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa?
Wannan kuwa, dõmin lalle ne su sun ce: "Wutã bã zã ta shãfe mu ba, fãce a 'yan kwãnaki ƙidãyayyu." Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya rũɗẽ su a cikin Addinin su.
To, yãya idan Mun tãra su a yini wanda bãbu shakka a cikinsa, kuma aka cikã wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhãli kuwa, sũ bã zã a zãlunce su ba?
Ka ce:* "Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne."
* Wato ka mayar da ĩkon kõme ga Allah, yana yin sa yandaYake so, bãbu mai iya hanãwa, sa'an nan kuma ka ce wa mũminai, kada su yi wata mu'amala da kãfirai, su bar yan'uwansu mũminai, sai dai a kan lalũra kawai. Wanda ya riƙi kãfirai ya bar mũminai, to, bã shi tãre da Allah a cikin kõme.
"Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba."
Kada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makõma take.
Ka ce: "Idan kun ɓõye abin da ke a cikin ƙirãzanku, kõ kuwa kun bayyana shi, Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah a kan kõwane abu Mai ĩkon yi ne."
A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata daga alhẽri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhãli yana gũrin, dã dai lalle a ce akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Kuma Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyin Sa.
A lõkacin da mãtar Imrãna* ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani."
* Mãtar Imrãna sunanta Hannatu ɗiyar fãƙũza, bã ta haifuwa, sai wata rãna ta ga tsuntsuwa tanã ciyar da tsãkonta, sai ta yi sha'awar sãmun ɗa sabõda haka ta rõki Allah Ya bã ta ɗa. Da mijinta Imrãna ya tãke ta sai ta sãmi ciki, dõmin murna sai ta yi alkwarin 'yanta shi da bakance ga Masallacin Baitil Muƙaddas dõmin ya riƙa yi masa hidima. To, a lõkacin da ta haihu sai ta sãmi ɗiya mace. Ga shari'arsu bã a 'yanta mace ga irin wannan aiki na hidimar masallaci, dõmin haka ta nemi uzuri da cewa ta haife ta mace, mace bã kamar namiji take ba. Har ta yi ruɗu ta jũya, ta ce, namijin bã kamar mace ba, dõmin namiji ne a cikin zũciyarta.
To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu* kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe."
* Maryam, ma'anarta mai ibãda. Abinci da ake kai mata a cikin Masallaci shĩ ne 'ya'yan itãce, irin na ɗãri, a lõkacin bazara, kuma irin na bazara a lõkacin ɗãri. Wannan kuma ya mõtsar da begen zakariyya ga sãmun ɗã, bãyan shi da mãtarsa sun tsũfa ba su haifu ba. Sai ya rõƙi Allah kuma Ya karɓa masa, Ya ba shi Yahaya Annabi.
Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe Zakariyya ya shiga masallãci, a gare ta, sai ya sãmi abinci a wurinta. (Sai kuwa) ya ce: "Yã Maryamu! Daga ina wannan yake gare ki?" (Sai) ta ce: "Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba."
Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin masallãci. (Suka ce), "Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga sãlihai."
Ya ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya sãme ni, kuma mãtãta bakarãriya ce?" Allah ya ce, "Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so."
Ya ce: "Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma!" (Allah) Ya ce "Alãmarka ita ce ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe."
Wannan yana daga lãbarun* gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma**.
* Wannan yana daga cikin dalĩlan annabcin Annabi Muhammad, tsira da aminci su tabbata a gare shi, wajen faɗar lãbãrin abin da bai halarta ba. ** Uwar Maryamu tã ɗauke ta, tã kai ta ga Bani kãhin ɗan Hãrũna ɗan'uwan MũSã, a lõkacin nan, sũ ne suke tsaron Baitil Muƙaddas, ta mĩka musu ita, ta ce: "Ku karɓa. Na 'yantar da ita, kuma mace mai haila bã ta shiga masallaci, kuma bã zan mayar da ita a gidanã ba." Sai suka ce: "Wannan ɗiyar limãminmu ce kuma shugaban Ƙurbãninmu." Zakariyya ya ce: "Ku bã ni ita dõmin innarta tanã tãre da ni." Su ka ce: "Rãyukanmu bã su iya barin ta ga wani." Sai suka yi ƙuri'a da alƙalumansu da suke rubũtun Attaura da su. Sai Zakariyya ya rinjãya. An ce sun tafi kõgin Urdun ne suka jefa alƙaluman nãsu, a kan cewa wanda alƙalaminsa bai bi ruwa ba, ya tsaya, shĩ ne ya rinjãya. Sai Zakariyya ya rinjãya, ga shi kuma shĩ ne shugabansu, kuma malaminsu, kuma annabinsu, sai ya sanya ta a cikin bene, a cikin masallacin sa.
A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta.
Ta ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba?" (Allah) Ya ce: "Kamar wannan ne, Allah yana halittar abin da Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, "Ka kasance!, Sai yana kasancẽwa."
Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga Bani Isrãila'ĩla (da sãko, cẽwa), Lalle ne, ni haƙĩƙa nã zõ muku, da wata ãyã daga Ubangijinku. Lalle ne ni ina halitta muku daga lãka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hũra a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makãho da kuturu, kuma ina rãyar da matottu, da izibin Allah. Kuma ina gayã muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyẽwa acikin gidãjenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyã a gare ku, idan kun kasance mãsu yin ĩmãni.
"Kuma inã mai gaskatãwa ga abin da yake a gabãnina daga Taurata. Kuma (nãzo) dõmin in halatta muku sãshen abin da aka haramta muku. Kuma nã tafo muku da wata ãyã daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.
To, a lõkacin da Ĩsa ya gane kãfirci daga gare su, sai ya ce: "Su wãne ne mataimakãna zuwa ga Allah?" Hawãriyãwa suka ce: "Mu ne mataimakan Allah. Mun yi ĩmani da Allah. Kuma ka shaida cẽwa lalle ne mu, mãsu sallamãwa ne.
A lõkacin da Ubangiji Ya ce: "Ya Ĩsa! Lalle NĨ Mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kãfirta, kuma Mai sanya waɗanda suka bĩ ka a bisa waɗanda suka kãfirta har Rãnar ¡iyãma. Sa'an nan kuma zuwa gare Ni makõmarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakãninku, a cikin abin da kuka kasance kuna sãɓã wa jũna.
Lalle ne misãlin Ĩsã a wurin Allah kamar misãlin Ãdama ne, (Allah) Yã halitta shi daga turɓãya, sa'an nan kuma Ya ce masa: "Ka kasance: "Sai yana kasancewa.
To, wanda ya yi musu* da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirãyi, 'yã'yanmu da 'yã'yanku da mãtan mu da mãtanku da kanmu da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar, Allah a kan maƙaryata."
* Wanda ya yi hujjacewa da Annabi a kan sha'anin Ĩsã; kamar Nasãran Najrãn, sun tafi dõmin su yi jãyayya da Annabi. Ya kira su zuwa ga mubãhala, suka ce: sai sun yi shãwara, suka ce wa jũnansu: "Kun san gaskiya mutumin nan Annabi ne. Ku bar ra'ayinku na mubãhala, dõmin wani Annabi bai taɓa yin ta tãre da wasu mutãne ba, fãce sun halaka." Bãyan haka suka iske Annabi yã fito shi da Hasan da Husaini da Fãtima da Ali, kuma ya ce musu: "ldan na yi addu'a ku ce, Ãmin." Sai suka ƙi mubahãlar, suka yi sulhu akan jizya.
Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi!* Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa** a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne."
* Mutãnen Littãfi sũ ne Yahũdu da Nasãra kõ da yake an ƙãre magana ne a kan Ĩsã, dõmin kira zuwa ga addini mai aƙĩda sahĩhiya ya haɗa kõwanensu. ** Kalma mai daidaitãwa ita ce kalmar shahãda dõmin tã tabbatar da cewa bãbu abin bautãwa fãce Allah. Bauta ita ce bin wani ga hukunce-hukunce na wajabtãwa kõ haramtãwa kõ halattãwa ko sanya wasu sharuɗɗa waɗanda sharĩ'a ba ta zo da suba. Wannan ãyã ba ta tsaya ga Yahũdu da Nasãra waɗanɗa suka ɗauki Ahbãr da Ruhbãn da mãsu ƙirƙira wasu hukunce-hukunce ba. A'a tã kai har ga Musulmi mãsu raunin hankali da ĩmãni, waɗanda suke zaton waliyyai sunã iya cũtãrwa, kõ sunã iya amfãnin wani da zãtinsu, kuma sunã iya halattãwar abin da Allah Ya haramta, kuma sunã iya haramtãwar abinda Ya halatta, tãre da haka kuma sunã ƙãga bidiõ'ĩ mãsu girma waɗanda Allah bai saukar da wani dalĩli a kansu ba, sunã sanya waɗannan bidi'õ'ĩ su zama ɗarĩƙu ga waɗannan waliyyan. Sunã riya cewa sũ ne mãsu ceton mutum kõ da suke sunã sãɓã wa sharĩ'a, sunã zaton cewa sunã kan wani abu. To, sũ ne maƙaryata, Shaiɗan yã rinjãye su har ya mantar da su daga tuna Allah. Waɗannan sũ ne ƙungiyar Shaiɗan. (Dubi Sãwi).
Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke hujjacẽwa a cikin sha'anin lbrãhĩma, alhãli kuwa ba a saukar da Attaura da injĩla ba fãce daga bãyansa? Shin bã ku hankalta?
Gã ku yã waɗannan! Kun yi hujjacẽwa a cikin abin da yake kunã da wani ilmi game da shi, to, don me kuma kuke yin hujjacẽwa a cikin abin da bã ku da wani ilmi game da shi? Allah yana sani, kuma kũ, ba ku sani ba!
Ibrãhĩma bai kasance Bayahũde ba, kuma bai kasance Banasãre ba, amma yã kasance mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamãwa, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
Lalle ne mafi hakkin mutãne da Ibrãhĩma haƙĩƙa, sũ ne waɗanda suka bi shi a (zamaninsa) da wannan Annabi (Muhammadu) da waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma Allah ne Majiɓincin mũminai.
Kuma wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi ta ce: "Ku yi ĩmãni da abin da aka saukar a kan waɗanda suka yi ĩmãni (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kãfirta a ƙarshensa; tsammãninsu, zã su kõmõ."
"Kada ku yi ĩmãni fãce* da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cẽwa an bai wa wani irin abin da aka bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne, Masani."
* Maganganu sun shiga jũna dõmin a yi raddin kõwace guntuwar magana da jawãbin da ya dãce da ita tãre da ita. A lũra da kyau.
Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri,* zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai.**" Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane.
* Ƙinɗar Shi ne ũƙiyya dubũ gõma sha biyu, kuma ũƙiyya ɗaya tanã daidai da dirhami dubũ biyu da ɗari biyar kõ dĩnari dubu. ** Bãbu laifi idan mun ci dũkiyarsu: Watau Bayahũde yana ganin cin dũkiyar wanda bã Bayahũde ba irinsa halal ne a gare shi.
Lalle ne waɗanda suke sayen 'yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da rantsuwõyinsu, waɗannan bãbu wani rabo a gare su a Lãhira, Kuma Allah bã Ya yin magana da su, kuma bã Ya dũbi zuwa gare su, a Rãnar ¡iyãma, kuma bã Ya tsarkake su, kuma sunã da Azãba mai raɗaɗi.
Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da Littãfi dõmin ku yi zaton sa daga Littãfin, alhãli kuwa bã shi daga Littãfin. Kuma suna cẽwa: "Shi daga wurinAllah yake." Alhãli kuwa shi, bã daga wurin Allah yake ba. Sunã faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa sunã sane.
Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa mutãne: "Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah." Amma (zai ce): "Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin da kuka kasance kuna karantar da Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa."*
* Wannan ya nũna karatun Alƙur'ãni kawai bã da sanin ma'anarsa ba, dõmin a yi aiki da shi, ba ya isar mutum. Amman wanda ya kõyi ibãda sõsai, sa'an nan ya karanta Alƙur'ãni, to, zã a bã shi lãda kõ dã ba ya fahimtar ma'anarsa.
Kuma ba ya umurnin ku da ku riƙi malã'iku da annabãwa lyãyengiji. Shin, zai umurce ku da kãfirci ne a bãyan kun riga kun zama mãsu sallamãwa (Musulmi)?
Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin Annabãwa: "Lalle ne ban bã ku wani abu ba daga Littãfi da hikima, sa'an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku; lalle ne zã ku gaskata Shi, kuma lalle ne zã ku taimake shi." Ya ce: "Shin, kun tabbatar kuma kun riƙi alkawarĩNa a kan wannan a gare ku?" suka ce: "Mun tabbatar." Ya ce: "To, ku yi shaida, kuma Nĩ a tãre da ku Inã daga mãsu shaida."
Shin wanin Addinin Allah suke nẽma, alhãli kuwa a gare Shi ne waɗanda ke cikin sama da ƙasa suka sallama wa, a kan sõ da ƙĩ, kuma zuwa gare Shi ake mayar da su?
Ka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne."
Yãya Allah zai shiryar da mutãne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, kuma sun yi shaidar cẽwa, lalle Manzo gaskiya ne, kuma hujjõji bayyanannu sun je musu? Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Lalle ne wanɗanda suka kãfirta, kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai to bã zã a karɓi cike da ƙasa na zinãri daga ɗayansu ba, kõ dã ya yi fansa da shi, waɗannan sunã da azãba mai raɗaɗi, kuma bã su da wasu mataimaka.
Dukan abinci yã kasance halal ne ga Bani lsrã'ĩla, fãce abinda Isrã'ĩla ya haramta wa kansadaga gabãnin saukar da Attaura. Ka ce: "To, ku zo da Attaura sa'an nan ku karantã ta, idan kun kasance mãsu gaskiya ne.
Kuma lalle ne, ¦aki na farko* da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka** mai albarka kuma shiriya ga tãlikai.
* Ɗãkunan Allah a cikin ƙasa dõmin mutãne su yi ibãda zuwa gare su biyu ne; Ka'aba a Makka da Baitil Muƙaddas. An gina Ka'aba a gabaninsa da shekara arba'in. Dãkin Bakka kuwa Ibrãhĩma ne ya gina shi alhãli Yahũdu da Nasãra sunã cewa kan addininsa suke. Dã sunã faɗar gaskiya dã sun kõma a gare shi gabã ɗaya. ** Ana ce wa Makka Bakka.
A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai.
Ka ce: "Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani."
Kuma yãyã kuke kãfircẽwa alhãli kuwa anã karanta ãyõyin Allah a gare ku, kuma a cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nẽmi tsari da Allah, to, an shiryar da shi zuwa ga hanya miƙaƙƙiya.
Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gãɓar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta, Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu.
Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna umurnida alhẽri, kuma suna hani dagaabin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara.
A rãnar da wasu fuskõki suke yin fari kuma wasu fuskõki suke yin baƙi (zã a ce wa waɗanda fuskokinsu suke yin baƙin): "Shin kun kãfirta a bayan ĩmãninku? Don haka sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci."
Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawan su fãsiƙai ne.
An dõka ƙasƙanci a kansu a inda duk aka sãme su fãce da wani alkawari daga Allah, da alkawari daga mutãne. Kuma sun kõma da fushi daga Allah, kuma aka dõka talauci a kansu. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe annabãwa, bã da wani haƙƙi ba. Wannan kuwa dõmin sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi.
Ba su zama daidai ba; daga Mutãnen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye, suna karãtun ayõyin Allah a cikin sã'õ'in dare, alhãli kuwa sunã yin sujada.
Suna ĩmãni da Allah da Yinin Lãhira, kuma suna umurui da abin da aka sani kuma suna hani daga abin da ba a sani ba, kuma sunã gaugãwa a cikin alhẽrai. Kuma waɗannan suna cikin sãlihai.
Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne.
Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne waɗanda suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi abõkan asĩri daga waninku, ba su taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Haƙĩka, ƙiyayya tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke ɓõyẽwane mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta.
Gã ku yã waɗannan! Kunã son su bã su son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukansa. Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce "Mun yi ĩmani". Kuma idan sun kaɗaita sai su ciji yãtsu a kanku don takaici. Ka ce "Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza."
Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bã ya cũtar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne.
Kuma a lõkacin* da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani.
* Misãli ne ga cewa idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, to, ƙullinsu bã ya cũtar da ku da kõme, dõmin abin da ya auku a Yãƙin Uhdu ya isa misãli ga cewa, sai kun karkace daga hanya sa'an nan wani abu zai sãme ku. Asalin maganar shĩ ne, Annabi yã fita Uhdu da mutum ɗari tara da hamsin kuma kãfirai sunã dubũ uku. Annabi ya sauka a Uhdu rãnar Asabat, bakwai ga Shawwal, shekara ta uku ga Hijira, ya sanya bayansa wajen dũtsen Uhdu, ya gyãra safũfuwan mayãƙa, kuma ya zaunar da wata runduna ta maharba a gefen dũtsen da shugabancin Abdullahi ɗan Jubair. Sa'an nan ya ce musu: "Ku kãre mu da harbi, kada su zo mana daga bãya, kada ku ɗaga daga nan, mun rinjãya kõ an rinjãye mu." Sai suka sãɓãwa umurnin, don haka masĩfar Uhdu ta auku.
A lõkacin da ƙungiyõyi* biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara.
* Banũ salimah da Banũ Hãrisa sun tãshi kõmãwa gida su bar yãƙi, a lõkacin da Abdullahi bn Ubayyi bn Salũl ya kõma da jama'arsa, Allah Ya tsare musu ĩmãninsu, ba su kõma ba. Watau yana cewa idan wani abu na masĩfa ya sãme ku, to, kun sãɓãwa Allah ne kamar yadda ya auku a Uhdu, suka sanya Annabi ya fito daga Madĩna kuma maharba suka bar wurin da aka ayyana musu. Amma kuma ai Allah Ya Taimake ku, a Badar a lõkacin da ƙarfinku bai kai haka ba, sabõda rashin saɓawarku ga umurninSa.
"Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma."
Kuma Allah bai sanya shi* ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.
Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne.
Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa.
Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane.
Waɗannan sakamakonsu gãfara ce daga Ubangijinsu, daga Gidajen Aljanna (waɗanda) ƙõramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. Kuma mãdalla da ijãrar mãsu aiki.
Idan wani mĩki ya shãfe ku, to, lalle ne, wani mĩki kamarsa ya shãfi mutãnen, kuma waɗancan kwãnaki Muna sarrafa su a tsakãnin mutãne dõmin Allah Ya san waɗanda suka yi ĩmãni kuma Ya sãmi mãsu shahãda daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzãlumai.
Kuma Muhammadu bai zama ba face manzo lalle ne manzanni sun shũɗe a gabãninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, zã kujũya a kan dugaduganku? To, wanda ya jũya a kan dugadugansa, bã zai cũci Allah da kõme ba. Kuma Allah zai sãka wa mãsu gõdiya.
Kuma bã ya yiwuwa ga wani rai ya mutu fãce da iznin Allah, wa'adi ne mai ƙayyadadden ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon dũniya Muna bã shi daga gare ta. Kuma wanda ke nufin samakon Lãhira Muna bã shi daga gare ta. Kuma zã Mu sãka wa mãsu godiya.
Kuma da yawa wani Annabi wanda ya yi yãƙi, akwai jama'a mãsu yawa tãre da shi, sa'an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son mãsu haƙuri.
Kuma bãbu abin da ya kasance maganarsu fãce faɗarsu cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Ka gãfarta mana zunubanmu da ɓarnarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."
Zã Mu jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta sabõda shirkin da suka yi da Allah gãme da abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi. Kuma makõmarsu wuta ce, kuma tir da mazaunin azzãlumai!
Kuma lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lõkacin da kuka kãsa,* kuma kuka yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma kuka sãɓã a bãyan (Allah) Ya nũna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra. Sa'an nan kuma Ya jũyar da ku daga gare su, dõmin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Ya yãfe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga mũminai.
* A lõkacin da aka fãra Yãƙin Uhdu Musulmi suka fãra kõra sunã kisa sunã kãmu. Sai wasu maharba suka ce: "Kada a kãme ganĩma a bar mu," Shugabansu Abdullahi bn Jubair ya ce musu, "Ku tuna da maganar Manzon Allah da ya ce kada mu bar wurinmu sai idan shi ne ya kirãye mu." Sai suka ƙi saurãran maganarsa suka tafi kãmun ganima. Sai Allah Ya biyõ musu da Khãlid bn walĩd ta bãya, ya kashe Abdullahi da sauran waɗanda suka rage. Sa'an nan kuma sai yãƙĩn Musulmi ya karye, suka gudu suka hau dũtse, sai mutum gõma sha ɗaya ko shã biyu kawai aka bari tãre da Annabi, yana kiran su sunã gudu.
A lõkacin da kuke hawan dũtse, gudãne. Kuma ba ku karkata a kan kõwa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku a cikin na ƙarshenku.* Sa'an nan (Allah) Ya sãkã muku da baƙin ciki a tãre da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.
* Bãyan da hankalinsu ya kõma gare su sai suka ga sakamakon sãɓãwa umurnin Allah, ya zama karyewar yãƙi da rashin ganĩma.
Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bãyan baƙin cikin; gyangyaɗi yanã rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rãyukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: "Da munã da wani abu daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã waɗanda aka rubũta musu kisa sun fita zuwa ga wurãren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu yã auku ne) dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.
Lalle ne waɗanda suka jũya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talãlãɓantar da su, sabõda sãshen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yãfe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gãfara Mai haƙuri.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan, sun yi tafiya a cikin ƙasa kõ kuwa suka kasance a wurin yãƙi: "Dã sun kasance a wurinmu dã ba su mutun ba, kuma dã ba a, kashe su ba." (Wannan kuwa) Dõmin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu. Kuma Allah ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani ne.
Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara* da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali.
* Annabi shi ne makomar al'amurra ga dukkan kome, amma Allah Ya lizimta masa sauƙin hali zuwa ga sahabbansa, da yin ma'ãmala da su, ma'ãmala mai kyau, da yi musu addu'a a kõwane hãli, kuma a wurin yãƙi kõ abin da ya shãfi yãƙi, Yã lizimta masa ya yi shãwara da su, kuma Ya bã shi damar yin ijtihãdi a nan, sa'an nan Ya umurce shi daya dõgara ga Allah wajen zartaswa, a kan ra'ayin da ya gani daga gare su.
Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake taimakon ku bãyanSa? Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara.
Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu.* Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba.
* Gulũlu shĩ ne satar wani abu daga ganimar yãƙi a gabãnin raba ta a tsakãnin mayãka. Allah Yã ce, "Yin gulũlu haram ne a kan kõwane annabi ko da waɗanda ba a halatta wa cin ganima ba, balle ga wanda aka halatta wa. Kamar yadda gulũlu yake haram a kan annabãwa haka yake haram a kan mabiyansu.".
Sũ, darajõji* ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa.
* Mũminai mãsu darajõji ne a wurin Allah gwargwadon ĩmãninsu da taƙawarsu da kuma falalar da Allah Ya yi musu. Haka sũ kuma kãfirai sunã da magangara zuwa ƙasa gwargwadon mugun aikinsu.
Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala* a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya.
* Allah Yã nũna falalar da Ya bai wa Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da yake har yanã yi wa mũminai gõri da kyautar da Ya yi musu ta hanyar aiko musu shi.
Shin kuma a lõkacin* da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku** yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne.
* Duk masĩfar da ta sãme ku, tõ, ku ne kuka jãwo wa kanku ita da wani laifi na sãɓãwa umurnin Allah. Kuma kãmin masĩfa guda ta sãme ku, to, alheri biyu sun sãme ku. ** Kowace irin masĩfa ta sãmi mutum, to, shĩ ne ya yi sababinta a kansa. Kuma yã kamata ya yi bincike ya gãne sababin, a inda ya jãhilce shi. Kuma duk da haka kãmin masĩfa guda ta sãme shi, ya sãmi ni'ima biyu kõ fiye da haka.
Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe.*" Suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku." Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa.
* Ku tunkuɗe mana maƙiyã da duhunku, kõ dã ba ku yi yãƙi ba.
Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: "Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya."
Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu*. Ana ciyar da su.
* A cikin Hadisi an ruwaito cewa, Annabi yã ce Allah Yanã sanya rũhinsu a cikin cikkunan tsuntsãye mãsu kõren launi, sunã tafiya da su a cikin Aljanna sunã ci daga 'ya'yan itãcenta da rãna, sa'an nan su kõma zuwa ga wasu fitillu waɗanda aka rãtaye a cikin inuwar Al'arshi.
Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; "Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba."
Waɗanda suka karɓa* kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata** yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa.
* Bayan kõmawar Musulmi daga Uhdu da miyãkun da suka sãme su, sai Annabi ya umurce su da fita a bãyan kãfirai, dõmin kada su yi tunãnin kõmãwa. Sai suka fita bãyansu, aka dãce kuwa Abu Sufyãna ya umurci mutãnensa da kõmawa Madĩna dõmin su tumɓuke Musulmi. An yi Uhdu ta farko ran Asabat, sa'an nan suka fita a bãyansu a rãnar Lahadi, suka riske su a Hamra'al Asad. Sai aka yi tawãfuƙi (yarjejeniya) tsakanin Annabi da Abu Sufyãna a kan a bar yãƙi a lõkacin, sai shekara mai zuwa, a haɗu a Badar. Allah Ya yabi Musulmi, da suka karɓa wannan kira, a cikin miyãkũ. Haka duka mai karɓawa irinsu, yã shiga a cikin irin wannan yabo har ya zuwa tãshin Ƙiyãma. ** Kyautata yi shi ne tsarkake aiki dõmin Allah watau ihsani kõ ihlasi.
Waɗanda mutãne* suka ce musu: "Lalle ne, mutãne sun tãra (rundunõni) sabõda ku, don haka ku ji tsõrnsu. Sai (wannan magana) ta ƙara musu ĩmãni, kuma suka ce: "Mai isarmu Allah ne kuma mãdalla da wakili Shĩ."
* Yãƙin Badar na Uku, a cikin shekara ta huɗu yake, a watan Sha'aban. Badar kãsuwa ce babba ga ƙabĩlun Lãrabãwa a kõwace shekara. A bãyan Uhdu an yi alkawari da Abu Sufyãna, a kan a haɗu a Badr shekara mai zuwa. Sabõda haka sai Abu Sufyãna ya fita daga Makka har ya sauka Marriz zahrãn, sai Allah Ya sanya masa tsõro a cikin zũciyarsa sai ya gamu da Nu'aima bn Mas'ũd el Ashja'iy, ya ce masa: "Ni nã yi alkawari da Muhammadu a kan mu haɗu a Kãsuwar Badar. Wannan kuwa shekar fari ce. Inã son sãɓãwar alkawarin ta zama daga gare shi, bã daga gare ni ba. Ka tafi Madĩna ka yi ƙõƙarin hana su fitõwa, zan bã ka rãƙuma gõma." Sai Nu'aimu ya tafi Madĩna ya iske Annabi da Sahabbansa suna shirin fita. Sai ya ce musu: "Me kuke nufi?" Suka ce; " Alkawarin Abu Sufyãna." Sai ya ce: "Bã zã ku iya ba, dõmin kuwa sun tãra rundunõni sabõda ku." Sai Annabi ya ce: "Zan fita kõ da nĩ kaɗai ne." Sai Annabi ya fita da mutum dubu da ɗari biyar, suka tafi Badar bãbu Abu Sufyãna. Suka ci kãsuwa suka kõmo.
Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma.
Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma.
Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa.
Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai* Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba.** Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa.*** Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma.
* Watau Allah bã zai bar mutãne su ce: 'Mun yi ĩmãni, da bãki kawai ba,' sai Yã jarraba su Ya fitar da mũminan ƙwarai daga munãfukai. Sabõda haka Ya sanya rãnaiku kamar rãnar Uhdu wadda Allah Ya jarrabi mũminai da ĩta har haƙurinsu da ɗã'arsu suka bayyana, kuma munãfukai suka bayyana. ** Allah bai sanar da gaibi ga mutãne waɗanda ba Annabãwa ba, sabõda haka bã ku iya sanin ĩmãnin mutum ko rashin ĩmãninsa, sai da alãma ta wani aikĩ ko magana wadda take da ita za a iya yin hukunci da kãfirci ko ĩmãnĩ ga mutum. *** Allah Yã zãɓi wanda Ya so daga manzanninSa, watau Yã zaɓi Annabi Muhammadu da ƙãrin daraja a kan sauran Annabãwa da falalarsa. Wannan ne mafificin yabo a gare shi.
Kuma kada waɗannan da suke yin rõwa da abin da Allah Ya bã su daga falalarSa su yi zaton shĩ ne mafi alhẽri a gare su A'a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu saƙandami da abin da suka yi rõwa da Shi a Rãnar ¡iyãma Kuma ga Allah gãdon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
Lalle ne, haƙĩƙa Allah Yã ji maganar waɗanda suka ce: "Lalle ne, Allah faƙĩri ne, mũ ne wadãtattu." za mu rubũta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: "Ku ɗanɗani azãbar gõbara!
Waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah Yã yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi ĩmãni sabõda wani Manzo sai yã zo mana da Baiko wadda wuta za ta ci." Ka ce: "Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabãnĩna, da hujjõji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance mãsu gaskiya?"
To, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske.
Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar ¡iyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi.
Lalle ne zã a jarraba* ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra.
* Duk wanda ya tsayu da gaskiya ko umurni da alheri, ko hani daga abin da ba a so, to lalle ne sai an cũtar dashi, kuma ba shi da mãgani sai haƙuri, dõmin Allah, da neman taimako daga Allah, da kõmãwa zuwa ga Allah.
Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa* Littãfi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba." Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye!
* A cikin wannan akwai gargaɗi ga mãlaman Musulmi, kada su shiga hanyar Yahũdu ta ɓõye ilmin gaskiya, ko kuwa abin da ya sãme su, sũ ma ya sãme su, kuma ya shiga da su mashigarsu. Wãjibi ne akan mãlamai su bãyar da abin da ke hannuwansu na ilmi mai amfãni, mai nũni a kan aikin ƙwarai, kada su ɓõye kõme daga gare shi. Idan sun ɓõye, to, la'anar Allah da malã'iku da ta mutãne zã ta tabbata a kansu, kamar yadda ta tabbata a kan mãlaman Yahũdu.
Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai raɗadi.
Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta.
"Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki.
"Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar Alkawari."
Sabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, "Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako.
Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa sunã da Gidãjen Aljanna (waɗabda) ƙoramu ke gudãna a ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyãfa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alhẽri ga barrantattu.
Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi* haƙĩƙa akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kaɗan da ãyõyin Allah. Waɗannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne.
* A cikin Mutãnen Littãfi akwai mutãnen ƙwarai na kirki waɗanda hãsada ba ta hana su bin gaskiya ba. Sun sifantu da sifõfin kamãla; watau ba dukkansu ne miyagu ba. Akwai na ƙwarai a cikinsu kamar yadda hãli yake a kõwane tãron mutãne.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku yi haƙuri kuma ku yi dauriya, kuma ku yi zaman dãko, kuma ku yi taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.*
* Haƙuri a kan ibãda da ɗaukar wahalõlin sharĩ'a gabãɗaya gwargwadon ĩkon yi. Dauriya a kan abokan gaba; watau kada maƙiya su fi mũminai haƙuri wajen yãƙi daɗaukar wahalõlinsa. Zaman dãko ga taushewar hanyõyin abõkan gaba daga barin shiga ƙasar Musulmi. Bãbu bambanci ga maƙiyi bayyananne da maƙiyi ɓõyayye. Maƙiyi ɓõyayye ya fi aibi dõmin kasancewarsa, zai shiga wuta, amma kasancewarsa maƙiyi bayyananne, zai shiga Aljanna. Taƙawa ita ce bin umuruin Allah da kangewa daga barin haninSa kamar yadda Ya faɗa. Wannan shĩ ne kan ibãda duka bãyan ĩmãni, dõmin haka ya ce kõ zã ku ci nasara, idan kun riƙe waɗannan abũbuwa da kyãwo.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
የፍለጋ ዉጤቶች:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".