ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي * - فهرس التراجم

XML CSV Excel API
تنزيل الملفات يتضمن الموافقة على هذه الشروط والسياسات

ترجمة معاني آية: (18) سورة: الرعد
لِلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِرَبِّهِمُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱلَّذِينَ لَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُۥ لَوۡ أَنَّ لَهُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفۡتَدَوۡاْ بِهِۦٓۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ سُوٓءُ ٱلۡحِسَابِ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ
Ga waɗanda* suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle dã sunã da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misãlinsa tãre da shi, haƙĩƙa, dã sun yi fansa da shi. Waɗancan sunã da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida.
* Bãyan da ya faɗi cewa Allah Yanã kira, kiran gaskiya a cikin ãyã ta l4, kuma waɗansu mutãne sun ƙi karɓar kiran Allah, sai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam, sai ya bayyana, a nan, sakamakon wanda ya karɓi kiran Allah sãmun ruwan sha, sabõda Mai abu ne Ya kirãwo shi, Ya kuma bã shi, ya sha a hankali kwance, sa'an nan kuma Allah zai bã shi abin da ya fi ruwan kyau, watau Aljanna. Amma wanda ya ƙi karɓãwa, to, yã yi hasãra biyu, bai sãmi ruwan da ya yi kiran wani ya bã shi ba, sa'an nan kuma ya haɗu da azãbar da take zai iya bãyar da dukan abin da ya mallaka dõmin ya yi fansar kansa da ita.
التفاسير العربية:
 
ترجمة معاني آية: (18) سورة: الرعد
فهرس السور رقم الصفحة
 
ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي - فهرس التراجم

ترجمة معاني القرآن الكريم إلى اللغة الهوسا، ترجمها أبو بكر محمود جومي. تم تصويبها بإشراف مركز رواد الترجمة، ويتاح الإطلاع على الترجمة الأصلية لغرض إبداء الرأي والتقييم والتطوير المستمر.

إغلاق