ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي * - فهرس التراجم

XML CSV Excel API
تنزيل الملفات يتضمن الموافقة على هذه الشروط والسياسات

ترجمة معاني آية: (106) سورة: المائدة
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ شَهَٰدَةُ بَيۡنِكُمۡ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ حِينَ ٱلۡوَصِيَّةِ ٱثۡنَانِ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ أَوۡ ءَاخَرَانِ مِنۡ غَيۡرِكُمۡ إِنۡ أَنتُمۡ ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةُ ٱلۡمَوۡتِۚ تَحۡبِسُونَهُمَا مِنۢ بَعۡدِ ٱلصَّلَوٰةِ فَيُقۡسِمَانِ بِٱللَّهِ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ لَا نَشۡتَرِي بِهِۦ ثَمَنٗا وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰ وَلَا نَكۡتُمُ شَهَٰدَةَ ٱللَّهِ إِنَّآ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡأٓثِمِينَ
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar* tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfar mutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi."
* Idan husuma ta auku a tsakãnin Musulmi da tsakãnin kãfirai, kuma su kãfiran suka zama mudda'a alaihim (waɗanda ake tuhuma), kuma bãbu wata shaida sai su, to, sai su yi rantsuwa a wurin ibãdarsu, a kan su ne da gaskiya, a hukumta musu da hakkin. Bayan haka, idan an sãmi wata shaida a kan ƙaryarsu ana warware hukuncin a bãyan mudda'i (mãsu ƙãra) biyu Musulmi sun yi rantsuwa cewa abin da waɗancan suka faɗa ƙarya ne, abin da shaidunsu suka yi shaida da shi, shi ne gaskiya.
التفاسير العربية:
 
ترجمة معاني آية: (106) سورة: المائدة
فهرس السور رقم الصفحة
 
ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي - فهرس التراجم

ترجمة معاني القرآن الكريم إلى اللغة الهوسا، ترجمها أبو بكر محمود جومي. تم تصويبها بإشراف مركز رواد الترجمة، ويتاح الإطلاع على الترجمة الأصلية لغرض إبداء الرأي والتقييم والتطوير المستمر.

إغلاق