ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي * - فهرس التراجم

XML CSV Excel API
تنزيل الملفات يتضمن الموافقة على هذه الشروط والسياسات

ترجمة معاني آية: (1) سورة: الممتحنة

سورة الممتحنة - Suratu Al'mumtahanah

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ عَدُوِّي وَعَدُوَّكُمۡ أَوۡلِيَآءَ تُلۡقُونَ إِلَيۡهِم بِٱلۡمَوَدَّةِ وَقَدۡ كَفَرُواْ بِمَا جَآءَكُم مِّنَ ٱلۡحَقِّ يُخۡرِجُونَ ٱلرَّسُولَ وَإِيَّاكُمۡ أَن تُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ رَبِّكُمۡ إِن كُنتُمۡ خَرَجۡتُمۡ جِهَٰدٗا فِي سَبِيلِي وَٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِيۚ تُسِرُّونَ إِلَيۡهِم بِٱلۡمَوَدَّةِ وَأَنَا۠ أَعۡلَمُ بِمَآ أَخۡفَيۡتُمۡ وَمَآ أَعۡلَنتُمۡۚ وَمَن يَفۡعَلۡهُ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩ Na kuma maƙiyinku masõyi, . Kuna jẽfa sõyayya* zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya.
* Wani Sahãbin Annabi da ake cewa Hãtibu bn Abi Balta'a, ya rubũta takarda zuwa ga Ƙuraishãwa yanã sanar da su cewa Annabi na zuwa garinsu da yãƙi, sai Allah Ya sanar da Annabi tun manzonsa bai isa ba ga Ƙuraishãwa, sai aka mayar da takardar. Da aka tambayi Hãtibu dalĩlin yin ta,sai ya ce dõmin yanã da ɗiya da dũkiya ne a can, dõmin haka ya so ya gaya musu zuwan Annabi kõ da yake yanã da cikakken ĩmãmin cewa Annabi gaskiya ne, kuma zai rinjãye su duk yadda aka yi. Sai Annabi ya karɓi uzurinsa, ba a yi masa kõme ba, sai dai abin da Allah Ya hana; kada Musulmi su sãke wata ma'amala da kãfirai a ɓõye, ko a bayyane sabõda dalĩlan da aka faɗa a cikin sũrar.
التفاسير العربية:
 
ترجمة معاني آية: (1) سورة: الممتحنة
فهرس السور رقم الصفحة
 
ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي - فهرس التراجم

ترجمة معاني القرآن الكريم إلى اللغة الهوسا، ترجمها أبو بكر محمود جومي. تم تصويبها بإشراف مركز رواد الترجمة، ويتاح الإطلاع على الترجمة الأصلية لغرض إبداء الرأي والتقييم والتطوير المستمر.

إغلاق