Alhãli kuwa sau nawa Muka *aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko!
* Tun da ba Mu bar mutãnen farko mãsu ɓarna ba, sai da Muka aika musu Manzanni, kuma kõwace ƙungiya daga cikin waɗanda aka aikawa wani Manzo sai da ta yi izgili game da Manzonsu, har abin ya kai ga halakar shũgabanninsu. To, haka mutãnenka, bã zã Mu bar su ba, sabõda ɓarnarsu, sai Mun aike ka zuwa gare su, su yi izgili game da kai, har a halaka shũgabanninsu, sa'an nan sauransu, su bi abin da aka umurce su da shi.
Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari).
Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba.
Kuma suka sanya *Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin.
* suka ce malã'iku 'ya'ya mãtane na Allah, sunã bauta musu ne dõmin su kusantar da su zuwa ga Allah, watau dõmin su cece su daga azãba. Sun yi wannan ƙarya ne dõmin su tabbatar da al'ãdarsu ta surkulle. Sabõda haka suka yi wa Allah ƙarya suka naƙasa shi da haka, kuma suka naƙasa malã'iku mãsu daraja a wurin Allah kuma suka kãfirce wa ni'imar da Allah Ya yi musu wajen aiko musu Manzo mai shiryar da su. Sa'an suka kafa hujja da ƙarya dõmin su danne gaskiya.
Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki.
Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su.
Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbansu."
(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi."
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun* nan biyu ba?"
* Sunã nufin Makka da tã'ifa, kuma sunã nufi a saukar da Alƙur'ãni ga walĩdu ɗan Mugĩra na Makka kõ ga Urwatu ɗan Mas'ũdi As saƙafi a Ta'ifa. Watau sunã sũkar Muhammadu dõmin bã shi da dũkiya. A gare su mai dũkiya shĩ ne babban mutum, wanda ya cancanta Allah Ya aiko shi ga mutãne.
Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci*), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa.
* Tun da ba Mu bar rabon abincin rãyuwarsu ta dũniya a hannunsu ba, to, ta yãya ne zã Mu bar babban abu kamar Annabci da shiryar da mutãne ga hannãyensu? Wãtau bã zai yiwu Mu yi ba sai yadda Muke so kawai, kõ su bi, kõ su kãfirta, duka daidai ne a gare Mu.
Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa.
Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!"
Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?"
Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli.* Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.
* Wãtau da aka ce gumãka damãsu bauta musu duka abincin wutar Jahannama ne kamar yadda yake a cikin sura ta 21 ãyã ta 98 da 99, sai suka ce sun yarda gumakansu su zama tãre da ɗan Maryama.
Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa*
* Dã Mun so dã Mun sanya ɗiyansu su zama malã'iku, su fi Ĩsa ɗan Maryama zama abin mãmãki ga halitta, sa'an nan su maye muku a cikin ƙasã maimakon ɗiya masu siffõfi irin na jikunkunanku. Zai fi zama abin mãmãki mutum yahaifi malã'ika bisa mace ta haifi ɗã bã da wani namiji yã kusance ta ba.
Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a."
Sai ƙungiyõyi *suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi!
* Nasãra suka kasu a cikin ƙungiyõyi a bayan Ĩsã. Ya'akubiyya, mãsu cewa Ĩsã ɗan Allah ne, da Malakãniyya, mãsu cewa Ĩsa ɗayan uku ne. Waɗansu kuma suka ce bãwan Allah ne watau su ne Musulminsu, kuma waɗansu daga Musulmin suka kãfirta a bãyan zakuwar, Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sabõda sun ƙi yarda da Annabcinsa. Yahũdu suka ce: "Ĩsã bã Annabi ba ne dan zina ne." Allah Ya la'ani kãfirai dukansu.
Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne.
Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurin Sa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
Kuma waɗanda suke kira baicin Sa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane* (da haka).
* Su waɗanda suka yi shaida da gaskiya sun san bãbu mai mallakar ceto ga wani fãce Allah. Sabõda haka Allah nã yi musu izni su ceci wanda Yake son su cece shi, ba wanda su suke so ba. Ma'anar iznin da ceto ga bãyin Allah sãlihai ita ce dõmin Allah Ya bayyana darajar mai ceton ne kawai, bã don yanã da wani hakki ba, ga Allah. Allah Ya tsarkaka daga wata halittar Sa ta sãmi wani hakki a kan Sa. Kõwa bãwan Sa ne.
Translation of the Meanings of the Noble Qur'an - Hausa language - Abu Bakr Jomy - Translations’ Index
Translation of the Quran meanings into Hausa by Abu Bakr Mahmoud Jomy. Corrected by supervision of Rowwad Translation Center. The original translation is available for suggestions, continuous evaluation and development.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
Search results:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".