Translation of the Meanings of the Noble Qur'an - Hausa language - Abu Bakr Jomy * - Translations’ Index

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Translation of the meanings Ayah: (101) Surah: Al-Mā’idah
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَسۡـَٔلُواْ عَنۡ أَشۡيَآءَ إِن تُبۡدَ لَكُمۡ تَسُؤۡكُمۡ وَإِن تَسۡـَٔلُواْ عَنۡهَا حِينَ يُنَزَّلُ ٱلۡقُرۡءَانُ تُبۡدَ لَكُمۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهَاۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin* da ake saukar da Alƙur'ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.
* Wannan lõkacin yã nuna shiɗai ne lõkacin saukar hukunci kõwane iri ne daga Allah. Wanda ya ce Annabi yã faɗa masa wani hukunci a kan wata matsala, bãyan rasuwarsa, tsĩra da aminci su tabbata gare shi, to, bã zã a karɓar masa ba, dõmin yã sãɓã wa nassin Alƙur'ãni. Kuma mafarki bã ya zama hujja, balle a ɗauke shi hukunci wanda ake yin aiki da shi. Mafarkin Annabãwa ko mafarkin da Annabãwa suka tabbatar shi ne gaskiya, saura kuma sai abin da ya bayyana, kuma bai sãɓã wa sharĩa ba.
Arabic explanations of the Qur’an:
 
Translation of the meanings Ayah: (101) Surah: Al-Mā’idah
Surahs’ Index Page Number
 
Translation of the Meanings of the Noble Qur'an - Hausa language - Abu Bakr Jomy - Translations’ Index

Translation of the Quran meanings into Hausa by Abu Bakr Mahmoud Jomy. Corrected by supervision of Rowwad Translation Center. The original translation is available for suggestions, continuous evaluation and development.

close