Check out the new design

Traducción de los significados del Sagrado Corán - Traducción al idioma hausa- Abu Bakr Jomy * - Índice de traducciones

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Traducción de significados Capítulo: Al-Maaida   Versículo:
وَلَوۡ أَنَّ أَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَكَفَّرۡنَا عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأَدۡخَلۡنَٰهُمۡ جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Kuma dã dai lalle Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dã Mun kankare miyãgun ayyukansu daga gare su, kuma dã Mun shigar da su gidãjen Aljannar Ni'ima.
Las Exégesis Árabes:
وَلَوۡ أَنَّهُمۡ أَقَامُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِم مِّن رَّبِّهِمۡ لَأَكَلُواْ مِن فَوۡقِهِمۡ وَمِن تَحۡتِ أَرۡجُلِهِمۚ مِّنۡهُمۡ أُمَّةٞ مُّقۡتَصِدَةٞۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ سَآءَ مَا يَعۡمَلُونَ
Kuma dã dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dã sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin ƙafãfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaitãwa kuma mãsu yawa daga gare su, abin da suke aikatawa yã munana.
Las Exégesis Árabes:
۞ يَٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ بَلِّغۡ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ وَإِن لَّمۡ تَفۡعَلۡ فَمَا بَلَّغۡتَ رِسَالَتَهُۥۚ وَٱللَّهُ يَعۡصِمُكَ مِنَ ٱلنَّاسِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Yã kai Manzo! Ka iyar da* abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancin Sa ba ke nan. Kuma Allah Yanã tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.
* Wannan ãya tã kãfirta dukan wanda ya ce kõ yã yarda da cewa Annabi yã ɓõye wani abu daga Allah, ko kuma yã keɓe wasu mutãne da wani abu daga manzancinsa daga Allah.
Las Exégesis Árabes:
قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَسۡتُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍ حَتَّىٰ تُقِيمُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُمۡۗ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗاۖ فَلَا تَأۡسَ عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ba ku zama a kan kõme ba, sai kun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku."Kuma lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yanã ƙara wa mãsu yawa daga gare su girman kai da kãfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai.
Las Exégesis Árabes:
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلصَّٰبِـُٔونَ وَٱلنَّصَٰرَىٰ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da Nasãra, wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su zamo sunã baƙin ciki ba.
Las Exégesis Árabes:
لَقَدۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَأَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمۡ رُسُلٗاۖ كُلَّمَا جَآءَهُمۡ رَسُولُۢ بِمَا لَا تَهۡوَىٰٓ أَنفُسُهُمۡ فَرِيقٗا كَذَّبُواْ وَفَرِيقٗا يَقۡتُلُونَ
Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isrã'ĩla, kuma Mun aiki manzanni zuwa gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da rãyukansu bã su so, wani ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sunã kashewa,
Las Exégesis Árabes:
 
Traducción de significados Capítulo: Al-Maaida
Índice de Capítulos Número de página
 
Traducción de los significados del Sagrado Corán - Traducción al idioma hausa- Abu Bakr Jomy - Índice de traducciones

Traducida por Abu Bakr Mahmud Jumi. Desarrollada bajo la supervisión del Centro Rowad Al-Taryamah. Se permite acceder a la traducción original con el propósito de brindar opiniones, evaluación y desarrollo continuo.

Cerrar