wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkin Sa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa.
Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana.
Kuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya kasance mai gargaɗi tãre da shi?
"Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare shi, yanã ci daga gare ta?" Kuma azzãlumai suka ce: "Bã ku bin kõwa, fãce mutum sihirtacce:"
Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan (abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidãje.
Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?"
suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku."
To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma.
Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani.
Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma.
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa.
Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma).
"Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya!
Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida* suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.
* Dabbõbin gida sun fi rashin hankali bisa ga na dãji, dõmin na dãji na gudun abin da zai cũce sũ su kuma dabbõbin gida sunã zamã tãre da mãsu cin su, su shã nõnonsu kuma su kashe 'ya'yansu.
Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi* a ciƙin kõwace alƙarya.
* Dã Muna so dã Mun aika wa kõwane gari da Annabinsa mai yi musu gargaɗi, amma ba Mu so haka ba, sai Muka aika ka kai ɗaya zuwa ga dukan dũniya dõmin Mu ɗaukaka darajarka.
Kuma shĩ ne Ya gauwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurbatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa.@تصحیح کننده
Kuma shĩ ne Ya garwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurɓatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa.
Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya* zuwa ga Ubangijinsa."
* Bã na neman wata ijãra sabõda inã karanta muku Alƙur'ãni, ko, sabõda inã shiryar da ku, amma wanda ya so ya ciyar da dũkiyarsa dõmin Allah, to, shĩ kam bã ni hana shi, sai ya ciyar. Kuma mun sani Annabi ba ya cin sadaka. A kan haka ne waɗansu Malamai suka hana karɓar ijãraa kan karantar da Alƙur'ãni. Abin da yake Mu'utamadi ya halatta sabõda Hadĩsi, kumada sauƙaƙewa ga aikin yãɗa addĩnin Musulunci. Hukumci yanã canzawa da canzãwar hãli.
kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa.@تصحیح کننده
Kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa.
Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da Shi.
* Idan kanã son sanin siffofin Allah, sai ka tambayi Allah, dõmin bãbu wanda ya san shi, sani na gani balle ya iya gaya maka yadda Yake, sabõda haka siffõfin Allah da sũnãyenSa duka bã a yin shisshigi a gare su, sai yadda aka ji su daga Manzon Allah.Tauƙifiyyai ne.
Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana* ta ƙãra musu gudu.
* Kõ sun san gaskiyar abin daaka kira su zuwa gare shi, bã zã su yi ɗã'ã ba, dõmin wai sunã jin nauyi su karɓi umurni daga wani mutum.
Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai* (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta.
* Taurãri bakwai waɗandaake cewa matafa su ne Mirrikh da Zahra da Uɗãrid da Ƙamar, wãtau Watã, da Rãnã, da Mushtari, da Zuhal; Kuma burjõji sũ gõma sha biyu ne, su ne Himlu, da Saur, da jauzã'a, da Sirtãn, da Asad, da Sunbula da Mĩzãn da Aƙrab, da Ƙausu, da Jadyu,da Dalwu da Hũt.
Kuma bãyin Mai rahama* su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya).
* Bãyan da ya ambaci masu ƙin su yi sujada ga Mai rahama sabõda kangararsu sai kumaya fãra ambaton siffofin mãsu son yin sujada gare shi, Yãyi musu sunã Bãyin Mai rahama.
Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra*
* Garama, ita ce uƙũba da dũkiya mai lazimtar wanda aka aza wa ita. Da Hausa anã cewa tãra. Watau azãba da zã tafi ƙarfin jiki har tanã neman wani abu wanda ya danganci jiki. Kõ mene ne, kamar dũkiya.
Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,
Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai.
Kuma wanda ya tũba,* kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah.
* Wanda ya tũba daga kõwane irin zunubi, waɗanda aka ambata da waɗanda ba a ambata ba, kõ dã laifinsa kãfirci ne, to, sai ya tũba zuwa ga Allah kawai, tũba ta gaskiya, lalle ne Allah zai karɓi tũbarsa matuƙar ajalin mutuwa bai sauka a kansa ba.
Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame* da makãfi.
* Idan an yi musu wa'azi zã su saurãre shi, kuma su yi aiki da shi. Bã zã su zama kurãme ba ga karɓar gaskiya, kuma bã zã su zama makãfi ba gaganin hanyar shiryawa.
Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya* mu shũgabanni ga mãsu taƙawa."
* Anã son mutum ya rõƙi Allah Ya ɗaukaka shi, shi da zuriyarsa, ɗaukakar addini, kamar yadda Annabi Ibrãhĩm ya yi rõƙon haka. Kuma wannan yanã cikin sifõfin Bãyin Mai rahama.
ترجمهٔ معانی قرآن کریم به زبان هوسا ـ برگردان: ابوبکر محمود جومی ـ مراجعه شده زیر نظر مرکز ترجمهٔ رواد. ترجمهٔ اصلی به هدف اظهار نظر و ارزشگذاری و بهبود مستمر در معرض نظر خوانندگان قرار دارد.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
نتایج جستجو:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".