ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمه ى هوساوى - ابوبكر جومى * - لیست ترجمه ها

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

ترجمهٔ معانی آیه: (48) سوره: سوره مائده
وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمُهَيۡمِنًا عَلَيۡهِۖ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۖ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡ عَمَّا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ لِكُلّٖ جَعَلۡنَا مِنكُمۡ شِرۡعَةٗ وَمِنۡهَاجٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ
Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyinsu daga abin da ya zo maka daga gaskiya.* Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya ku al'umma guda, kuma amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã sãɓãwa a cikinsa.
* Allah. Kuma Mun bai wa kowa shari'õ'insa da dõkõkinsa sa'an nan kuma da hanyar da ake bi wajen zartar da shari'ar.
تفسیرهای عربی:
 
ترجمهٔ معانی آیه: (48) سوره: سوره مائده
فهرست سوره ها شماره صفحه
 
ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمه ى هوساوى - ابوبكر جومى - لیست ترجمه ها

ترجمهٔ معانی قرآن کریم به زبان هوسا ـ برگردان: ابوبکر محمود جومی ـ مراجعه شده زیر نظر مرکز ترجمهٔ رواد. ترجمهٔ اصلی به هدف اظهار نظر و ارزش‌گذاری و بهبود مستمر در معرض نظر خوانندگان قرار دارد.

بستن