ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمه ى هوساوى - ابوبكر جومى * - لیست ترجمه ها

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

ترجمهٔ معانی آیه: (93) سوره: سوره مائده
لَيۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جُنَاحٞ فِيمَا طَعِمُوٓاْ إِذَا مَا ٱتَّقَواْ وَّءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ ثُمَّ ٱتَّقَواْ وَّءَامَنُواْ ثُمَّ ٱتَّقَواْ وَّأَحۡسَنُواْۚ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata*. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
* Yã maimaita faɗin taƙawa sau uku ga wanda ya tuba da shan giya da cãca dõmin ya nuna nauyinsu. Wanda ya shã giya kõ ya yi cãca, yã keta haddin Allah da alfarmar mutãne da darajar kansa. Sai yã yi taƙawa daga waɗannan zai iya rabuwa da su. Tsare su yanã cikin cika alkawari a tsakãnin mutum da Allah da kuma mutãne da ransa.
تفسیرهای عربی:
 
ترجمهٔ معانی آیه: (93) سوره: سوره مائده
فهرست سوره ها شماره صفحه
 
ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمه ى هوساوى - ابوبكر جومى - لیست ترجمه ها

ترجمهٔ معانی قرآن کریم به زبان هوسا ـ برگردان: ابوبکر محمود جومی ـ مراجعه شده زیر نظر مرکز ترجمهٔ رواد. ترجمهٔ اصلی به هدف اظهار نظر و ارزش‌گذاری و بهبود مستمر در معرض نظر خوانندگان قرار دارد.

بستن