Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau.
Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda* suka ce: "Allah yanã da ɗa."
* Lãrabawa sun ce malã'iku 'ya'yan Allah ne. Yahũdawa sunce Uzairu ɗan Allah ne, Nasãra sun ce Ĩsã ɗan Allah ne. Bãbu ladabi ga faɗin wannan magana. Sabõda haka Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gaya musu, cewa wannan magana ƙarya ce kuma rashin ladabi ne ga Allah, da ba su yi ĩmãni ba, ya ji tsõro kada ya zama shĩ ne ya yi ƙwauron bãki ga faɗã musu gaskiya. Sai Allah Ya gaya masa, cewa kada ya halakar da ransa dõmin baƙin cikin haka.
Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya.
Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa* ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.
* Sabõda haka ƙawar ƙasa, kamar furen itãcenta ne, bã su ruɗin mai hankali ga tsarewar ladabi tãre da Ubangijinsa, da bin sharĩ'ar Littafin da aka saukar wa Annabi kuma ba a sanya masa karkata ba.
Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo* da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?
* Lõkacin da Allah Ya ce: "kada Annabi ya wahalar da kansa dõmin baƙin cikin ba a karɓi maganarsa ba, sai Ya ba shi lãbãrin ma'abũta kõgo, yadda suka yi gudun hijira da addininsu, Allah Ya tsare su daga wahala, a cikin halin abin al'ajabi. Sa'an nan ƙissar ta tattara a kan ladubba waɗanda ake nħman Mutum ya tsare su tãre da Ubangijinsa a cikin dukan mõtsinsa, kamar yadda bayãni zai nũna.
A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu*! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu."
* Sun fara da addu'a ta nħman shiriya daga Allah, Ubangijinsu. Addu'a tun farko ga kõme ladabi ne. Kuma fãrãwa da nũna bautarsu ga Ubangiji, ladabi ne. Hijira da addini 1adabi ne, kuma amincewa da sãmun rahamar Allah, ladabi ne ga Allah, sabõda haka Allah ya jiɓinci tsaron kõgon ya zame musu mafi kyawun wurin zama.
Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi wanin Sa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan."
"Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah?"
"Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa, fãce Allah, to, ku tattara zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamar Sa kuma Ya sauƙaƙe muku madõgara daga al'amarinku."
Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba.
Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen dãma da wajen hagu, kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga farfãjiya (ta kõgon). Dã ka lẽka (a kan) su (dã) lalle ne, ka jũya daga gare su a guje kuma (dã) lalle ne ka cika da tsõro daga gare su.
Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin* su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin**. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum."
* Mahãwarar muminai a bãyan barcin shekara ɗari uku, amma duk da haka sunã cikin hankalinsu sunã mayar da al'amari ga Allah. ** Birnin shi ne Tarasus. Sunan sarƙinsu Daƙayãnus.
Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu* sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su." Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riƙi masãllãci a kansu."
* Muhãwarar mũminai da kãfirai, da yadda kãfirai ke zartar da al'amari bã da ambaton yardar Allah Ubangijinsu ba. Da yadda suke yin sãri-faɗi ga matsalõlin ilmi da ya kamãta a mayar da saninsu ga Allah.
Zã su ce: "Uku ne da na huɗunsu karensu."Kuma sunã cẽwa, "Biyar ne da na shidansu karensu," a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, "Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu."Ka ce: "Ubangijĩna* ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya san su fãce kaɗan."Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa** ga kõwa daga gare su a cikin al'amarinsu.
* Bayãnin ladubban magana ga matsalõlin ilmi da na aiki. Bãbu wanda ya san gaibu sai Allah. Bã a tambayar mãlaman ɓata da son zũciya, dõmin sãri-faɗi suke yi ga jawãbin mai tambaya.** Dõmin haka ba a yin fatawa a wurin mãlamin bidi'a kõ jãhili dõmin zai faɗi abin da yake so, kõ kuma ya yi ƙaddari faɗi, jĩfa a cikin duhu.
Fãce idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "¦ammãni ga Ubangijĩna, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya."
Ka ce: "Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shĩ ne da (sanin) gaibin sammai da ƙasa. Mũne ne ya yi ganin Sa da jin Sa! Bã su da wani majiɓinci baicin Sa kuma bã Ya tãrayya da kõwa a cikin hukuncinsa."
Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littãfin Ubangijinka. Bãbu mai musanyãwa ga kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata madõgara ba daga waninsa.
Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardar Sa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya.* Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncin Mu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna.
* Ãyõyi na ashirin da bakwai da ashirin da takwas sunã umurni da bin shari'a ta Alƙur'ãni, kuma sunã hani daga bin son zũciya dõmin nħman ƙawar rãyuwar dũniya wadda aka yi dõmin a jarrabi wãwã da ita, sa'an nan ta kõma turɓãya ƙeƙasasshiya. Dũbi ãya kuma, ta takwas da ta tara. Mun dai sani, cewa umurni da bin sharĩ'a bayyananna shĩ ne kan labarin sũrar.
Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu.
Waɗannan sunã da gidãjen Aljannar zama, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, anã sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar waɗansu tũfãfi kõre, na alharĩni raƙĩƙi da alharini mai kauri sunã kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa.
Kuma ka buga musu misãli* da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gõnaki biyu na inabõbi, kuma Muka kẽwayesu da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a tsakãninsu (sũ gõnakin).
* Misãli ga mai shagala da dũniya da ƙawarta, mai saurin kõmãwa turɓaya ƙeƙasasshiya, da maĩ bin umurnin Allah, mai ladabi da bin sharĩ'a. Yadda aƙibar kõwanensu zã ta kasance.
Kuma ɗan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã muhãwara da shi, "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a wajen jama'a."
"Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma."
Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, "Ashe kã kãfirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?"
"Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya."
"To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai santsi."
Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra* wani da Ubangijina ba!"
* Ya yi nadãmar halakar gõnar kawai, amma bai yi nadãmar kãfircin shirkin da ya yi ba, sabõda haka Allah bai mayar masa da badalinta ba. Daga nan kuma anã fahimtar cewa rashin mai da al'amari ga Allah shirku ne, kuma girman kai sabõda dũkiya, shirku ne wanda ƙawar dũniya ke sanya wãwãye a ciki.
Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari dudduga, iska tanã shiƙar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩkon yi ne a kan dukan kõme.
Dũkiya da ɗiya,* sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri.
* Dũkiya da ɗiya, ƙawar dũniya ne, idan suka zama abin alfahari ga mai su, amma idan an ciyar da dũkiya ga tafarkin Allah, kuma aka karantar da ɗiya ga bisa tafarkin hanyar sharĩ'a suka tãshi Musulmin ƙwarai, to, sun zama aikin sharĩ'a na Lãhira kħ nan.
Kuma a gittã* su ga Ubangijinka sunã sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne haƙĩƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba."
* Bayãnin abũbuwan da ke aukuwa a wurin hisãbi ke nan ga mãsu bin son zũciya, su bar sharĩ'a.
Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?" Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa.
Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai.**
** Allah Shĩ ne Ya halitta mutãne, kuma Ya ɗaukaka darajarsu, dõmin Yã sanya malã'iku su yi sujada ga ubansu Ãdamu. Sabõda wannan sõyayyar kuma Ya bã su sharĩ'ar da zã su bi su shiryu har su shiga Aljanna, amma sai suka ƙi, suka kõma wa Shaiɗan wanda yake shi ne farkon maƙiyin ubansu, Ãdamu, wanda ya ƙi yi wa sujada, har aka la'ane shi, sunã bin sa, shi da ɗiyansa, alhãli kuwa bãbu wani abin da zã su iya yi musu na alheri ko na sharri, dõmin sũ ma halitta ne kamarsu. Bã su san kõme ba a sama kõ a ƙasa, kuma Allah bã Ya yin ma'amalar kõme da su. Wanda ya bi Shaiɗan ya bar Allah, to, yã yi mugunyar musanya, kuma yã zãlunci kansa ƙwarai.
Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rãyukansu ba kuma ban kasance mai riƙon mãsu ɓatarwa (da wani) su zama mataimaka ba.
Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, "Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka riya." Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa* (Mahalaka) a tsakãninsu,
* Maubiƙã sũnan wani rãfi ne na wuta, asalinsa daga 'Wabiƙa,' wãtau yã halaka. Za a sanya wannan rãfi a tsakãnin mãsu bin Shaiɗan da sũrõrin gumãka, da wanda ya shirya musu gumãkan, sunã bauta musu.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli.*
* Jidãli, shĩ ne jãyayya, alhãli kuwa mutum yã san yanã kan ƙarya.
Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko* ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i-nau'i.
* Hanyar farko ita ce Allah Ya halaka su sabõda laifinsu kõ kuma azãba ta je musu nau'i-nau'i, dõmin su musulunta sai ƙarshe idan sun ƙi a halaka su. Waɗansu sun fassara 'ƙubala' ko 'ƙibala' da ta fuskance su bayyane, bisa ga karãtun kalmar 'ƙibala' da wasalin ƙasa, da ma'anar azaba.
Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita, kuma suka riƙi ãyõyi Na da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili.
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada.
Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa.*
* Watau ba su da wata makõma su bar wannan lõkacin alkawarin saukar azãbar.
Kuma waɗancan alƙaryu* Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka** su.
* Alƙaryun Ãdãwa da samũdãwa da waɗansunsu. ** Kõme Allah Zai yi, sai Yã sanya masa lõkacin aukuwarsa, kuma bã zai aukun ba sai ajalin nan da Ya ambata masa ya zo.
Kuma a lõkacin da Mũsã* ya ce wa yãronsa, "Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru."
* Shĩ ne MũSã bn Imrãn Manzon Banĩ Isrã'ĩla. Sababin wannan ƙissa, an tambaye shi ne, "Wãne ne ya fi ilmi a saninsa?" Sai ya ce: "Shĩ ne ya fi. Wannan jawãbi nãsa gaskiya ne, dõmin shĩ ne Manzon zãmaninsa, shĩ ne aka bai wa Attaura, kuma Allah Ya yi magana da shi, sai dai ya mance bai ce Allah Ya fi sani ba, dõmin haka aka ce masa ya tafi neman ilmi ga wani mutum a magamar teku biyu. Wannan bãwan Allah Haliru ne. Yãron Mũsã kuwa, shĩ ne Yũsha'u bn Nũn, Manzon Allah a bãyan Mũsã. Kĩfin kuma na guzurinsu ne wanda Allah Ya umurce shi ya ɗauka, sõyayye, kuma aka ce musu duka inda yai rai, to, a nan ne Bãwan Allah yake, mai shirin ƙãra wa Mũsã ilmi. Mayar da ilmi ga Allah, shĩ ne ladabin shari'a.
(Yãron) ya ce: "Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan, dõmin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki!"
Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyin Mu, Mun bã shi wata rahama* daga wurin Mu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gun Mu.
* Rahama a nan ita ce Annabci sabõda cħwa kuma an bã shi ilmi daga gun Allah, kuma ya yi hukunci da shi. Ilmin ilhãma bã a yin hukunci da shi dõmin Annabãwa kawai Allah Ya tsare daga kuskure game da wahayi. Wannan ne bambanci bayyananne a tsakanin wahayin Annabci da wahayin walicci. Haka mu'ijiza da karãma, su duka sãɓãwar al'ada ne, amma mu'ujizar Annabi an san zã ta zo daga bãkin wanda aka yi dõminsa, amma karãma bãbu mai saninta, sai tã auku. Sabõda waliyyi bã ya iya yin tãkara, amma annabi yana iya yin tãkara a kan maƙiyansa.
Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, "Kã hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, haƙĩƙa, kã zo da wani babban abu!"
Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na ƙyãma."
Ya ce: "Idan na tambaye* ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni."
* Mũsã ya kãsa yin haƙuri a bãyan ya yi alkawura cewa zai yi haƙuri, sabõda ba yã halatta ga mutum ya ga abin da ya sãɓa wa shari'a, sa'an nan ya yi shiru. Dã zai halatta a yi shiru, dã Mũsã bai yi magana ba ga aikin mãlamin da Allah Ya umurce shi da ya tafi ya karɓo ilmi daga gare shi, a bãyan Yã gaya masa cewa,Yã bã shi wani ilmi daga gare shi. Dõmin sharaɗin da ya sãɓa wa shari'a warwararre ne. Sabõda haka Allah bai zargi Mũsa ba a bayan sun rabu. Sake al-munkar wãjibi ne a cikin ladubban shari'a gwargwadon hãli, kamar yadda yake a cikin Hadĩsi. Ana gabãtar da hukuncin da ya fi tsanani.
Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩƙe. (Mũsã) ya ce: "Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa."
"Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki* a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karɓẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da ƙwãce.
* Watau wani kamfani ne na matalauta, sunã sana'ar ɗaukar kãya a cikin teku, sharika watau kamfani ciniki ya halatta da sharuɗɗansa.
"Kuma amma bangon, to, yã kasance na waɗansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum* ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar ƙarfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa."
* Wannan ya nũna cewa kirkin uba yanã amfãnin ɗiyansa, haka gari na daraja sabõda sãmun mutãnen kirki a cikinsa, kamar yadda yake ƙasƙanta da ƙasƙancin mazaunansa bisa dalĩlin da farko an kira garin 'alƙarya' sabõda rõwar mazauna, kuma aka kira shi Madĩna sabõda darajar yãran nan biyu da ubansu da taskarsu. Alƙarya ita ce ƙaramin gari watau ƙauye, kuma Madĩna ita ce babban gari.
Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini*, ka ce: "Zan karanta muku ambato daga gare shi."
* Zulƙarnaini an ce sarki ne yanã bin shari'ar lbrãhĩm, ga hannunsa ya musulunta sunansa Askandar. Haliru wazirin sane yanã tafiya a gaban yãƙinsa, kuma ɗan innarsa, watau ɗan khãlarsa ne. Shi ne ya gĩna Askandariyya. Sai dai ga maganar akwai warware jũna. Allah Ya sani. Abin da ke a gabãninmu a nan shĩ ne sanin cħwa Allah Yã bã shi mulki, ya kõ yi shĩ bisa sharĩ'a, ya yi ƙarfi, da ƙarfin Allah.
Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacẽwa a cikin wani ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta. Muka ce: "Yã Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu."
"Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau*, kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu."
* Kyauta mai kyau a nan ba Aljanna ba ce, dõmin maganar ta Zulƙarnaini ce idan ya ci ƙasa, yanã iya sanya mãsu ĩmãninta a cikin hãli mai kyau. Amma idan an ɗauki maganar, ta Allah ce, a cikin maganar Zulƙarnaini ga kãfiri, to, a nan 'mai kyau' sai ta zama Aljanna ke nan.
Suka ce: "Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu?"
Ya ce: "Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhẽri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu."
"Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: "Ku hũra (da zugãzugai)." Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: "Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa."
Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin* Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce."
* Wa'adin Ubangiji da fitõwar Yãjũj da Mãjũj. A yanzu bãbu wanda ya san inda suke zaune, sai Allah.
Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa.*
* Allah Ya nũna yadda hãlin da Zulƙarnaini ya bar Yãjũj da Mãjũj, watau sun garwaya a cikin jũnansu, sa'an nan kuma wannan ma'anar aka bãyar da ita ga mutãne waɗanda ke bin son ransu, bã su bin shari'ar Allah, sunã hargitse a tsakãninsu, har a yi bũsar farko, su mutu, kuma a yi bũsa ta biyu su tãshi a cikin hargitsinsu, sai kuma a gitta Jahannama gaba gare su.
Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã* Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa.
* Zikr- tunãwa- shi ne Alƙur'ãni da abin da ya tãra na ibãda da sauran ma'ãmalõli, dukansu ibãda ne, matuƙar an bi abin da Allah Ya ajiye a cikinsu na hukunce-hukunce.
Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa*, majiɓinta baic iNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.
* Waɗanda suka riƙi wasu bãyin Allah, sunã bauta musu, kamar Yahũdu mãsu bauta wa Uzairu da Nasãra mãsu bautawa Ĩsã da wasu Musulmi mãsu bauta wa wasu sãlihai sun zama kãfirai. Ma'anar bautawar shi ne su ƙirƙira wasu hukunce-hakunce kõ wasu sifõfi waɗanda suka sãɓa wa maganar Alƙur'ãni da Hadĩsi, sa'an nan su jingina su zuwa ga waɗannan bãyin Allah, su bi su da su.
Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo* ba a Rãnar ¡iyãma.
* Watau ko aunawa bã zã a yi ba balle a daidaita ma'auni.
Ka ce: "Dã tẽku* ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."
* Ma'anar ãyar nan ita ce Allah ne Mafi sani. llmin Allah bã shi da iyãka, kõ kalmõmin da suka ɗauki ma'anõninsa, bã zã a iya rubuta su ba, balle ma'anõnin da ke cikinsu. Sabõda haka abin da ke hankali a mutum, shĩ ne ya yi aiki da ɗan ilmin da Allah Ya umurce shi da aiki dashi. Idan ya nemi ya wuce nan, to, ya halakar da kansa dõmin bai san inda zai fãɗa ba. Wannan ilmin shi ne sharĩ'a da aiki da ita.
Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa."*
* Wannan ãya, a dunƙule, ta tãra dukan abin da ke cikin sũrar. Allah Ya shiryar da mu, ga kaɗaita shi ga ibãda, da yin ibadar, kuma yadda Allah Ya ce a yĩ ta, ga mai tsammãnin rabo a Lãhira. Wanda ba ya tsammãnin rabon Lãhira, ya tsaya ga dũniya mai gushħwa da sauri, to, shĩ bã a shiga batunsa ba.
Terjemahan makna Alquran Alkarim - Terjemahan Berbahasa Hausa - Abu Bakar Jomy - Daftar isi terjemahan
Terjemahan makna Al-Qur`ān Al-Karīm ke bahasa Hausa oleh Abu Bakar Mahmud Jomy. Sudah dikoreksi di bawah pengawasan Markaz Ruwād Terjemah. Teks terjemahan asli masih bisa ditampilkan untuk diberi masukan, evaluasi dan pengembangan.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
Hasil pencarian:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".