Terjemahan makna Alquran Alkarim - Terjemahan Berbahasa Hausa - Abu Bakar Jomy * - Daftar isi terjemahan

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Terjemahan makna Ayah: (78) Surah: Surah Al-Ḥajj
وَجَٰهِدُواْ فِي ٱللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِۦۚ هُوَ ٱجۡتَبَىٰكُمۡ وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمۡ إِبۡرَٰهِيمَۚ هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ مِن قَبۡلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيۡكُمۡ وَتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِۚ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعۡتَصِمُواْ بِٱللَّهِ هُوَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ فَنِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ
Kuma ku yi jihãdi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihãdinSa. shĩ ne Ya zãɓe ku alhãli kuwa bai sanya wani ƙunci* ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrãhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi** daga gabãnin haka. Kuma a cikin wannan (Littãfi ya yi muku sũna Musulmi), dõmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemãsu shaida a kan mutãne. Sabõda haka ku tsayar da salla kuma ku bãyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Sãbõda haka mãdalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mãdalla da Shi ya zama Mai taimako.
* Bãbu ƙunci a cikin Musulunci, duk inda aka faɗi tsanani kuma an faɗi yadda sauƙi zai sãmu a kõwane hãli. ** Sharaɗin Musulunci ya zama a kan aƙĩdar Ibrãhĩm wanda ya yi wa wannan al'umma sũna da Musulmi tun a zãmaninsa, kuma an ambaci wannan magana a cikin wannan Littafi, wãtau Alƙur'ãni, a cikin sũrar Baƙara ãyã ta 128.
Tafsir berbahasa Arab:
 
Terjemahan makna Ayah: (78) Surah: Surah Al-Ḥajj
Daftar surah Nomor Halaman
 
Terjemahan makna Alquran Alkarim - Terjemahan Berbahasa Hausa - Abu Bakar Jomy - Daftar isi terjemahan

Terjemahan makna Al-Qur`ān Al-Karīm ke bahasa Hausa oleh Abu Bakar Mahmud Jomy. Sudah dikoreksi di bawah pengawasan Markaz Ruwād Terjemah. Teks terjemahan asli masih bisa ditampilkan untuk diberi masukan, evaluasi dan pengembangan.

Tutup