Kamar wancãn *(asĩrin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabãninka.
* Asirin haɗa jama'a bã zã su rarrabu ba. Watau su riƙi Allah Shi kaɗai ne Ubangiji Mai yin umurni ko hani, kuma su riƙi cewa Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gareshi, shĩ ne cikamakin Annabãwa, bãyansa bã a bai wa kõwa kõme fãce fahimta ga abin da ya zo da shi.
Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur'ãni) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr.
Kuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al'umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãlumaii bã su da, wani majiɓinci, kuma bã su da wani mataimaki.
Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna.
(Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasai, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.
Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. *Abin da kuke kira zuwa gare shi,** ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyar Sa.
* Ku bi umurnin Allah kamar yadda Ya aza muku hukunce-hukuncenSa, kada ku karkace da bin umurnin waɗansu na dabam waɗanda bã Allah ba, kõ kuma kada ku bi son zũciyarku. Bin umurnin wani zai sanya ku sãɓãwa jũnanku, ku rarrabu, ku rasa ƙarfi a kan maƙiyanku. Wanda ya bi umurnin waɗansu, waɗanda bã Allah ba, to ya yi shirka da Allah ke nan kuma haɗuwar mãsu bin umurnin waɗansu waɗanda bã Allah ba, to, tanã da wuya. Wannan ãya ta hana bin ɗarĩƙõƙin ƙungiyõyin sũfãye duka, dõmin bin su, bin umurnin waɗansu ne waɗanda bã Allah ba kuma yanã rarraba Musulmi, su zama ƙungiya-ƙungiya, da sãɓãni mai nĩsa. Bã zã a ce ba, "Ã'aha! Wannan ãya ta sauka ga Yahũdu da Nasãra kawai" dõmin ãyõyi biyu l4 da l5, mãsu bin wannan, sun gama harda Musulmi, dõmin umurni ga Annabi, umarni ne sabõda al'ummarsa. Kuma sãɓãnin mãsu ɗariƙõƙi sãɓãni ne a kan asali watau aƙida, bã sãɓãnine a kan rassuna na furũ'a ba. Sabõda haka bãbu ƙiyayya a tsakãnin mabiya mazhabõbi, dõmin sãɓãninsu, na fahimta ne kawai. Sãɓãni ga reshe, rahama ce, amma sãɓãni ga asali azãba ce. ** Watau haɗuwar jama'a ga bin addini guda, bã da sãɓawa ba ga asalinsa. Wanda ya ce: An saukar wa wani mutum, baicin Muhammadu, da wani abu daga Allah, to, shĩ ya sãɓãwa asali. Sãɓãwa ga asali kãfirci ne.
Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma* tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.
* Kalmar da ta gabãta, ita ce "Allah bã zai halaka mutane ba sabõda zunubi sai ajalinsu ya zo." Zãlunci da ke hana su haɗuwa a bãyan sanin gaskiya, shi ne hassadar jũna, sa kwaɗayi da son shugabanci a cikin mu'amala.
Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take."
Kuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al'amarin Allah daga bãyan an karɓa masa, hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã da wata azãba mai tsanani.
Waɗanda ba su yi ĩmãni da ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa, sunã a cikin ɓata Mai nĩsa.
Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira.
Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bã dõmin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi.
Kanã ganin azzãlumai sunã mãsu tsõro daga abin da suka sanã'anta alhãli kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai sunã a cikin fadamun Aljanna sunã da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma.
Wancan shĩ ne Allah ke bãyar da bushãra da shi ga bãyin Sa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya.
Kõ zã su ce: "Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zũciyarka, kuma Allah Yana shãfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmõminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata.
Kuma Yanã karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yanã ƙãra musu (sakamako) daga falalar Sa. Kuma kãfirai sunã da wata azãba mai tsanani.
Kuma dã Allah Ya shimfiɗa arziki ga bãyinSa, dã sun yi zãluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yanã sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, game da bãyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani.
Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan bãyan tẽkun, Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai gõdiya.
Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci, kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai.
Kuma waɗanda *ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfãsha, kuma idan sun yi fushi, sũ, sunã gãfartawa.
* Bayãnin siffõfin mũminai, waɗanda suke tsare su, Yana lãmunce zama haɗe, da gamuwar Musulmi, sũ ne siffõfi shida, nisantar manyan zunubbai da zina, da gãfarta fushi, da tsayar da salla, da shãwara ga al'amuran tsakãninsu, da ciyar da dũkiya da ta wajabci mutum ya ciyar da ita a cikin alheri ga inda Allah Ya ce a ciyar da ita.
Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã ciyarwa.
Da waɗanda* idan zãlunci ya sãme su, sunã nẽman taimako (su rãma).
* Wajen rãma zãlunci kõ yinsa, mutãne sun kasu kashi huɗu. Mãsu rãmãwa gwargwadon zãlunci, bã su da laifi; da mãsu rãmãwa da abin da ya fi laifin da aka yi musu, to, sunã da laifi kamar mãsu fãra zãlunci, da mãsu gãfartãwa, waɗannan sũ ne Allah ke so.
Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bã Ya son azzãlumai.
lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai raɗaɗi.
Kuma wanda* (Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyan Sa, kuma zã ka ga azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, "Shin, akwai hanya zuwa ga kõmãwa?"
* Bayãnin mai zãlunci da sakamakonsa a Rãnar Lãhira.
Kuma kanã ganin su anã gitta su a kanta, sunã ƙasƙantattu sabõda wulãkanci, sunã hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sai su ce, "Lalle ne, mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu da iyãlansu a Rãnar ¡iyãma." To, lalle ne, azzãlumai sunã a cikin wata azãba zaunanniya.
Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani gõdabe na tsĩra.
To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin kãfirci ne.
Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã bãyar da 'ya'ya mãtã ga wanda yake so, kuma Yanã bãyar da ɗiya maza ga wanda Yake so.
Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana* fãce da wahayi, kõ daga bãyan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.
* Annabãwa a lõkacin da Allah Ya yi musu magana ba su gan shi ba, sai dai sun ji maganarsa kamar yadda Musã ya ji, kõ kuma da wãsiɗar malã'ika kamar sauran Annabãwa, kõ kuwa da ilhama watau ya san hukunci ba da magana kõ wani wãsiɗar malã'ika ba. Ilhãmar Annabãwa da mafarkinsu gaskiya ne. Ilhãma da mafarkin sauran mutãne bã ya zama hujja sai idan yã dãce da shari'a, sai a yi aiki da shi a kan shari'a bã a kan mafarkin ko ilhãmar ba.
Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩn Mu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya.
Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi - Indice Traduzioni
Traduzione dei significati del Nobile Corano in hausa di Abubakar Gomi, rivista sotto la supervisione di Pioneer Translation Center (Ruwwad at-Tarjama). L'accesso alla traduzione originale è disponibile allo scopo di esprimere opinioni e valutazioni per un perfezionamento continuo del testo
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
Risultati della ricerca:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".