Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi * - Indice Traduzioni

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Traduzione dei significati Sura: Al-Jumu‘ah   Versetto:

Suratu Al'Jumu'a

يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡمَلِكِ ٱلۡقُدُّوسِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ
Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah, Mamallaki, Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima.
Esegesi in lingua araba:
هُوَ ٱلَّذِي بَعَثَ فِي ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ رَسُولٗا مِّنۡهُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُزَكِّيهِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu,* wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyin Sa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna.
* Lãrabawa sũ ne mabiya al'ãdu, watau ummiyyũn daga ummu, watau uwa watau kamar yadda uwãye suka haife su dõmin bã su da wani littãfi da suke bi sai al'ãdunsu da hukunce-hukuncen shaihunansu.
Esegesi in lingua araba:
وَءَاخَرِينَ مِنۡهُمۡ لَمَّا يَلۡحَقُواْ بِهِمۡۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Da waɗansu mutãne* daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
* Su ne Ajamãwan da zã su musulunta su bi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Kõ kuwa duk wanda ya musulunta a bãyan sahabban Annabi. Wannan yanã nunã falalar sahabbai a kan waɗansunsu.
Esegesi in lingua araba:
ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abũcin dukan falala mai girma.
Esegesi in lingua araba:
مَثَلُ ٱلَّذِينَ حُمِّلُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ ثُمَّ لَمۡ يَحۡمِلُوهَا كَمَثَلِ ٱلۡحِمَارِ يَحۡمِلُ أَسۡفَارَۢاۚ بِئۡسَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen* nan da suka ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai.
* Tir da wanda ya yi siffa da irin siffõfin Yahũdu daga Musulmi wajen ɗaukar karãtun Alƙur'ãni amma kuma bai yi aiki da shi ba. Yahaya bn Yamãni ya ce: "Sunã rubuta nadĩsi bã su fahimtarsa, kuma bã su kula da ma' anarsa." Watau sunã wahala wajen ɗaukar ilmin da aka ɗõra musu ɗaukarsa amma kuma bã su yin amfãni da shi a wajen aikinsu da mu'ãmalõlinsu.
Esegesi in lingua araba:
قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ هَادُوٓاْ إِن زَعَمۡتُمۡ أَنَّكُمۡ أَوۡلِيَآءُ لِلَّهِ مِن دُونِ ٱلنَّاسِ فَتَمَنَّوُاْ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Ka ce: "Yã kũ waɗanda suka tũba (Yahũdu)! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa* idan kun kasance mãsu gaskiya."
* Ba a sãduwa da Allah sai a bãyan mutuwa. Masõyi nã bũrin sãduwa da masõyinsa, kuma bã zai yi gudun sababin sãduwar ba.
Esegesi in lingua araba:
وَلَا يَتَمَنَّوۡنَهُۥٓ أَبَدَۢا بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّٰلِمِينَ
Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abadã sabõda abin da hannãyen su suka gabãtar. Kuma Allah ne masani ga azzãlumai
Esegesi in lingua araba:
قُلۡ إِنَّ ٱلۡمَوۡتَ ٱلَّذِي تَفِرُّونَ مِنۡهُ فَإِنَّهُۥ مُلَٰقِيكُمۡۖ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta, to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
Esegesi in lingua araba:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَوٰةِ مِن يَوۡمِ ٱلۡجُمُعَةِ فَٱسۡعَوۡاْ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَذَرُواْ ٱلۡبَيۡعَۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar* ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
* Ba a hana Musulmi aiki ba a kõwace rãna, sai dai an hana duk wanda Jumu'a ta lazimta a kansa da ya yi wani aiki wanda bã na tattalin salla ba a rãnar Jumma'a, a bãyan kiran salla. Anã nufi da kiran salla na biyu a bãyan limãmi ya zauna a kan mumbarinsa, dõmin wannan kiran aka sani azãmanin Annabi da Abubakar da Umar. Amma kira na farko, Usman bn Affãn ne ya fãra shi dõmin farkar da mutãne, a bãyan sun yi yawa kuma sun kama sana'õ'i. Kuma a bãyan an ƙãre salla, sai a wãtse zuwa ga ayyuka da neman abinci. Bã a tsayãwa yin wata nãfila a bãyan sallar Jumu'a, sai dai an so yin raka'a biyu a bãyan fita daga masallãci kamar yadda Annabi ke yi. A farko, anã yin huɗubar sallar Jumma'a a bãyan salla har a lõkacin da ãyarin Dihyatul Kalbi ya kõmo daga shãm (Syria) da abinci,ya sauka a Baƙĩ'a, suka buga ganga, sai Sahabbai suka fita dõmin neman sayen abincin a gabãnin a ƙãre huɗubar suka bar mutum gõma shã biyu tãre da Annabi. Sai aka mayar da huɗubar a gabãnin salla. Kuma an fahimci cewa anã yin huɗuba a tsaye. Kuma ba a kafa Jumu'a, sai a kafaffen gari, amma Jumu'a nã ƙulluwa da mutum gõma sha biyu da lĩman.
Esegesi in lingua araba:
فَإِذَا قُضِيَتِ ٱلصَّلَوٰةُ فَٱنتَشِرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا لَّعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban rabo.
Esegesi in lingua araba:
وَإِذَا رَأَوۡاْ تِجَٰرَةً أَوۡ لَهۡوًا ٱنفَضُّوٓاْ إِلَيۡهَا وَتَرَكُوكَ قَآئِمٗاۚ قُلۡ مَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ مِّنَ ٱللَّهۡوِ وَمِنَ ٱلتِّجَٰرَةِۚ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ
Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrin mãsu arzũtãwa."
Esegesi in lingua araba:
 
Traduzione dei significati Sura: Al-Jumu‘ah
Indice delle Sure Numero di pagina
 
Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi - Indice Traduzioni

Traduzione dei significati del Nobile Corano in hausa di Abubakar Gomi, rivista sotto la supervisione di Pioneer Translation Center (Ruwwad at-Tarjama). L'accesso alla traduzione originale è disponibile allo scopo di esprimere opinioni e valutazioni per un perfezionamento continuo del testo

Chiudi