Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, "Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu."Kãfirai suka ce: "Lalle ne wan nan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne."
Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yanã gudãnar da al'amari. Bãbu wani macẽci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunãni?
zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai halitta wan nan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne waɗan da suke sani.
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yanã shiryar da su sabõda ĩmãninsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, a cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
Kiransu a cikinta, "Tsarkin Ka yã Allah!" Kuma gaisuwarsu a cikinta,"Salãmun", kuma ƙarshen kiransu, cẽwa, "Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu."
Kuma dã Allah Yana gaggãwa ga mutãne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alhẽri, haƙĩƙa dã an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabõda haka Munã barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sunã ta ɗimuwa.
Kuma idan cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, yanã (kwance) ga sãshensa kõ kuwa zaune, kõ kuwa a tsaye. To, a lõkacin, da Muka kuranye cũtar daga gare shi, sai ya shũɗe kamar ɗai bai kirãye Mu ba zuwa ga wata cũta wadda ta shãfe shi. Kamar wannan ne aka ƙawãta ga maɓannata, abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabãninku, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, amma ba su kasance sunã ĩmãni ba. Kamar wannan ne, Muke sãkãwa ga mutãne mãsu laifi.
Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi.*" Ka ce: "Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma."
* Sunã nufin idan ya musanya shi, su ce: " To, gã shi ka bayyana cewa kai ne mai ƙirƙira shi, kanã jinginã shi ga Allah.".
Ka ce: "Dã Allah Ya so dã ban karanta shi ba a kanku, kuma dã ban sanar da kũ ba gameda shi, dõmin lalle ne nã zauna a cikinku a zãmani mai tsawo daga gabãnin (fãra saukar) sa. Shin fa, bã ku hankalta?"
Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah."Ka ce: "Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi."
Kuma mutãne ba su kasance ba fãce Al'umma guda, sa'an nan kuma suka sãɓã wa jũna, kuma ba dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijin ka, dã an yi hukunci a tsakãninsu a kan abin da yake a cikin sa suke sãɓã wa jũna.
Kuma sunã cẽwa: "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a gare shi, daga Ubangijin sa?" To, ka ce: "Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira. Lalle ne nĩ, tãre da ku, inã daga mãsu jira."
Kuma idan Muka ɗanɗanã wa mutãne wata rahama, a bãyan wata cũta tã shãfe su, sai gã su da mãkirci a cikin ãyõyinMu. Ka ce: "Allah ne mafi gaggãwar (sakamakon) mãkirci." Lalle ne Manzannin Mu sunã rubũta abin da kuke yi na mãkirci.
Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya.
To, a lõkacin da Ya kuɓutar da su, sai, gã su sunã zãlunci a cikin ƙasa, bã da wanĩ hakki ba. Yã ku mutãne! Abin sani kawai, zãluncinku a kanku yake, a bisa rãyuwar dũniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makõmarku take, sa'an nan Mu bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa,
Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurnin Mu ya je mata da dare kõ kuma da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗan da suke tunãni.
Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari)1), wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.
* Mãsu aikin ƙwarai waɗanda suka karɓa kiran Allah sunã da sakamakon abu mai kyau, wãtau Aljanna, kuma da ƙãri, watau ganin Ubangijinsu a cikin Aljanna. Haka Hadisi ya yi fassara.
Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yanã rufe su. Bã su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntãyen ƙirãruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abõkan wuta, sunã madawwama a cikinta.
Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, "Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku." Sa'an nan Mu rarrabe a tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: "Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa ba."
A can ne kõwane rai yake jarraba abin da ya bãyar bãshi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace musu.
Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?"
Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake fãra halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita?" Ka ce: "Allah ne Yake fãra halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yãyã akejũyar da ku?"
Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?" Ka ce: "Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bã ya shiryarwa fãce dai a shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yãya kuke yin hukunci?"
Kuma wan nan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãnin sa da bayãnin hukuncin littãffan Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake.
Kõ sunã cẽwa, "Yã ƙirƙira shi?" Ka ce: "Ku zo da sũra guda misãlinsa, kuma ku kirãyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya."
Ã'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassarar sa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba, yãya ãƙibar Azzãlumai ta kasance?
Kuma daga cikin su akwai wanda yake yin ĩmãni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bã ya yin ĩmãni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata.
Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: "Inã da aikĩna kuma kunã da aikinku, kũ kuɓutattu ne daga abin da nake aikatãwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatãwa."
Kuma rãnar da Yake tãra su, kamar ba su zauna ba fãce sa'a guda daga yini. Sunã gãne jũna a tsakãninsu. Haƙĩƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasãra. Kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.
Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu alkawari, kõ kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makõmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatãwa.
Ka ce: "Ba na mallaka wa kaina wata cũta, haka kuma wani amfãni, sai abin da Allah Ya so. Ga kõwace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, bã zã su yi jinkiri daga gare shi ba, kõ dã sã'ã guda, kuma bã zã su gabãta ba."
Kuma dã kõwane rai wanda ya yi zãlunci yã mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, dã yã yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma bã zã a zãlunce su ba.
Ka ce: "Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabõda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?" Ka ce: "Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirãwar ƙarya?"
Kuma mẽne ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Rãnar ¡iyãma? Lalle haƙĩƙa, Allah Ma, abũcin falala ne a kan mutãne, amma kuma mafi yawansu bã su gõdẽwa.
Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne.
To, Lalle ne masõyan* Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba.
* Waliyyin Allah, shi ne masõyin Allah da sharaɗin ya zama mumini mai taƙawa watau yanã aiki da abin da Allah Ya umurce shi, kuma yanã barin abin da Allah Ya hana shi, bisa harshen Annabinsa wanda yake biya. Bãbu ƙarin kõme bãbu ragi. Bushãrarsu, ita ce yabon mutãne a gare su, kõ kuma a lõkacin mutuwarsu malã'iku su riƙa yi musu bushãra da gamuwa da Ubangijinsu, kõ kuma a cikin kabari wajen tambaya. Allah ne Mafi sani.
To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa (ga Allah a Mulkin Sa). Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi kawai.
Suka ce: "Allah Ya riƙi ɗa." Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah?
Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ya mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri."
"Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."*
* Watau dukan abin da na zo muku da shi na umurni kõ hani, to, ni ma an umurce ni da yinsa kõ barinsa. Kuma bã ni neman wata ijãrar karantarwa daga gare ku dõmin Allah Ya umarce ni da iyar da manzancinsa zuwa gare ku, sabõda haka Shi ne zai biyã ni tsãdar aikĩna.
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗan da aka yi wa gargaɗi ta kasance.
Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bãyansa zuwa ga mutãnensu, suka jẽmusu da hujjõji bayyanannu, to, ba su kasance zã su yi ĩmãni ba sabõda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukãtan mãsu ta'addi.
Sa'an nan kuma a bãyansu Muka aika Mũsa da Hãrũna zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, tãre da ãyõyin Mu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutãne mãsu laifi.
Suka ce: "Shin, ka zo mana ne dõmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bã zã mu zama mãsu ĩmãni ba sabõda ku."
Sa'an nan bãbu wanda ya yi ĩmãni da Mũsa fãce zuriya daga mutãnensa, a kan tsõron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjãyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga mãsu ɓarna.
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla*, kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni.
* Su sanya gidãjensu sunã fuskantar Alƙibla ta Ka'aba dõmin su riƙa yin salla a cikin gidãjen, sabõda tsõron in sun tafi masallaci zã a fãɗa su da dũka sunã a cikin salla. Wannan kuma yã nũna yadda ake son gidajen Musulmi su kasance a kõ da yaushe.
Sai MũSã ya ce: "Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar (damutãne) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri* a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi."
* Mũsã ya yi addu'a a kansu, har da rashin ĩmãni sabõda yã sãmi lãbãrin bã zã su yi imãni ba, kamar mutãnen Nũhu.
Kuma Muka ƙẽtãrar da Banĩ Isrã'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zãlunci da ƙẽtare haddi, har a lõkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: "Nã yi* ĩmãni cẽwa, haƙĩƙa, bãbu abin bautawa fãce wannan da Banũ Isrã'il suka yi ĩmãni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi."
* Ĩmãni a bãyan Manzon mutuwa ya isa ga kãfiri bã zai yi masa amfãni ba.
To, a yau Munã kuɓutar* da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu.
* Kuɓutar da jikin Fir'auna: Banda rũhinsa dõmin a tabbatar da yã mutu.
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar* da Banĩ Isrã'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa mãsu dãɗi. Sa'an nan ba su sãɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Kiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna.
* Allah Yã bai wa Banĩ Isrã'ila mulkin Masar da falasɗĩnu gabã ɗaya a bãyan halaka Fir'auna da mutãnensa.
To, idan ka kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littãfi daga gabaninka. Lalle ne, haƙĩƙa, gaskiya tã jẽ maka daga Ubangijinka dõmin haka kada ka kasance daga mãsu kõkanto.
To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi* ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye Azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci.
* Alƙaryun da aka aika da Manzanni cikinsu, ba su yi ĩmãni duka ba fãce mutum ɗaya, kõ biyu a gabãnin halaka ta sãmi mutãnensu. Sai dai alƙaryar Yũnusa, ita kam tã ji tsõro, ta yi ĩmãni a gabãnin saukar azãba, sabõda haka suka tshĩra, ba a halaka garin bawatau Nĩnawa. Watau bãbu mai iya sãmun ĩmãni sai Allah Ya nufe shi da haka. Kõ da mai yin gargaɗin ya kan yiwu ya karkace, sai da tsarin Allah.
To, Shin sunã jiran wani abu fãce kamar misãlin kwãnukan waɗanda suka shũɗe daga gabãnin su? Ka ce: "Ku yi jira! Lalle nĩ tãre da ku, inã daga mãsu jira."
Ka ce: "Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa, waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni."
"Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci."
Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyẽ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhẽri, to, bãbumai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Ka ce: "Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba."
Kilniojo Korano reikšmių vertimas - Hausų k. vertimas - Abu Bakr Žomy - Vertimų turinys
Kilniojo Korano reikšmių vertimas į hausų k., išvertė Abu Bakr Muchammed Džūmi. Jis buvo taisytas prižiūrint Ruad vertimų centrui, o originalų vertimą galima peržiūrėti nuomonės išreiškimo, vertinimo ir nuolatinio tobulinimo tikslais.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
Paieškos rezultatai:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".