Kilniojo Korano reikšmių vertimas - Hausų k. vertimas - Abu Bakr Žomy * - Vertimų turinys

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Reikšmių vertimas Aja (Korano eilutė): (89) Sūra: Sūra Al-Ma’idah’
لَا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا عَقَّدتُّمُ ٱلۡأَيۡمَٰنَۖ فَكَفَّٰرَتُهُۥٓ إِطۡعَامُ عَشَرَةِ مَسَٰكِينَ مِنۡ أَوۡسَطِ مَا تُطۡعِمُونَ أَهۡلِيكُمۡ أَوۡ كِسۡوَتُهُمۡ أَوۡ تَحۡرِيرُ رَقَبَةٖۖ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٖۚ ذَٰلِكَ كَفَّٰرَةُ أَيۡمَٰنِكُمۡ إِذَا حَلَفۡتُمۡۚ وَٱحۡفَظُوٓاْ أَيۡمَٰنَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa* a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa.
* Rantsuwa alkawari ce da sunãn Allah, cewa mai rantsuwar zai aikata ko kuwa bã zai aikata ba, kõ kuwa a kan tabbatar wani abu a kan sifar da ya ambata, kõ kuwa kõruwarsa daga wannan sifar. Wanda ya yi rantsuwa sa'an nan ya yi hinsi, to, sai ya yi kaffãra, kamar yadda aka ambata a cikin ãyar. Sai fa idan ta zama yãsassar rantsuwa ce, wadda mutum ya yi a kan saninsa, sa'an nan sanin nan ya warware, sabõda bayyanar wani abu. Wasu sun ce ita ce rantsuwar da ake yi a cikin magana bã da nufi ba, kamar ã'a wallãhi, ko ĩ, wallãhi. Kuma akwai rantsuwar gamusa a kan ƙarya. Ita ma bãbu kaffãra sabõda ita, sai tuba zuwa ga Allah da istigfãri, kuma tanã sanya tsiya.
Tafsyrai arabų kalba:
 
Reikšmių vertimas Aja (Korano eilutė): (89) Sūra: Sūra Al-Ma’idah’
Sūrų turinys Puslapio numeris
 
Kilniojo Korano reikšmių vertimas - Hausų k. vertimas - Abu Bakr Žomy - Vertimų turinys

Kilniojo Korano reikšmių vertimas į hausų k., išvertė Abu Bakr Muchammed Džūmi. Jis buvo taisytas prižiūrint Ruad vertimų centrui, o originalų vertimą galima peržiūrėti nuomonės išreiškimo, vertinimo ir nuolatinio tobulinimo tikslais.

Uždaryti