Kuma waɗanda* suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa, su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
* Wata ƙungiyã ta munãfukai mãsu aiki dõmin tumɓuke ƙarfin Musulmi ta hanyar da bã a iya gãnewa da sauri. Kamarsu gina masallaci kusa da wani tsõhon masallãci da sũnan taimakon addĩni amma da nufin su raba jama'ar Musulmi,kuma sun sãmi wurin da zã su riƙa tãro da ɓõye kãyan yãƙi da shirin sharri ga Musulmi. Kamar ma'abũta Masjidil Darãr, wanda aka yi kusa da masallacin Kuba a Madĩna. Aikinsu bai tsaya ga lõkacin yãƙin Tabũka ba, sabõda haka aka ce: da bagewa ga wanda ya yãƙi Allah a gabãni, watau a gabãnin bayyanar fallasar munãfukai da yãƙin Tabũka.
Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka*. Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman tsarkakuwa.
* Sunã son tsarkaka ta ɓõye da ta bayyane. Ta ɓõye sananniya ce: ita ce rashin munãfunci, kuma ta bayyane ita ce sunã kãma rũwa a bãyan sun karce kãshinsu da dũtse, kamar yadda ya zo a cikin Hadĩsi. Allah ne Mafi sani.
Shin, wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne mafi alhẽri kõ kuwa wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan gãɓar rãmi mai tusgãwa? Sai ya rũsa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne Azzãlumai.
Lalle ne, Allah Ya saya* daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ su. (Allah Yã yi) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma.
* Bãyan bayãnin nau'ukan kãfirai da alãmõminsu da yadda zã a bi wajen yankewa da su, da barin fage ga muminai na ƙwarai, sai kuma Yã kirãyi muminai zuwa ga mubãya'a ga Allah, watau ciniki, sa'an nan Ya bayyana musu kuɗin saye da abin sayarwa, ya ce: "Allah Yã saya daga muminai.".
Vertaling van de betekenissen Edele Qur'an - Hausa vertaling - Abu Bakr Jumi - Index van vertaling
Vertaald door Aboe Bakr Mahmoed Jumi. Ontwikkeld onder supervisie van het Centrum van Pionier Vertalers, de originele vertaling is beschikbaar voor inzage, beoordeling en voortdurende verbetering.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
Zoekresultaten:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".