Check out the new design

Tradução dos significados do Nobre Qur’an. - tradução Hawsia - Abu Bakr Jumi * - Índice de tradução

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Tradução dos significados Surah: Saba   Versículo:
لَقَدۡ كَانَ لِسَبَإٖ فِي مَسۡكَنِهِمۡ ءَايَةٞۖ جَنَّتَانِ عَن يَمِينٖ وَشِمَالٖۖ كُلُواْ مِن رِّزۡقِ رَبِّكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥۚ بَلۡدَةٞ طَيِّبَةٞ وَرَبٌّ غَفُورٞ
Lalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa[1] a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara."
[1] Ƙissar Dãwũda da ta Sulaimãn sunã nũna yadda Allah ke sauƙaƙe wa bãyinsa hanyar ibãda da ta sãmun abinci da sauƙi idan sun mayar da al'amuransu gare shi. Ƙissar sabaãwa tanã nũna yadda Allah ke karɓe wadãta daga wanda ya kãfirce Masa
Os Tafssir em língua árabe:
فَأَعۡرَضُواْ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ سَيۡلَ ٱلۡعَرِمِ وَبَدَّلۡنَٰهُم بِجَنَّتَيۡهِمۡ جَنَّتَيۡنِ ذَوَاتَيۡ أُكُلٍ خَمۡطٖ وَأَثۡلٖ وَشَيۡءٖ مِّن سِدۡرٖ قَلِيلٖ
Sai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan: talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan.
Os Tafssir em língua árabe:
ذَٰلِكَ جَزَيۡنَٰهُم بِمَا كَفَرُواْۖ وَهَلۡ نُجَٰزِيٓ إِلَّا ٱلۡكَفُورَ
Wancan, da shi Muka yi musu sakamako sabõda kãfircinsu. Kuma lalle, bã Mu yi wa kõwa[1] irin wannan sakamako, fãce kafirai.
[1] Allah na saka wa kãfirai gwargwadon aikinsu, kuma Yanã yin falala ga mũmini da kyautar da ta fi aikinsa.
Os Tafssir em língua árabe:
وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُمۡ وَبَيۡنَ ٱلۡقُرَى ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَا قُرٗى ظَٰهِرَةٗ وَقَدَّرۡنَا فِيهَا ٱلسَّيۡرَۖ سِيرُواْ فِيهَا لَيَالِيَ وَأَيَّامًا ءَامِنِينَ
Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin[1] garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu."
[1] Tafiya a tsakãnin Yemen, ƙasar Saba'awa da Syria, watau Sham, ƙasã mai albarka, ƙasarAnnabãwa kuma ƙasa mai yawan ruwa da itãce.
Os Tafssir em língua árabe:
فَقَالُواْ رَبَّنَا بَٰعِدۡ بَيۡنَ أَسۡفَارِنَا وَظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَ وَمَزَّقۡنَٰهُمۡ كُلَّ مُمَزَّقٍۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ
Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce[1] su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya.
[1] Muka sanya saba'ãwa suka wãtse a cikin waɗansu ƙasãshe sabõda ruwa ya halaka ƙasãrsu, sa'an nan kuma ta bũshe bãbu wadãta, har ana cewa 'Sun yi rarrabar Saba'ãwa' watau sun wãtse.
Os Tafssir em língua árabe:
وَلَقَدۡ صَدَّقَ عَلَيۡهِمۡ إِبۡلِيسُ ظَنَّهُۥ فَٱتَّبَعُوهُ إِلَّا فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Kuma lalle, haƙĩƙa, Iblĩs ya gaskata zatonsa a kansu, sai suka bi shi fãce wani ɓangare na mũminai.
Os Tafssir em língua árabe:
وَمَا كَانَ لَهُۥ عَلَيۡهِم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يُؤۡمِنُ بِٱلۡأٓخِرَةِ مِمَّنۡ هُوَ مِنۡهَا فِي شَكّٖۗ وَرَبُّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَفِيظٞ
Kuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kõme, Mai tsaro ne.
Os Tafssir em língua árabe:
قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا لَهُمۡ فِيهِمَا مِن شِرۡكٖ وَمَا لَهُۥ مِنۡهُم مِّن ظَهِيرٖ
Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su.
Os Tafssir em língua árabe:
 
Tradução dos significados Surah: Saba
Índice de capítulos Número de página
 
Tradução dos significados do Nobre Qur’an. - tradução Hawsia - Abu Bakr Jumi - Índice de tradução

Traduzida por Abu Bakr Mahmoud Jumi. Desenvolvida sob a supervisão do Centro Rowad de Tradução, e está disponível para consulta com o objetivo de oferecer opiniões, avaliação e desenvolvimento contínuo.

Fechar