Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bã za mu shige ta ba har abada matuƙar sun dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dõmin ku yi yãƙi. Lalle ne mu, munã a nan zaune."
(Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtãwa ce a gare su, shekara arba'in, sunã yin ɗimuwa a cikin ƙasa[1]. Sabõda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne fãsiƙai."
[1] Wannan shi ne sakamakon sãɓawar alkawari, da aka ce wa magewaya kada su faɗi abin da suka gani, saboda aƙibar abin, kusan duka sai da suka mutu a cikin halin ɗimuwar.
Kuma karantã musu[1] lãbãrin ɗiya biyu[2] na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne."
[1] Ƙuraishawa ko kuwa al'ummarka. [2] Ɗiyan Ãdamu, biyu, Ƙãbĩla da Hãbĩla. Asalin maganar kamar yadda aka ruwaito, mãtar Ãdamu, Hauwa'u, tana haifuwar namiji da mace a kowane ciki, wajen aure sai a shirɓata dõmin bãbu wasu mutãne sai su. Sai Ƙabĩla ya ƙi yarda a bai wa Hãbĩla 'yar'uwarsa, har Ãdam ya sanya su yin baiko da abin sana'arsu. Ƙãbĩla manõmi ne, ya bãyar da munãna daga kãyan nõmansa, shi kuma Hãbĩla ya bãyar da rãgo mai kyau dõmin sana'arsa kiwo ne. Sai wuta ta sauko ta ɗauki rãgon Hãbĩla, alãmar karɓa. Wannan kuwa ya ɗauki Ƙãbĩla ga tunãnin kashe shi. Laifi guda yana sabbaba wasu laifuka mãsu yawa.
"Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai.
Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan'uwana?" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã.
Tradução dos significados do Nobre Qur’an. - tradução Hawsia - Abu Bakr Jumi - Índice de tradução
Traduzida por Abu Bakr Mahmoud Jumi. Desenvolvida sob a supervisão do Centro Rowad de Tradução, e está disponível para consulta com o objetivo de oferecer opiniões, avaliação e desenvolvimento contínuo.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
Resultado de pesquisa:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".