Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma.
Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.
Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, *dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
* Kwanukan Allah, sũ ne masĩfu waɗanda ke sãmun kãfirai waɗanda bã su bin sharĩ'ar Allah. Wãtau Allah Ya umurci Annabi ya gaya wa Musulmi, cewa wanda bã ya tsõron masĩfu sabõda ya ki aiwatar da sharĩ'ar Allah a kansa to kada Musulmi su dãmu da shi, watau kãfiran amãna nã iya bin dõkõkinsu na al'ãda, bãbu ruwan Musulmi matuƙar dai ba su shũka wata fitina ba a gare su. A bãyan haka Allah zai sãka wa kõwa game da aikinsa.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai* (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu).
* Bã Musulmi kawai aka aikowa Manzo ba,ba su kawai aka bã su sharĩ'a ba, kuma aka umurce su da binta ba, Banĩ Isrã'ĩla ma an bã su haka kuma sunɗaukaka a kan mutãne a lõkacin da suka yi aiki da sharĩ'ar, kuma suka ƙasƙanta a lõkacin da suka bar aiki da ita. Musulmi ma haka suke idan sun bar sharĩ'ar da Allah Ya aza su a kanta, zã su ƙasƙanta yadda Yahũdawa suka ƙasƙanta.
Kuma Muka bã su hujjõji na umarni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna).
Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa.
Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã!
Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba.
Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi,* Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba?
* Ilmin Allah bã shi da iyãka, Yanã bũɗa shi ga wanda Ya ga dãma, a inda kõ a lõkacin da Ya ga dãma, amma dai duk ilmin da bai saukar da shi ga Annabi Muhammadu ba, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, to, bã a aiki da shi ga hukunci kõ sharĩ'a, wanda ya bi shi kuwa, to, ya ɓace ga aikinsa, bã ya cikin shiryayyu mãsu zaman lãfiya a dũniya kuma su shiga Aljanna a Lãhira, dõmin sharaɗin haka shĩne bin sunna. Wanda ya bar sunna kuwa, ya yi kuskuren hanya, bãbu mai shiryar da shi kuma sai Allah idan Yã so shi da rahama, watau Ya sanya shi ya tũba. Wannan ya nũna cewa ibãda da mu'ãmala duka ɗaya suke ga Musulunci, barin aiki da sharĩ'a a cikin kõwannensu duka, kãfirci ne ga wanda ya halatta yin haka nan. Mafi yawan kãfircin da ya sãmi Musulmi, ya zo musu ne ta hanyar barin mu'ãmalõli da sharĩ'ar Allah, suka ɗauki yin salla da mai kama da ita, shi kaɗai ne Musulunci, suka kãfirta da haka.
Kuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa (da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato.
Kuma idan anã karanta ãyõyin Mu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
Ka ce: "Allah ne ke rãyar* da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
* Wãtau ba kũ ne ke rãyuwa da kanku ba, sai an rãyar da ku, haka ne ga mutuwa, bã ku ne ke mutuwa da kanku ba, sai an matar da ku, kuma Allah Shi Ɗaya ke iya rãyarwa ko matarwa. To, yãya ne zã ku ƙi bin sharĩ'ar da Ya umurce ku da binta?.
"Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra."
Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. (A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩ Nã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?"
"Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."'
"Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba."
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
Igisubizo cy'ibyashatswe:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".