Check out the new design

Ibisobanuro bya qoran ntagatifu - Ibisobanuro bya Qur'an Ntagatifu mu rurimi rw'igihawusa - Abu Bakr Jomy. * - Ishakiro ry'ibisobanuro

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Ibisobanuro by'amagambo Isura: Al Maidat   Umurongo:
سَمَّٰعُونَ لِلۡكَذِبِ أَكَّٰلُونَ لِلسُّحۡتِۚ فَإِن جَآءُوكَ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُمۡ أَوۡ أَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡۖ وَإِن تُعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ فَلَن يَضُرُّوكَ شَيۡـٔٗاۖ وَإِنۡ حَكَمۡتَ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُقۡسِطِينَ
Mãsu yawan saurãre[1] ga ƙarya ne, mãsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka, sai ka yi hukunci a tsakãninsu kõ ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira daga gare su, to, bã zã su cuce ka da kõme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai ka hukunta a tsakãninsu da ãdalci. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu ãdalci.
[1] An bai wa Annabi zaɓi da ya yi hukunci ko kada ya yi, a tsakãnin kafirai biyu idan sun yarda da hukuncinsa. Wannan dãmã tana aiki a kotunan Musulmi ga abin da ya shafi haƙƙoƙi kawai, amma ga 'jara'im a ƙasar Musulmi tilas sai a bi shari'ar Musulunci domin tsaron aminci, sai dai kafiri yana iya shan giyarsa, ga misãli a ɓoye banda a cikin jama'a. Haka kuma laifuka na al'adunsu kuma Musulmi bã za su taɓa masu su ba, sai su yi hukuncinsu a tsakãninsu.
Ibisobanuro by'icyarabu:
وَكَيۡفَ يُحَكِّمُونَكَ وَعِندَهُمُ ٱلتَّوۡرَىٰةُ فِيهَا حُكۡمُ ٱللَّهِ ثُمَّ يَتَوَلَّوۡنَ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۚ وَمَآ أُوْلَٰٓئِكَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci, alhãli a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan? waɗannan bã muminai ba ne!
Ibisobanuro by'icyarabu:
إِنَّآ أَنزَلۡنَا ٱلتَّوۡرَىٰةَ فِيهَا هُدٗى وَنُورٞۚ يَحۡكُمُ بِهَا ٱلنَّبِيُّونَ ٱلَّذِينَ أَسۡلَمُواْ لِلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلرَّبَّٰنِيُّونَ وَٱلۡأَحۡبَارُ بِمَا ٱسۡتُحۡفِظُواْ مِن كِتَٰبِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ عَلَيۡهِ شُهَدَآءَۚ فَلَا تَخۡشَوُاْ ٱلنَّاسَ وَٱخۡشَوۡنِ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِـَٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗاۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji tsõron mutãne kuma ku ji tsõroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyoyi Na. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai.
Ibisobanuro by'icyarabu:
وَكَتَبۡنَا عَلَيۡهِمۡ فِيهَآ أَنَّ ٱلنَّفۡسَ بِٱلنَّفۡسِ وَٱلۡعَيۡنَ بِٱلۡعَيۡنِ وَٱلۡأَنفَ بِٱلۡأَنفِ وَٱلۡأُذُنَ بِٱلۡأُذُنِ وَٱلسِّنَّ بِٱلسِّنِّ وَٱلۡجُرُوحَ قِصَاصٞۚ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِۦ فَهُوَ كَفَّارَةٞ لَّهُۥۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ
Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (anã kashe) rai sabõda rai, kuma (anã ɗebe) idõ sabõda idõ, kuma (ana katse) hanci sabõda hanci, kuma kunne sabõda kunne kuma haƙori sabõda haƙõri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai.
Ibisobanuro by'icyarabu:
 
Ibisobanuro by'amagambo Isura: Al Maidat
Urutonde rw'amasura numero y'urupapuro
 
Ibisobanuro bya qoran ntagatifu - Ibisobanuro bya Qur'an Ntagatifu mu rurimi rw'igihawusa - Abu Bakr Jomy. - Ishakiro ry'ibisobanuro

Yasobanuwe na Abu Bakr Mahmoud Gumi. Byakosowe bihagarariwe n'ikigo Rowad cy'ubusobanuzi bw'inyigisho z'idini ya islam, wanabibona mu buryo bworoshye buhoraho mu rwego rwo kubitanga ibitekerezo no kubikosora.

Gufunga