Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyãwa: "Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutãne* mãsu tsananin yãƙi (dõmin) ku yãƙe su kõ kuwa su musulunta. To, idan kun yi ɗã'a, Allah zai kãwo muku wata ijãra mai kyau, kuma idan kuka jũya bãya kamar yadda kuka jũya a gabãnin wancan, zai azãbtã ku, azãba mai raɗadi."
* Abũbakar zai kira su dõmin su yãƙi mutãnen Musailama, ko kuma su yãƙi Rũmu da fãrisa a bãyan rãyuwar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi a gidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya bãya, (Allah) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi.
Lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yarda da muminai a lõkacin da suke yi maka mubãya, a* a ƙarƙashin itãciyar nan dõmin Yã san abin da ke cikin zukãtansu sai Yã saukar da natsuwa a kansu, kuma Ya sãka musu da wani cin nasara makusanci.
* A bãyan da Annabi ya sauka a Hudaibiyya, ya kirãyi Khuraish bn Umaiya el Khuzã'i ya aike shi Makka ya azã shi a kan rãƙuminsa dõmin ya gaya wa shugabanninsu cewa yãtaho Umra ne, bai zo da yãƙi ba. Sai suka sõke rãƙumin Annabi, kuma suka yi nufin kashe Khuraish amma Ahãbish suka hana su, ya zo ya gaya wa Annabi. Sa'an nan Annabi ya kira Umar bn Khattãb dõmin ya aika shi zuwa Makka, sai ya ce: "Ya Manzon Allah inã tsõron raina ga Ƙuraishãwa, bãbu banĩ Adiyyin bn Ka'ab a Makka balle su kare ni daga gare su, amma inã nũna maka wani mutum wanda ya fĩ ni dangi a cikinta shĩ ne Usman bn Affãn." Sai Annabi ya kira Usman ya aike shi zuwa ga Abi sufyãn da shugabannin Ƙuraish, ya bã su lãbãrin cewa bai zo yãƙi ba. ya taho ne dõmin ziyãra kawai ga wannan Ɗãki dõmin ya girmama alfarmarsa. Ya rubũta masa takarda ya tafi da ita. Kuma ya umurce shi da ya yi bushãra ga Musulmi mãsu rauni, cewa cin nasara yã yi kusa, kuma Allah zai ɗaukaka addininsa. Usman ya fita ya tafi Makka ya iske cewa Ƙuraishãwa sun haɗu a kan hana Annabi shiga Makka. Abban bn sa'ĩd bn Asi ya haɗu da Usman a lõklcin shigarsa Makka, sai ya ɗauke shi a kan rãƙumarsa, ya bã shi maƙwabtaka dõmin kada a kashe shi, har ya kai takardar Annabi. Suka nãce cewa Annabi bã zai shiga ba suka ce wa Usmãn: "Idan yanã son ɗawãfi sai ya yi," Sai ya ce bã zai yi ba sai Manzon Allah ya yi. Musulmi suka ce: "Usmãn ya ji daɗi yã yi ɗawafi," sai Annabi ya ce: "Ban yi zaton Usmãn zai yi ba." Sa'an nan lãbãri ya zo wa Annabi, cewa an kashe Usmãn sabõda haka Annabi ya ce: "Idan sun kashe shi, sai mun yaƙe su." Wannan ya sa aka yi masa mubãya'a a ƙarƙashin itãciyar ɗalh mai kama da farar ƙaya. A bãyan haka Annabi ya aza hannunSa na hagu a kan hannunsa na dãma, ya ce: "Gã hannun Usmãnu." Mãsu mubãya'a dubũ da ɗari uku kõ ɗari huɗu ne, da cewa za su yi yãƙi da Ƙuraishawa, bã zãsu gudu ba, sai dai su mutu. Daga nan shugabancin ya tabbata. Umar bn Khattãb yã sanya an sãre itãciyar nan dõmin mutãne sun fãra salla a ƙarƙashinta. Ba a yi yãƙi ba, sai aka yi sulhu. Annabi ya kõma a shekara mai zuwa yã yi Umra.
Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta* muku wannan. Kuma Ya kange** hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya.
* Cin nasara makusanci, shĩ ne cin Haibara, a bãyan kõmawar Annabi Madĩna a ƙarshen zul Hajji. Sa'an nan ya fita wajen ƙarshen Muharram shekara ta bakwai. Aka samo ganĩma mai yawa. Waɗansu ganĩmõmi na waɗansu ƙasãshen da zã a ci a nan gaba har ƙarshen dũniya. Ganĩmar Haibara ita ce aka gaggauta. ** A lõkacin da Annabi ya fita daga Madĩna zuwa Hudaibiyya Allah Ya kange hannuwan Yahũdãwa daga iyãlan Musulmi na cikin Madĩna, in dã bã dõmin haka ba sai su je su fãɗa su da kashi da kãmu. Sai Allah Ya jefa tsõro a cikin zukãtansu.
Da waɗansu (ganĩmõmin) *da bã ku da ĩko a kansu lalle Allah Ya kẽwaye su da saninSa, kuma Allah Ya kasance Mai ikon yi ne a kan dukan kõme.
* Ganĩma da aka yi musu gaggãwa da ita, ita ce Haibara. Ganĩma wadda ba su da ĩko da ita, ita ce sauran ƙasãshen dũniya inda Musulmi suka ci, suka mallake shi, na ƙasar Rumãwa da farisãwa da Masar da sauransu.
పవిత్ర ఖురాన్ యొక్క భావార్థాల అనువాదం - హౌసా అనువాదం - అబూ బక్ర్ జూమీ - అనువాదాల విషయసూచిక
దీనిని అబూ బకర్ మహ్మూద్ జోమీ అనువదించారు. ఇది రువాద్ అనువాద కేంద్రం యొక్క పర్యవేక్షణలో అభివృద్ధి పరచబడింది. మరియు పాఠకులు తమ అభిప్రాయాలను తెలియజేయడానికి మూలఅనువాదాన్ని పొందుపరచబడుతుంది. మరియు నిరంతరాయంగా అభివృద్ధి మరియు అప్డేట్ కార్యక్రమం కొనసాగుతుంది.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
అన్వేషణ ఫలితాలు:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".