Check out the new design

قرآن کریم کے معانی کا ترجمہ - ہاؤسا ترجمہ - ابو بکر جومی * - ترجمے کی لسٹ

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

معانی کا ترجمہ سورت: مؤمنون   آیت:
مَا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ
Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
عربی تفاسیر:
ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا تَتۡرَاۖ كُلَّ مَا جَآءَ أُمَّةٗ رَّسُولُهَا كَذَّبُوهُۖ فَأَتۡبَعۡنَا بَعۡضَهُم بَعۡضٗا وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَۚ فَبُعۡدٗا لِّقَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ
Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni!
عربی تفاسیر:
ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَٰرُونَ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ
Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyin Mu da, dalĩli bayyananne.
عربی تفاسیر:
إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمًا عَالِينَ
Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya.
عربی تفاسیر:
فَقَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لِبَشَرَيۡنِ مِثۡلِنَا وَقَوۡمُهُمَا لَنَا عَٰبِدُونَ
Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne."
عربی تفاسیر:
فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡلَكِينَ
Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku.
عربی تفاسیر:
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ لَعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu[1] zã su shiryu.
[1] Banĩ Isrã'ĩla na yanzu idan sun tuna cewa Alƙur'ãni bã shĩ ne farkon littafin sama ba, an bai wa Mũsã wani littafi, su kuma sunã alfahari da shi.
عربی تفاسیر:
وَجَعَلۡنَا ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةٗ وَءَاوَيۡنَٰهُمَآ إِلَىٰ رَبۡوَةٖ ذَاتِ قَرَارٖ وَمَعِينٖ
Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã[1] Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari.
[1] Ãyar Ĩsã da uwarsa ita ce an haife shi bãbu uba. Kuma a lõkacin nan Yahũdu suka so sarkin zãmanin nan ya kashe shi, sai uwarsa ta gudu da shi zuwa Baitil Maƙaddas, kõ Dimashƙa, kõ Falasɗĩnu, inda suka zauna shekara gõma sha biyar har sarkin nan ya mutu.
عربی تفاسیر:
يَٰٓأَيُّهَا ٱلرُّسُلُ كُلُواْ مِنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَٱعۡمَلُواْ صَٰلِحًاۖ إِنِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ
Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi[1] kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
[1] Allah Ya umurci ManzanninSa da cin halat sa'an nan su aikata aikin ƙwarai. Haka kuma Ya umurci Mũminai. Sabõda haka karɓar aiki na ƙwarai an tsayar da shi ne a kan cin halat.
عربی تفاسیر:
وَإِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱتَّقُونِ
Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa.[1]
[1] Taƙawa, ita ce bautawa Allah da abin da Ya yi umurni a bauta Masa, a kan harshenAnnabinsa na zamaninsa. Yanzu bãbu taƙawa sai a cikin Musulunci kawai.
عربی تفاسیر:
فَتَقَطَّعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡ زُبُرٗاۖ كُلُّ حِزۡبِۭ بِمَا لَدَيۡهِمۡ فَرِحُونَ
Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu,[1] kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.
[1] Kõwa ya kãma hanyarsa, al'ummar Musulmi ta zama ƙungiyõyi dabam-dabam, kõwanensu yanã farin ciki da abin da ke gare shi, yanã ganin shi ne mafifici
عربی تفاسیر:
فَذَرۡهُمۡ فِي غَمۡرَتِهِمۡ حَتَّىٰ حِينٍ
To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci.
عربی تفاسیر:
أَيَحۡسَبُونَ أَنَّمَا نُمِدُّهُم بِهِۦ مِن مَّالٖ وَبَنِينَ
Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya,
عربی تفاسیر:
نُسَارِعُ لَهُمۡ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ بَل لَّا يَشۡعُرُونَ
Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri?
عربی تفاسیر:
إِنَّ ٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ خَشۡيَةِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ
Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu,
عربی تفاسیر:
وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ يُؤۡمِنُونَ
Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni,
عربی تفاسیر:
وَٱلَّذِينَ هُم بِرَبِّهِمۡ لَا يُشۡرِكُونَ
Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki,
عربی تفاسیر:
 
معانی کا ترجمہ سورت: مؤمنون
سورتوں کی لسٹ صفحہ نمبر
 
قرآن کریم کے معانی کا ترجمہ - ہاؤسا ترجمہ - ابو بکر جومی - ترجمے کی لسٹ

ابو بکر محمود جومی نے ترجمہ کیا۔ مرکز رواد الترجمہ کے زیر اشراف اسے اپڈیٹ کیا گیا ہے اور اصلی ترجمہ مطالعہ کے لیے فراہم کیا جا رہا ہے تاکہ قارئین کی رائے لی جائے اور مسلسل اپڈیٹ اور اصلاح کا کام جاری رہے۔

بند کریں