Traduction des sens du Noble Coran - Traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy * - Lexique des traductions

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Traduction des sens Verset: (52) Sourate: AL-HAJJ
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٖ وَلَا نَبِيٍّ إِلَّآ إِذَا تَمَنَّىٰٓ أَلۡقَى ٱلشَّيۡطَٰنُ فِيٓ أُمۡنِيَّتِهِۦ فَيَنسَخُ ٱللَّهُ مَا يُلۡقِي ٱلشَّيۡطَٰنُ ثُمَّ يُحۡكِمُ ٱللَّهُ ءَايَٰتِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri,* sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyin Sa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
* Annabãwa sukan yi wahami ga tunãninsu, su yi zaton wani abu daidai ne alhãli kuwa a wurin Allah bã haka Yake nufi ba. A kan wannan, sai shakka ta shiga wãwã a kansu, amma wanda ke da ĩmãni to bã zai rikice ba sabõda wannan kuskure dõmin Allah bã Ya barin su a kansa, sai Ya gyãra abin da ke ciki na wahami. Misãli ƙissar Yũnusu, da ƙissar Annabi a cikin suratu Abasa, da ƙissar Ibrãhim wajen jãyayya da malã'ikun da aka aika zuwa alƙaryõyin mutãnen Lũɗu.
Les exégèses en arabe:
 
Traduction des sens Verset: (52) Sourate: AL-HAJJ
Lexique des sourates Numéro de la page
 
Traduction des sens du Noble Coran - Traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy - Lexique des traductions

ترجمة معاني القرآن الكريم إلى اللغة الهوسا، ترجمها أبو بكر محمود جومي. تم تصويبها بإشراف مركز رواد الترجمة، ويتاح الإطلاع على الترجمة الأصلية لغرض إبداء الرأي والتقييم والتطوير المستمر.

Fermeture