Check out the new design

Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy * - Lexique des traductions

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Traduction des sens Sourate: Muhammad   Verset:
إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَتَمَتَّعُونَ وَيَأۡكُلُونَ كَمَا تَأۡكُلُ ٱلۡأَنۡعَٰمُ وَٱلنَّارُ مَثۡوٗى لَّهُمۡ
Lalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi (adũniya) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su.
Les exégèses en arabe:
وَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ هِيَ أَشَدُّ قُوَّةٗ مِّن قَرۡيَتِكَ ٱلَّتِيٓ أَخۡرَجَتۡكَ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡ فَلَا نَاصِرَ لَهُمۡ
Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su.
Les exégèses en arabe:
أَفَمَن كَانَ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّهِۦ كَمَن زُيِّنَ لَهُۥ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُم
Shin, wanda ya kasance a kan wata hujja daga Ubangijinsa, zai zama kamar wanda aka ƙawãce masa mugun aikinsa, kuma suka bibbiyi son zũciyõyinsu?
Les exégèses en arabe:
مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ فِيهَآ أَنۡهَٰرٞ مِّن مَّآءٍ غَيۡرِ ءَاسِنٖ وَأَنۡهَٰرٞ مِّن لَّبَنٖ لَّمۡ يَتَغَيَّرۡ طَعۡمُهُۥ وَأَنۡهَٰرٞ مِّنۡ خَمۡرٖ لَّذَّةٖ لِّلشَّٰرِبِينَ وَأَنۡهَٰرٞ مِّنۡ عَسَلٖ مُّصَفّٗىۖ وَلَهُمۡ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَمَغۡفِرَةٞ مِّن رَّبِّهِمۡۖ كَمَنۡ هُوَ خَٰلِدٞ فِي ٱلنَّارِ وَسُقُواْ مَآءً حَمِيمٗا فَقَطَّعَ أَمۡعَآءَهُمۡ
Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu?
Les exégèses en arabe:
وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُ إِلَيۡكَ حَتَّىٰٓ إِذَا خَرَجُواْ مِنۡ عِندِكَ قَالُواْ لِلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ مَاذَا قَالَ ءَانِفًاۚ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡ
Kuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare* zuwa gare ka, har idan sun fita daga wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi "Mẽne ne (Muhammadu) ya fãɗa ɗazu?" Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shãfe haske daga zukãtansu, kuma suka bi son zũciyõyinsu.
* Wannan shĩ ya nũna cewa wani ɗan rahõto ba zai iya fahimtar gaskiya ba, matuƙar anã aikin Allah da gaskiya. Allah na sanya tsõro a cikin zukãtan kãfirai.
Les exégèses en arabe:
وَٱلَّذِينَ ٱهۡتَدَوۡاْ زَادَهُمۡ هُدٗى وَءَاتَىٰهُمۡ تَقۡوَىٰهُمۡ
Kuma waɗannan da suka nẽmi shiryuwa (Allah) Ya ƙara musu shiryuwarsu, kuma Yã bã su (sakamakon) taƙawarsu.*
* Taƙawa, ita ce bin umarnin Allah da nĩsantar haninsa sabõda haka abin da Allah ke bai wa mai taƙawa, shi ne sakamkon aikinsa wanda ya yi daidai da sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare Shi.
Les exégèses en arabe:
فَهَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأۡتِيَهُم بَغۡتَةٗۖ فَقَدۡ جَآءَ أَشۡرَاطُهَاۚ فَأَنَّىٰ لَهُمۡ إِذَا جَآءَتۡهُمۡ ذِكۡرَىٰهُمۡ
To shin sunã jiran (wani abu)? Fãce Sa'a ta jẽ musu bisa abku. dõmin lalle sharuɗɗanta sun zo. To, yãya tunãwarsu* take, idan har ta jẽ musu?
* Tunãwarsu da wa'aztuwarsu ga Sa'a bã zai yi musu amfãni ba, a bãyan tã je musu. Wa'azi bã ya amfãni, sai idan wanda aka yi wa shi, yã yi aiki da shi a gabãnin mutuwa ta je masa.
Les exégèses en arabe:
فَٱعۡلَمۡ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مُتَقَلَّبَكُمۡ وَمَثۡوَىٰكُمۡ
Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka,* (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.
* An umurci Annabi ya nemi gãfara dõmin mutãne su yi kõyi da shi, dõmin Allah Ya riga ya tsare shi daga zunubi a gabãni da bayan Manzanci.
Les exégèses en arabe:
 
Traduction des sens Sourate: Muhammad
Lexique des sourates Numéro de la page
 
Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy - Lexique des traductions

Traduite par Abou Bakr Mahmoud Jomi. Développement achevé sous la supervision du Centre Rouwwâd At-Tarjamah (Les Pionniers de la Traduction). La traduction originale peut-être consultée en vue de donner une opinion, une évaluation et dans le cadre du développement continu.

Fermeture