Traduction des sens du Noble Coran - Traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy * - Lexique des traductions

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

Traduction des sens Verset: (5) Sourate: AL-JOUMOU’AH
مَثَلُ ٱلَّذِينَ حُمِّلُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ ثُمَّ لَمۡ يَحۡمِلُوهَا كَمَثَلِ ٱلۡحِمَارِ يَحۡمِلُ أَسۡفَارَۢاۚ بِئۡسَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen* nan da suka ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai.
* Tir da wanda ya yi siffa da irin siffõfin Yahũdu daga Musulmi wajen ɗaukar karãtun Alƙur'ãni amma kuma bai yi aiki da shi ba. Yahaya bn Yamãni ya ce: "Sunã rubuta nadĩsi bã su fahimtarsa, kuma bã su kula da ma' anarsa." Watau sunã wahala wajen ɗaukar ilmin da aka ɗõra musu ɗaukarsa amma kuma bã su yin amfãni da shi a wajen aikinsu da mu'ãmalõlinsu.
Les exégèses en arabe:
 
Traduction des sens Verset: (5) Sourate: AL-JOUMOU’AH
Lexique des sourates Numéro de la page
 
Traduction des sens du Noble Coran - Traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy - Lexique des traductions

ترجمة معاني القرآن الكريم إلى اللغة الهوسا، ترجمها أبو بكر محمود جومي. تم تصويبها بإشراف مركز رواد الترجمة، ويتاح الإطلاع على الترجمة الأصلية لغرض إبداء الرأي والتقييم والتطوير المستمر.

Fermeture