Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske*, sa'an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.
* Duffai na dare da zãlunci da bin hukunce-hukuncen al'ãdu, haske kuma shĩ ne na taurãri da wuta da shari'u na Littãfi da annabci.
Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabãninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tanã ta zuba, kuma Muka sanya kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sa'an nan Muka halakã su sabõda zunubansu kuma Muka ƙãga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu?
Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce: "Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne."
Suka ce: "Don me ba a saukar da wani malã'ika ba a gare shi?" to dã Mun saukar da malã'ika haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin* sa'an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba.
* Dã an hukunta al'amari da halakarsu, dõmin idan malã'ika ya sauka ga mutãnen da ake yi wa wa'azi bayyane, to, halakarsu tã je ke nan.
Ka ce: "Na wãne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Na Allah ne." Yã wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yanã tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ ba zã su yi ĩmani ba."
Ka ce: "Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhãli Allah ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?" Ka ce: "Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki."
"Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi."
Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirka"
Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa* kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.
* Yahũdu da Nasãra sunã sanin Annabi Muhammadu tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da abin da ya zo da shi na Alƙur'ãni, kamar yadda suka san ɗiyan tsatsõnsu; kamar yadda Abdullahi ɗan Sallãmi ya ce wa Umar: "Lalle ne na san shi a lõkacin da na gan shi, kamar yadda nake sanin ɗãna, kuma lalle ne, ni, mãfi tsananin sani ne ga Muhammadu fiye da ɗãna.".
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."
Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu ƙaryata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai."
Ã'aha, abin da suka kasance suna ɓõyẽwa, daga gabãni, ya bayyana a gare su. Kuma dã an mayar da su, lalle dã sun kõma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
Kuma dã kana gani, a lõkacin da aka tsayar da su ga UbangiJinsu, Ya ce: "Ashe wannan bai zama gaskiya ba?" Suka ce: "Nã'am, muna rantsuwa da Ubangijinmu!" Ya ce: "To ku ɗanɗani azaba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci."
Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara, har idan Sa'a ta je musu kwatsam, sai su ce: "Yã nadãmarmu a kan abin da muka yi sakaci a cikinta!" Alhãli kuwa su suna ɗaukar kayansu masu nauyi a kan bayayyakinsu. To, abin da suke ɗauka yã mũnana.
Lalle ne Muna sani cewa haƙĩƙa, abin da suke faɗa yana ɓãta maka rai. To, lalle ne su, bã su ƙaryata ka (a cikin zukatansu) kuma amma azzãlumai da ãyõyin Allah suke musu.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an ƙaryata manzanni daga gabãninka, sai suka yi haƙuri a kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cũtar da su, har taimakon Mu ya je musu, kuma babu mai musanyãwa ga kalmõmin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da kai) ya zo maka daga lãbãrin (annabãwan) farko.
Kuma idan yã kasance cewa finjirewarsu tã yi nauyi a gare ka, to, idan kana iyãwa, ka nemi wani ɓullõ a cikin ƙasa, kõ kuwa wani tsãni a cikin sama dõmin ka zo musu da wata ãyã, (sai ka yi). Kuma dã Allah Yã so haƙĩƙa dã Yãtãra su a kan shiriya. Sabõda haka, kada lalle ka kasance daga jãhilai.
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da ãyã ba, a kansa, daga Ubangjinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Mai ĩko ne a kan Yasaukar da ãyã, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba."
Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa kuma bãbu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa fãce al'umma ne misãlanku. Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi, sa'an nan kuma zuwa ga Ubangjinsu ake tãra su.
Kuma waɗanda suka ƙaryata gameda ãyõyin Mu, kurãme ne kuma bebãye, acikin duffai. Wanda Allah Ya so Yanã ɓatar da shi, kuma wanda Ya so zai sanya shi a kan hanya madaidaiciya.
Ka ce: "Shĩn, kun gan ku, idan azãbar Allah ta zo muku, kõ Sã'ar Tashin Kiyãma ta zo muku, shin wanin Allah kuke kira, idan dai kun kasance mãsu gaskiya?"
To, don me, a lõkacin da tsananin Mu ya jẽ musu ba su yi tawãlu'i ba? Kuma amma zukatansu sun ƙẽƙashe kuma shaiɗan yã ƙawãta musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Sa'an nan kuma alõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũɗe, a kansu, ƙõfõfin dukkan kõme, har a lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yi tsuru tsuru.
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya riƙe jinku, da gannanku, kuma Ya sanya hãtimi a kan zukãtanku, wane abin bauttãwa ne, wanin Allah, zai jẽ muku da shi?" Ka dũba yadda Muke sarrafaãyõyi, Sa'an nan kuma sũ, sunã finjirẽwa.
Kuma bã Mu aikãwa da manzãnni fãce mãsu bayar da bushãra, kuma mãsu gargaɗi. To, wanda ya yi ĩmãni kuma yagyãra aiki, to, babu tsõro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki.
Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni." Ka ce: "Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni?"
Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masõyi baicin Sa, kuma babu mai cẽto, tsammãninsu, sunã yin taƙawa.
Kuma kada ka kõri waɗanda* suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.
* Musulunci addinin Allah ne, wanda yake faƙĩrin dũkiya da mawãdãcinta, duka ɗaya suke a gare shi. Sabõda haka wanda duka ya rigayi wani a cikinsu, to, bã za a kõre shi ba dõmin ɗayan ya shiga. Allah ĩmãni Yake so, kõ daga wãne irin mutum yake, bã Ya bukãtar dũkiya.
Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sãshensu da sãshe, dõmin su ce: "Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakãninmu?" Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga mãsu gõdiya?
Kuma idan waɗanda suke yin ĩmãni da ãyõyinMu suka jẽ maka, sai ka ce: "Aminci ya tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cẽwa lalle ne wanda ya aikata aibi da jãhilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tũba daga bãyansa, kuma ya gyãra, to, lalle Shi, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
Ka ce: "Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin Allah." Ka cc: "Ba ni bin son zũciyõyinku, (dõmin in nã yi haka) lalle ne, nã ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba."
Ka ce: "Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke nẽman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin mãsu rarrabẽwa."
Ka ce: "Lalle ne, dã a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugãwa da shi, haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin, a tsakãnina da tsakãninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga azzũlumai."
Kuma a wurin Sa mabũdan* gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa.
* Lõkacin aukuwar abũbuwa na alheri da na azãba da rãyuwa da mutuwa da sauransu, bãbu wanda ya san su sai Allah. Wanda ya ce ya san wani abu na gaibi alhãli kuwa shĩ ba wani manzon Allah ba, to, kãfiri ne. haka kuma wanda yake cewa, Annabãwã sun san dukkan gaibi, kamar yadda Allah Ya sani, shĩ mã kãfiri ne.
Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar* rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
* Karɓar rai da dare dõmin barci, tãyarwa a cikin ranã, watau yini daga barci. Akwai misalta dare da dũniya kuma rãna da Rãnar Ƙiyãma, kuma mutuwa da barci, da farkawa daga barci da Tãshin Ƙiyãma. Ãyar tã ƙunsa asĩrai mãsu yawa.
Kuma Shĩ ne Mai rinjãya bisa ga bãyinSa, kuma Yanã aikan mãsu tsaro a kanku, har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayanku, sai manzannin Mu su karɓi ransa alhãli su ba su yin sakaci.
Ka ce: "Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kunã kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓõye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan (masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga mãsu gõdiya?'"
Ka ce: "Shĩ ne Mai ĩko a kan Ya aika da wata azãba a kanku daga bisanku, kõ kuwa daga ƙarƙashin ƙafãfunku, kõ kuwa Ya gauraya ku ƙungiyõyi, kuma Ya ɗanɗanã wa sãshenku masĩfar sãshe." "Ka dũba yadda Muke sarrafa ãyõyi, tsammãninsu sunã fahimta!"
Kuma idan kã ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kũtsa a cikin wani lãbãri waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunãwa tãre da mutãne azzãlumai.
Kuma babu wani abu daga hisãbinsu (mãsu kutsãwa a cikin ayõyin Allah (a kan mãsu taƙawa amma akwai tunãtarwa (a kansu), tsãmmãninsu (mãsu kutsawar) zã su yi taƙawa.
Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wãsa* da wargi alhãli rãyuwar dũniya tã rũɗe su, kuma ka tunãtar game da shi (Alƙur'ãni): Kada a jẽfa raia cikin halaka sabõda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai cẽto; kuma, kõ ya daidaita dukan fansa, ba zã a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammãni sabõda abin da suka tsirfanta; sunã da wani abin shã daga ruwan zãfi, da wata azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
* Suka sanya sãbabbin abũbuwa a cikinsa, waɗanda suke bãbu su a cikinsa, kamar Khawãrijãwa da sãshen wanda ke da'awar danganuwa zuwa ga sãlihai inda suka sanya Ɗarĩka mai sãdarwa zuwa ga Allah, bandiri da algaita, kuma suka fãra abũbuwa waɗanda ba su halatta ba ga shari'a. Daga Sãwĩ.
Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'"* Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai."
* Shi kuma bã ya karɓãwa balle ya nufi wurin shiriyar da suke kiran sa ya tafi, sabõda yã riga yã fãɗi daga sama zuwa ƙasa, kuma ɗimuwa tã kãmã shi.
Kuma Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da mulkinSa, kuma a Rãnar da Yake cẽwa: "Ka kasance," sai abu ya yi ta kasancẽwa. Maganar Sa ce gaskiya, kuma gare Shi mulki yake a Rãnar da ake bũsa a cikin ƙaho. Masanin fake da bayyane ne, Kuma Shi ne Mai hikima Masani.
Kuma a lõkacin da Ibrãhĩma ya ce wa ubansa Ãzara: "Shin, kanã riƙon gumãka abũbuwan bautãwa? Lalle nĩ, inã ganin ka kai damutã- nenka, a cikin ɓata bayyananniya."
To, a lõkacin da dare ya rufe a kansa, ya ga wani taurãro, ya ce: "Wannan ne, ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya faɗi, ya ce: "Ba ni son mãsu fãɗuwa."
Sa'an nan a lõkacin da ya ga watã yanã mai bayyana, ya ce: "Wannan ne Ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya fãɗi, ya ce: "Lalle ne idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa, inã kasancẽwa daga mutãne ɓatattu."
Sa'an nan a lõkacin da ya ga rãnã tanã bayyana, ya ce: "Wannan shĩ ne Ubangijina, wannan ne mafi girma?" Sa'an nan a lõkacin da ta fãɗi, ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki."
Kuma mutãnensa suka yi musu da shi. Ya ce: "Shin kunã musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhãli kuwa Yã shiryai da ni? Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, fãce idan Ubangijina Yã so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõme da ilmi. Shin, ba zã ku yi tunãni ba?"
"Kuma yãyã nake jin tsõron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsõron cẽwa lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane ɓangare daga sãshen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kunã sani?"
Kuma waccan ita ce hujjar Mu, Mun bayãr da ita ga Ibrãhĩma a kan mutãnensa. Munã ɗaukaka wanda Muka so da darajõji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani.
Kuma Muka bã shi Is'hãƙa da Yãƙubu, dukansu Mun shiryar, kuma Nũhu Mun shiryar da shi a gabãni, kuma daga zuriyarsa akwai Dãwũda da Sulaimãnu da Ayyũba, da Yũsufu da Mũsã da Hãrũna, kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Waɗancan ne waɗanda Muka bai wa Littãfi da hukunci da Annabci. To idan waɗannan (mutãne) sun kãfirta da ita, to, haƙĩƙa, Mun wakkala wasu mutãne gare ta, ba su zama game da ita kãfirai ba.
Waɗancan ne Allah Ya shiryar, sabõda haka ka yi kõyi da shiryarsu. Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijãra. Shĩ (Alƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ga tãlikai."
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lõkacin da suka ce: "Allah bai saukar da kõme ba ga wani mutum." Ka ce: "Wãne ne ya saukar da Littãfi wanda Mũsã ya zo da shi, yanã haske da shiriya ga mutãne, kunã sanya shi takardu, kũna bayyana su, kuma kunã ɓõye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah,"* sa'an nan ka bar su a cikin sharhõliyarsu sunã wãsã.
* Allah ne Ya saukar da shi, sabõda haka ba zai zama abin mãmãki ba ko abin musu ga Ya saukar da wani littãfi kamar Alƙur'ãni ga wani mutum a bãyan Taurãta ga Musã. Kuma a cikin Taurãtar ba a ce ita ce ƙarshen Littãfin Allah ba kuma Mũsã bã shi ne ƙarshen Annabawa ba.
Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda yake a gabansa ne, kuma dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda yake gefenta. Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da Lãhira sunã ĩmãni da shi (Alƙur'ãni), kuma sũ, a kan sallarsu, sunã tsarẽwa.
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai."
Kuma lalle ne haƙĩƙa, kun zo Mana ɗai ɗai, kamar yadda Muka halittã ku a farkon lõkaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma ba Mu gani a tãre da kũ ba, macẽtanku waɗanda kuka riya cẽwa lalle ne sũ, a cikinku mãsu tãrayya ne. Lalle ne, hãƙĩƙa, kõme yã yanyanke a tsakãninku, kuma abin da kuka kasance kunã riyãwa ya ɓace daga gare ku.
Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai,* wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?
* Mai ĩmãni daga kãfiri kõ kãfiri daga mai ĩmãni, da mai arziki daga matalauci da matalauci daga mawadãci, sarki daga talaka da talaka daga sarki,da mai sanyi daga mai zãfi ko mai zãfi daga mai sanyi, haka dai ga kõme Allah Yanã fitar da kĩshiyarsa.
Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.
Kuma Shi ne Ya ƙãga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke fahimta.
Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren),* kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni.
* Allah na halitta kõren ganye daga hasken rãnã, sa'an nan Ya halitta gãrin ƙwãyã daga kõren.
Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa.
Mafarin* halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?
* Shi ne wanda Ya fãri halittarsu bã da Yã kõya daga wani ba. Sautin jan wasalin fa zaiyi sama dõmi bambanci daga mafãri watau sababin abu, ana mĩƙe sautin maddi a gare shi.
Lalle ne abũbuwan lũra sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to, dõmin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yanã a kansa, kuma nĩ, a kanku, bã mai tsaro ba ne.
Kuma kada ku zãgi waɗanda suke kira, baicin Allah, har su zãgi Allah bisa zãlunci, ba, da ilmi ba. Kamar wannan ne Muka ƙawãta ga kõwace al'umma aikinsu, sa'an nan zuwa ga Ubangijinsu makõmarsu take, sa'an nan Ya ba su lãbari da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwõyinsu (cẽwa) lalle ne idan wata ãyã ta jẽmusu, haƙĩƙa, sunã yin ĩmãni da ita. Ka ce: "Abin sani kawai, ãyõyi a wurin Allah suke. Kuma mẽne nezai sanya ku ku sansance cẽwa, lalle ne su, idan ãyõyin sun je, ba zã su yi ĩmãni ba?"
Kuma dã a ce, lalle Mũ Mun saukar da Malã'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tãra dukkan kõme a kansu, gungu-gungu, ba su kasance sunã iya yin ĩmãni ba, sai fa idan Allah Yã so, Kuma amma mafi yawansu sunã jãhiltar haka.
Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra* zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa.
* Wahayin shaiɗãnu sãshensu zuwa ga sãshe da ƙãwata ƙarya ta zama kamar gaskiya. Kamar Shaiɗan ya sanya wasiwãsi: Dã da'awar Annabi gaskiya ce: Ai dã manyan mutãne ne zã su fãra bin ta, ba matalautã ba, kõ kuwa annabi mai sihiri ne dõmin yanã raba miji da mãta, da ɗa da uba. Watau su karkatar da magana, dõmin su karkatar da wãwãye daga bin gaskiya.
Kuma dõmin zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata.
Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi (Alƙur'ãni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakka.
Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya* da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.
* Musulunci kõ Alƙur'ãni ne cikon addinin Allah, babu mai iya zõwa da wani abu sãbo kõ ya ƙãra wani abu a cikin sa ta kõwace hanya kuma bãbu mai iya musanya wani abu a cikinsa. Ya cika ya kammala, sai biya kawai. Annabi ya ce: "Wanda ya yi wani aiki ba da umuruinsa a kan abin da ya aikata ɗin nan ba, to, an mayar masa; ba a karɓaba.".
Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah* kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa.
* An sani daga nan cewa ambaton sũnan Allah wajen yankan dabba wãjibi ne, idan an tuna. Wanda ya manta, anã cin yankansa, amma wanda ya bari da gangan, bã zã a ci yankansa ba.
Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã zã ku ci ba daga abin da aka ambaci sũnan Allah a kansa, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Ya rarrabe, muku daki-daki, abin da Ya haramta a kanku, fãce fa abin da aka bukãtar da ku bisa lalũra zuwa gare shi? Kuma lalle ne mãsu yawa sunã ɓatarwa, da son zũciyõyinsu, ba da wani ilmi ba. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga mãsu ta'addi.
Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa.* Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne.
* Sabõda haka bã a cin yankan majũsu. Anã cin yankan bakitãbe, babu ruwanmu da abin da yake faɗa, tun da Allah Ya halatta mana cin abincinsu alhãli kuwa Ya san sun riga sun musanya addininsu. Idan Musulmi ya bar sũnan Allah da gangan, amma bai ambaci sũnan kõwa ba, to, akwai riwãya biyu game da haka, ci kõ rashin ci. Amma idan ya haɗa sũnan Allah da na wani, to, ba zã a ci ba, dõmin yã yi ridda.
Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya wani haske dõminsa, yanã tafiya da shi, yanã zama kamar wanda misãlinsa yanã cikin duffai, shĩ kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka ƙawãta wa kãfirai abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma kamar wancan ne Mun sanya a cikin kõwace alƙarya, shugabanni sũ ne mãsu laifinta dõmin su yi mãkirci a cikinta, alhãli kuwa ba su yin makirci fãce ga rayukansu, kuma ba su sansancẽwa.
Kuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: "Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa.* Wani wulaƙanci** a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi waɗanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci.
* Manzanci da zãɓin Allah yake, bã da kuɗi kõ'ya'ya kõ kabĩla yake ba, sai a wurin da Allah Ya aza shi. ** Mai girman kai ga bin umurnin Allah, sakamakonsa wulaƙanci ne.
Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa* ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni.
* Mai tãkãwa zuwa sama ƙirjinsa ƙunci yake yi, sabõda iskar numfashi tanã raguwa gare shi. Kuma shi yanã shasshekar gajiya da rashin iska. Wannan ilmi yanã a cikin mu'ujizar Alƙur'ani.
Kuma rãnar da yake tãra su gaba ɗaya (Yanã cẽwa): "Yã jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne." Kuma majiɓantansu daga mutãne suka ce: "Yã Ubangjinmu! Sãshenmu* ya ji dãɗi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!" (Allah) Ya ce: "Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani."
* Haka dai mai laifi a bãyan azãbar laifinsa ta tabbata a kansa bã ya ɓõyewar abin da ya riga ya bayyanã, sai ya faɗa da kansa dõmin ya bayyanar da nadãmarsa a lõkacin da nadãma bã ta da amfãni
Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kãwunanmu." Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai.
Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.*
* Allah bã Ya halaka mutãne sabõda wani laifi, sai bãyan Ya aiki mai gargaɗi ya tafi ya yi musu gargaɗi, sun san laifinsu, sun ƙi bari, sa'an nan azãba ta je musu.
Kuma Ubangijinika Wadãtacce* ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.
* Rashin gaugãwar yin sãkamako ga mãsu laifi sabõda wadãtar Allah ne. Bã shi yin uƙũba dõmin Ya yi fushin an rage masa mulki, haka kuma bã shi yin ni'ima domin an ƙãra masa mulki. Sai dai dõmin Ya nũna ãdalci da falala ne kawai.
Ka ce: "Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa'an nan da sannu zã ku san wanda ãƙibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzãlumai bã zã su ci nasarã ba."
Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: "Wannan* na Allah ne," da riyãwarsu "Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne." Sa'an nan
* Sun kasance a cikin jahiliyya idan suka yi nõma kõ kuwa idan suka sami 'ya'yan itace, sai su sanya wani juz'i daga gare shi ga Allah, wani juz'i kuma ga gumãka. Abin da yake rabon gumaka, sai su tsare shi, kuma su lissafce shi. Idan wani abu ya fãɗi daga abin da aka ambace shi ga Samad, sai su mayar da shi zuwa ga rabõn gumãka, amma rabõn gumãkan, bã ya zuwa ga na Allah. Anã bayãr da rabon Allah ga miskĩnai, kuma rabõn gumaka ga matsaransu.
Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar* 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.
* Sunã turbuɗe 'ya'ya mata, dõmin tsõron talauci kõ dõmin tsõron kunya. Sai mai haihuwa ta haihu a bãkin rãmi, idan mace ta haifa, sai ta tũra ta cĩkin rãmin ta rufe, idan kuma namiji ne sai ta bar shi. Haka kuma kashe 'ya'ya, a kan bãkance da alwãshi, sunã ganin sa ibada ne.
Kuma sukace: "Waɗannan dabbõbi da shũka hanannu ne; bãbu mai ɗanɗanar su fãce wanda muke so," ga riyãwarsu. Da wasu dabbõbi an hana bãyayyakinsu, da wasu dabbõbi bã su ambatar sũnan Allah a kansu, bisa ƙirƙiren ƙarya gare Shi. Zai sãka musu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa.
Kuma suka ce: "Abin da yake a cikin cikkunan waɗannan dabbõbi kẽɓantacce ne ga mazanmu, kuma hananne ne a kan mãtan aurenmu. Kuma idan ya kasance mũshe, to, a cikinsa sũ abõkan tãrayya ne, zai sãka musu sifantãwarsu. Lalle ne Shĩ, Mai hikima ne, Masani."
Lalle ne waɗanda suka kashe ɗiyansu sabõda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasãra! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne sun ɓace, kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.
Kuma Shĩ ne Wanda Ya ƙãga halittar gõnaki mãsu rumfuna da wasun mãsu rumfuna da dabĩnai da shũka, mai sãɓãwa ga 'yã'yansa na ci, da zaituni da rummãni mai kama da jũna da wanin mai kama da jũna. Ku ci daga 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'yã'yan, kuma ku bãyar da hakkinSa a rãnar girbinsa, kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ, ba Ya son mafarauta.
Kuma daga dabbõbi (Ya ƙãga halittar) mai ɗaukar kãya da ƙanãna; Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, kuma kada ku bi zambiyõyin shaiɗan: LalLe ne shi, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne.
Nau'õ'i takwas daga tumãkai biyu, kuma daga awãkai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko mãtan biyu, ko abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Ku bã ni lãbãri da ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya.
Kuma daga rãƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, dõmin ya ɓatar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne Azzãlumai.
Ka ce: "Bã ni sãmu,* a cikin abin da aka yõ wahayi zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
* Bayãnin abũbuwan da aka haramta cinsu daga dabbõbi waɗanda Allah Ya hana, bã waɗanda al'ãda ta hana ba.
Kuma a kan waɗanda suka tũba (Yahũdu) Mun haramta *dukan mai akaifa, kuma daga shãnu da bisãshe Mun haramta musu kitsattsansu fãce abin da bãyukansu suka ɗauka, kõ kuwa kãyan ciki, kõ kuwa abin da ya garwaya da ƙashĩ wannan ne Muka sãka musu sabõda zãluncinsu, kuma Mu, haƙĩƙa, Mãsu gaskiya ne.
* Bayãnin abũbuwan da Allah Ya hana a kan Yahũdu, shi ma hanin an yĩ shi sabõda wani laifinsu ne.
Waɗanda suka yi shirki* zã su ce: "Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi."
* Wahayin shaiɗan zuwa ga mãsu shirki da hana dabbõbi da ƙãga wasu hukunce-hukunce. Kalmar gaskiya ce ake yin nufin ƙarya da ita, da bãyanin warware rikicin. Jũyar da maganar gaskiya dõmin a yi ƙarya da ita yanã sabbaba saukar azãba. Kuma dukan maganar da bã ta da asali ga Littãfi kõ sunna, to, bã gaskiya ba ce, bin ta nau'in shirki ne.
Ka ce: "Ku kãwo shaidunku, waɗanda suke bãyar da shaidar cẽwa Allah ne Ya haramta wannan." To idan sun kãwo shaida kada ka yi shaida tãre da su. Kuma kada ka bi son zũciyõyin waɗanda suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, da waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira, alhãli kuwa sũ daga Ubangijinsu suna karkacẽwa.
Ka ce: "Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta." wãjibi ne a kanku kada ku yi shirkin kõme da Shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatãwa, kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su, kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammãninku, kunã hankalta.
Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa.
Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa.
Sa'an nan kuma Mun bai wa Mũsã Littãfi, yanã cikakke bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah) da rarrabẽwa, daki-daki, ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu,* sunã yin ĩmãni da haɗuwa da Ubangijinsu.
* Mabiya Littãfin Mũsã watau Yahũdu, idan sun san cewa Alƙur'ãni kamar Attaura yake daga Allah aka saukar da shi, kuma Muhammadu Annabin Allah ne kamar Mũsã kuma sũ duka suna gaskata jũnã, sai su ji sauƙin ĩmãni da shi.
(Dõmin) kada ku ce: "Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan ƙungiya* biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance, daga karatunsu, haƙĩƙa, gãfilai."
* Ana magana da mãsu shirkin Larabawa, ƙungiyõyin biyu kuwa su ne Yahũdu da Nasãra, littãfin shĩ ne Attaura da Linjĩla.
Kõ kuwa ku ce: "Dã dai lalle mũ an saukar da Littãfi a kanmu, haƙĩƙa, dã mun kasance mafiya, shiryuwa daga gare su." To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, tã zo muku, da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Zã Mu sãka wa waɗanda suke finjirẽwa daga barin ãyõyinMu da mugunyar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na hinjirẽwa.
Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku* su je musu kõ kuwa Ubangijinka Ya je, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka ya je. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka yake zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba a gabãni, kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri, bã ya amfãninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne."
* Zuwan malã'iku dõmin karɓar rãyukansu, zuwan Allah dõmin yin hisãbin bãyi, zuwan sãshen ãyõyin Ubangiji shĩ ne fitõwar rãnã daga yamma da fitar Rãƙumar Sãlihu. Waɗannan abũbuwa duka idan sun auku a kan wanda bã shi da imani a gabãnin aukuwarsu, kuma ya zama yã aikata ayyukan alheri da shari'a ta umurce shi da yi, to, bã za a karɓi wani ĩmãninsa ba.
Lalle ne waɗanda* suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
* Bãyan bayãnin wanda bai yi ĩmani ba sai bayãnin sababin rashin karɓar ĩmãnin ya zo, sai kuma ya ci gaba da bayãnin cewa, kõ wanda ya yi ĩmãnin idan yã ƙãra wasa abũbuwa a cikin addĩni bisa ga abin da Allah Ya saukar, ta haka har mutane suka zama ƙungiya ƙungiya, kamar mãsu ɗarĩƙõƙi na tasawwufi, to, su ma Annabi bã ya tãre da su ga kõme dõmin sun kõma wa hanyar jahiliyya a lõkacin da wasu suke ƙãga hukunce-hukunce a kan mutãne, suka zama da yin haka nan abũbũwan bautãwa, kuma mãsu bin su suka zama mushirikai. Daga nan har zuwa ga ƙarshen sũrar duka ta'lĩƙi ne ga dukan abin da sũrar ta ƙunsa na tauhĩdin Rubũbiyya da taƙaitãwa ga bãyanin muhimman mas'alolin da ta ƙunsa. Saninta shi ne rũhin Addini.
Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su.
Ka ce: "Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni, ƙĩmantãwa (ga abũbuwa), mai aƙĩdar Ibrãhĩm, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
Ka ce: "Shin wanin Allah nake nẽma ya zama Ubangiji, alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce dõmin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?"
"Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya ku mãsu maye wa jũnaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sãshenku bisa ga sãshe da darajõji; dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku." Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggãwar uƙkũba ne, kuma lalle ne Shi, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
क़ुरआन के अर्थों का अनुवाद - हाउसा अनुवाद - अबू बक्र गूमी - अनुवादों की सूची
पवित्र क़ुरआन के अर्थों का हाउसा अनुवाद, अनुवादक : अबू बक्र मुहम्मद जोमी। संशोधन का काम रुव्वाद अनुवाद केंद्र की निगरानी में संपन्न हुआ। मूल अनुवाद सुझाव प्राप्त करने तथा मूल्यांकन एवं निरंतर उन्नयन हेतु उपलब्ध है।
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
खोज परिणाम:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".