Check out the new design

ශුද්ධවූ අල් කුර්ආන් අර්ථ කථනය - හවුසියානු පරිවර්තනය - අබු බකර් ජූමි * - පරිවර්තන පටුන

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

අර්ථ කථනය පරිච්ඡේදය: තාහා   වාක්‍යය:
فَأَخۡرَجَ لَهُمۡ عِجۡلٗا جَسَدٗا لَّهُۥ خُوَارٞ فَقَالُواْ هَٰذَآ إِلَٰهُكُمۡ وَإِلَٰهُ مُوسَىٰ فَنَسِيَ
"Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta."
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
أَفَلَا يَرَوۡنَ أَلَّا يَرۡجِعُ إِلَيۡهِمۡ قَوۡلٗا وَلَا يَمۡلِكُ لَهُمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا
Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni?
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
وَلَقَدۡ قَالَ لَهُمۡ هَٰرُونُ مِن قَبۡلُ يَٰقَوۡمِ إِنَّمَا فُتِنتُم بِهِۦۖ وَإِنَّ رَبَّكُمُ ٱلرَّحۡمَٰنُ فَٱتَّبِعُونِي وَأَطِيعُوٓاْ أَمۡرِي
Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umarnĩna."
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
قَالُواْ لَن نَّبۡرَحَ عَلَيۡهِ عَٰكِفِينَ حَتَّىٰ يَرۡجِعَ إِلَيۡنَا مُوسَىٰ
Suka ce ba zamu gushe ba muna bauta a gareshi ba har sai Musa dawo[1] @නිවැරදිකරු
Suka ce: "Ba zã mu gushe ba faufau a kansa munã mãsu lazimta,* sai Mũsã ya kõmo zuwa gare mu."
[1] Lazimta a kan bautawa maraƙin akwai wahala a cikinta dõmin haka aka kãwo wannan ƙissa sabõda a nũna cewa bautar Allah bãbu lazimta da wahala a cikinta duk abin da yake da wahala a cikinsa, bã addinin Allah ba ne. Akwai ĩ'itikãfi a cikin Musulunci wanda mafi yawansa kwãna gõma ne a cikin masallaci. Mutãnen Sãmiri ne suka fãra ibãda da kiɗa da rawa da wãƙã a cikin wurin ibãdarsu.
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
قَالَ يَٰهَٰرُونُ مَا مَنَعَكَ إِذۡ رَأَيۡتَهُمۡ ضَلُّوٓاْ
(Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace."
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
أَلَّا تَتَّبِعَنِۖ أَفَعَصَيۡتَ أَمۡرِي
"Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umarnina ne?"
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
قَالَ يَبۡنَؤُمَّ لَا تَأۡخُذۡ بِلِحۡيَتِي وَلَا بِرَأۡسِيٓۖ إِنِّي خَشِيتُ أَن تَقُولَ فَرَّقۡتَ بَيۡنَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَلَمۡ تَرۡقُبۡ قَوۡلِي
(Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba."
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
قَالَ فَمَا خَطۡبُكَ يَٰسَٰمِرِيُّ
(Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Kai Sãmiri!"
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
قَالَ بَصُرۡتُ بِمَا لَمۡ يَبۡصُرُواْ بِهِۦ فَقَبَضۡتُ قَبۡضَةٗ مِّنۡ أَثَرِ ٱلرَّسُولِ فَنَبَذۡتُهَا وَكَذَٰلِكَ سَوَّلَتۡ لِي نَفۡسِي
(Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini."
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
قَالَ فَٱذۡهَبۡ فَإِنَّ لَكَ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ أَن تَقُولَ لَا مِسَاسَۖ وَإِنَّ لَكَ مَوۡعِدٗا لَّن تُخۡلَفَهُۥۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ إِلَٰهِكَ ٱلَّذِي ظَلۡتَ عَلَيۡهِ عَاكِفٗاۖ لَّنُحَرِّقَنَّهُۥ ثُمَّ لَنَنسِفَنَّهُۥ فِي ٱلۡيَمِّ نَسۡفًا
(Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi,[1] sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa."
[1] Mũsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya ƙõne maraƙin ya sheke shi a cikin ruwan teku ya nũna ĩkon maraƙin ga kãre kansa daga wata cũta kuma da ƙarancinsa a cikin teku wadda take ɗaya ce daga cikin abũbuwan ĩkon Allah da suke iya gani, da lãlãcewar ibãdar mãsu bauta wa wanin Allah, a bãyan wahalarsu mai yawa ta lazimta a kansa.
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
إِنَّمَآ إِلَٰهُكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَسِعَ كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمٗا
Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci[1] dukkan kõme da ilmi.
[1] Allah Ya yalwaci dukan kõme da sani, watau Yanã aikata kõme da ilminsa kuma Yanã umurni da bauta Masa da ilmi, wanda Ya aiki Manzannin sa da shi.
අල්කුර්ආන් අරාබි අර්ථ විවරණ:
 
අර්ථ කථනය පරිච්ඡේදය: තාහා
සූරා පටුන පිටු අංක
 
ශුද්ධවූ අල් කුර්ආන් අර්ථ කථනය - හවුසියානු පරිවර්තනය - අබු බකර් ජූමි - පරිවර්තන පටුන

එය අබු බකර් මහමූද් ජුමි විසින් පරිවර්තනය කරන ලදී. රුව්වාද් පරිවර්තන මධ්‍යස්ථානයේ අධීක්ෂණය යටතේ එය වැඩි දියුණු කර ඇත. අදහස් ප්‍රකාශ කිරීමට ඇගයීමට හා තවදුරටත් වැඩි දියුණු කිරීමට මුල් පරිවර්තනය දෙස යොමු විය හැක.

වසන්න