To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci.
Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara.
Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah Ubangijin ku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?
Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da kãfirci ga bãyin Sa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku, kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata.
Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga 'yan wutã ne."
Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni.
Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩ Na waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi *ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba.
* Bãbu dalĩli da zai sanya mutum ya zauna a inda bã ya iya bautawa Ubangijinsa da kyau. Watau hijira zuwa wurin yardar Allah, wãjibi ne, sai idan dũniya ta zama haka a kõ'ina bãbu wurin tafiya, kõ kuma tafiya can da wuya ƙwarai tanã kallafa nauyin da zai zama wani laifin da ke daidai da rashin hijirar, to, sai mutum ya zauna, ya tsare kansa gwargwadon hãli.
"To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna."
Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyin Sa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa.
Waɗanda ke sauraren* magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali,
* Bãyin Allah na ƙwarai sũ ne waɗanda suke saurãren maganar Allah, sa'an nan su yi aiki da abin da yake mai bayyanannar ma'ana daga gare ta, kuma su bar abin da ba su gãne ma'anarsa ba bãyan sun yi ĩmãni da shi cewa daga Allah yake, kuma su tsarkake Allah daga abin da ba ya sifantuwa da Shi na sũrõrin hãlittarSa.
Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa.
Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna).
Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata bayyananna.
Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi, sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa.
Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba su sani ba.
To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai?
Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara."
Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba.
Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.
Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasun Sa, sai gãsu sunã yin bushãrar farin ciki.
Ka ce: "Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa."
Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su.
To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An bã ni ita ne a kan wani ilmi nãwa kawai." Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba.
Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba.
Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni.
Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩ Na waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra."
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin* ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.
* Yã yi bayãnin yadda zã a iya ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yin Sa da cewa, "ƙasã duka damƙarSa ce har zuwa ƙarshen sũrar. Wãtau yã dunƙule sũrar abũbuwan da zã su auku a Rãnar Ƙiyãma dõmin su bai wa mai hankali yadda suranta ikon yi na Allah Mai girma zai yiwu.
Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.
Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.
Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!"
Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama (a cikinta)."
Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijãrar ma'aikata.
Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu."
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
ผลการค้นหา:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".