แปล​ความหมาย​อัลกุรอาน​ - คำแปลภาษาเฮาซา - อบูบักร จญูมีย์ * - สารบัญ​คำแปล

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

แปลความหมาย​ อายะฮ์: (35) สูเราะฮ์: Al-Mā’idah
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱبۡتَغُوٓاْ إِلَيۡهِ ٱلۡوَسِيلَةَ وَجَٰهِدُواْ فِي سَبِيلِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi* a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara.
* Wasĩla ita ce dukkan aikin ibãda wanda zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangijinsa, amma da sharaɗin an gina shi a kan taƙawa. Kuma taƙawa ita ce bin Allah kamar yadda Ya yi umurni a bi Shi, ta hanyar manzon Sa kawai. Jihãdi yana cikin taƙawa amma Yã kõma ambatonsa ne domin muhimmancinsa. Shi kuma iri biyu ne: ƙararmi, watau yãƙin abokan gãbã na bayyane, da babba, shi ne yãƙin abokan gãbã na ɓoye, watau rai da shaiɗan. Wanda maƙiyinsa na bayyane ya kashe shi yã mutu shahĩdi, wanda maƙiyinsa na ɓoye ya kashe shĩ ya mutu fãsiƙi ko kãfiri watau shaƙiyyi.
ตัฟสีรต่างๆ​ ภาษาอาหรับ:
 
แปลความหมาย​ อายะฮ์: (35) สูเราะฮ์: Al-Mā’idah
สารบัญสูเราะฮ์ หมายเลข​หน้า​
 
แปล​ความหมาย​อัลกุรอาน​ - คำแปลภาษาเฮาซา - อบูบักร จญูมีย์ - สารบัญ​คำแปล

การแปลความหมายอัลกุรอานเป็นภาษาเฮาซา โดยอบูบักร มะหฺมูด จญูมี ได้รับการปรับปรุงแก้ไขอย่างสมบูรณ์โดยศูนย์การแปลรุววาด คำแปลต้นฉบับมีให้เพื่อการพัฒนา การประเมินอย่างต่อเนื่อง และการเสนอข้อชี้แนะ

ปิด