Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu.
Ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.*
* Tarbiyyar uba ga ɗansa.Yaro ƙarami anã renon sa da jawãbi mai laushi a fahimtar matsayin yãron.
"Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."
Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi* sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa** dõmin mãsu tambaya.
* Ãyõyi a nan, anã nufin hãlãye waɗanda suka zama darussa na kõyarwa ga mutãne dõmin tarbiyya ga yãra da manya na kõwane matsayi ga rãyuwar ɗan Ãdam. ** Yũsufu da ɗan'uwansa shaƙĩƙi, Binyãmĩnu, da sauran gõma. Babbansu ga shekaru, shi ne Raubĩlu, kuma sai Lãwiya. A cikin gidansa aka yi Annabãwa, sai Yahũza kuma shĩ ne shũgabansu a ra'ayi, shĩ ne uban sarãkunansu, sabõda haka sũnansa ya rinjãya a kan ƙabĩlar, aka ce musu Yahũdu.
A lõkacin da suka ce:* lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.
* Hĩrar yãra a tsakãninsu. Sunã tunãnin sõyayyar ubansu ga ɗayansu wanda bã ya cikinsu yanzu. Sunã tunãnin yadda zã su sãmi ãdalcin daidaitãwar so daga ubansu bãki ɗayansu. Ɗan'uwansu wanda ubansu yake so, watau Yũsufu, ya sãmi baƙin jini daga gare su dõmin ubansu yana sonsa. Sabõda haka shaiɗan yanã sanya musu tunãnin su yi zunubin rabuwa da shi, sa'an nan su tũba ga Allah.
Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
Suka ce: "Yã bãbanmu*! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?"
* Sun fara zartar da abin da suka shirya, watau ɗauke Yusufu daga gaban ubansa. Sun fãra da maganar da ubansu yake so game da su tattara da ɗan'uwansu ƙarami. Sunã muhãwara da ubansu sunã neman yardarsa don ya bar su su tafi da Yusufu.
To, a lõkacin* da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba."
* Suka cire rĩgarsa, suka jefa shi da gũga a cikin rĩjiya. Sa'an nan suka sanya wa rigarsa jinin wata dabba da suka yanka, dõmin ya zama alãmar cewa kerkeci ya cinye Yũsufu. Gã rĩgarsa ta ɓãci da jinin jikinsa, watau jinin shĩ ne alãmar yã mutu. Sai suka manta cewa kãfin kerkeci ya cinye yãro a cikin rĩgarsa, sai yã kekketa rĩgar tukun.
Suka ce: "Yã bãbanmu!* Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya!"_
* Muhãwararsu tãre da ubansu.Yã nũna baƙin ciki, amma kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: "Ã'a, zukatanku suka ƙawãta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantãwa."
Kuma wani ãyari* ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Yã bushãrata! Wannan yãro ne." Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.
* Ãyari ya je kusa da rĩjiyar Yũsufu, har suka kãma shi ya zama bãwa abin sayarwa a hannunsu.
Kuma suka sayar* da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.
* Ãyarin, sun tafi da shi, sun sayar da shi a kan kuɗi kaɗan, dõmin sun sani, shĩ bã bãwansu ba ne, tsintõ shi suka yi. Sabõda haka kõme suka sãmu game da shi, rĩba ce a gare su. Kuma gudun kada iyãyensa su gãne shi, su rasa kõme daga gare shi gabã ɗaya.
Kuma wanda ya saye shi daga Masar* ya ce wa mãtarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu, a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
* Yũsufu a gidan sarauta, kuma a cikin hãlin girma da ɗaukaka. Gidan Azĩzĩ Masar, watau firãyim Minista, babban wazĩrin Masar.
Kuma wadda yake *a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, "Yã rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!"
* Yũsufu yã shiga cikin fitinar uwar ɗãkinsa, Zalĩha. Yã mai da al'amarinsa ga Ubangijinsa wanda ya fitar da shi daga rĩjiya zuwa gidan sarautar Masar kuma Ya bã shi hukunci, watau Annabci da ilmi da Ya saukar masa na ibãda da mu'amãla. Ya sanar da shi halal da haram kuma ya sanya masa tsaro daga zunubi.
Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.
Kuma suka yi tsẽre* zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi."
* Idan namiji da mace sun haɗu, to, bã ya halatta ga namijin ya dõgara ga ilminsa na amanarsa, ya zauna tãre da fitinar Shaiɗan. Sabõda haka Yũsufu ya gudu, ta bĩ Shi da hãlin kãsãwar mutum ga hãlin so har bãkin kõfa. Suka haɗu da mijinta. Ta mayar da maganar rawãtsa (ƙarya) a kan Yũsufu. Shi kuma ya kãre kansa da maganar gaskiya. Sai shaida zã a nema.Tã himmantu da dũkarsa dõmin yã ƙi ya yi mata ɗã'a ga abin da take so daga gare shi alhãli yanã bãwanta, shĩ kuma yã himmantu da dũkarta dõmin ya tunkuɗe macũci. Alfãshar ita ce zina, cũtar kuwa ita ce dũka, dalĩlin Ubangijinsa shĩ ne bin sharĩ'ar Allah.
Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: *"Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata."
* Bãyar da shaida a kan al'ãda, mai bãyar da shaidar yanã gabãtar da ita da magana a kan Yusufu, dõmin a ganinsa tuhuma a kanta, tã fi karfi, kuma zumuntarsa da ita ba ta ɗauke shi ba ga karkatar da magana dõmin ya taimake ta.
Kuma waɗansu mãtã* a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna."
* Tsegumin mãtã a cikin gari da yadda mãtar Azĩz ta yi maganin tsegumin, ta hanyar yiwa mãtan liyafa. Mace bã ta kunyar mãtã 'yan'uwanta ga irin wannan fitina idan ta sãme ta, ita kaɗai, balle mãtã ga sũ duka sun kãmu a cikin tarkon da ya kãma ta. Sai ta gaya musu gaskiyar abin da ya auku a tsakãninta da Yũsufu, a bãyan ta rãma zargin da suka yi mata.
Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja!"
Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge* ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu."
* A cikin maganar mãtar Azĩz a tsakãnin mãtã bãbu wata kunya, dõmin tã nũna kãsãwarsu. Kuma akwai tsõratarwa ga Yũsufu idan bai yi mata ɗã'a ba ga bukãtarta gare shi.
Ya ce: "Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai."
Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi.* ¦ayansu ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa."
* Yũsufu a cikin kurkuku tare da abõkan shigarsa kurkukun. Kuma yanã fassara mafarki a bãyan kiransa zuwa ga Addini.
Ya ce: "Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa,* kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne."
* Kõwane irin abin ne kãfin in gan shi da idõna, zan iya gaya muku nau'insa, kamar yadda Ĩsa ya ce: " Inã bã ku lãbãrin abin da kuke ci a gidãjenku." A Sũrar Ãl Imrãna ãyã ta 49.
"Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa."
"Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
"Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shãyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa."
Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, "Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka." Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunãwar Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru.
Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, nã yi mafarki*; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa."
* Mafarkin sarki wanda zai zama sanadin fitar Yũsufu daga kurkuku. Wannan yanã nũna ba akeɓance yin mafarki ga Musulmi kawai, kãfiri ma yanã yin mafarki. Bã a iya fassara mafarki sai da ilmin Alƙur'ãni da Hadisi da kuma sanin al'ãdun mutãne. Mafarki bã ya zama hujja sai idan wani annabi yã fassara shi.
"Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani."
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lõkacin da manzo ya je masa (Yũsufu), ya ce: "Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidin su."
Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mãtar Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya* ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya.
* Da wannan magana ta mãtarAzĩz Zalĩha anã fahimtar ita tã musulunta ta hannun Yũsufu kãfin a ɗaure shi.
"Kuma bã ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina." To, a lõkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce."*
* Maganar da Yusuf ya gayã wa sarki lõkacin da ya je masa ba a faɗe ta ba, sai dai an nuna ta ƙãyatar da shi har ya yabe shi da cewa shi mai daraja ne amintacce.
Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa* yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa.
* Lõkacin da Yũsufu yanã aikin tattalin arzikin ƙasa a cikin shekarar wadãta, ya Mallakeƙasar Masar duka a lõkacin da wahala da yunwa suka auku.
Kuma 'yan'uwan* Yũsufu suka jẽ, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya gãne su, alhãli kuwa su, sunã mãsu musunsa.
* 'Yan'uwan Yũsufu sun zo sunã neman awo a gunsa, ya gãne su dõmin baƙauye kõ matalauci bai faye canja kamanninsa ba, amma sũ, ba su gane shi ba, sabõda haibar mulki da kwarjinin halittarsa a bayan ya zama babban mutum ga idonsu a inda bã su zaton sa.
Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani ɗan'uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma'auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?"
To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: "Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan'uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu lũra da Shi ne."
Ya ce: "Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama."
Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: "Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙãra awon kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki."
Ya ce: "Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku." To, a, lõkacinda suka yi mãsa alkawari, ya ce: "Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa."
Kuma ya ce: "Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam,* kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara."
* Yãƙũbu ya umurci ɗiyansa su shiga garin, ta ƙõfõfi dabam- dabam, yanã nũna cewa yanã gudun kyawunsu da yawansu zai ja hankalin mutãne zuwa gare su. A cikin mutãne akwai mãsu kambun baka da mugun nufi kõ da yake Yãƙũba a cikin hãlin haka ya aza tawakkalinsa ga Allah. Ya yi abin da yake zaton alhħri ne, wanda bai saɓa wa sharĩ'a ba. Amma kuma yã yi haka ne a kan wani ilmi da Allah Ya sanar da shi cewa a wannan fitar tãsu ce Allah zai yi sanadin sãke sãduwarsu da Yũsufu, sabõda haka ya umurce su da su shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, dõmin mutum shi kaɗai yã fi sãmun dãmar ta'ammalin ganin mutãne da abũbuwa. Kuma ta yin haka, yanã tsammãnin waninsu zai ga Yũsufu.
Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu, ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: "Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
Sa'an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kãyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa," Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne."
Suka ce: "Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa,* kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai."
* Shari'ar Banĩ yã'aƙũbu ita ce anã bautar da ɓarãwõ shekara guda. Wannan shĩ ne shari'ar da Tũrãwa suka ɗauka suka mayar da ita ɗaurin kurkuku da bautar da ɓarãwo a cikin mudda ayyananna.
To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani.
Suka ce: "Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye* ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa."
* 'Yan'uwan Yũsfu sun faɗi cewa ɗan'uwan Binyaminu ya taɓa yin sãta, dõminsu nũna cewa a wajen ubansu tsarkakakku ne daga yin sãta. Shi kuma wanda ya yi sãtan ya gade ta ne daga wajen uwarsa, dõmin wani shaƙĩƙinsa(Yũsufu) ya taɓa yin sãta. To, sai Yũsufu ya ce a ransa: "Kũ ne dai mafi sharrin mutãne, Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffintãwa." Asalin wannan magana wata goggonsa ce (Shi Yũsufu) ɗiyar Is'hãƙa, ta riƙe shi, yanã yaro, har a lõkacin da ubansa (Yãƙũbu) ya so ya karɓe shi daga gare ta, sai ta yi kaidin sanya kãyan sãta a cikin rigarsa (Yũsufu) dõmin ta hana uban ɗaukarsa. A wata ruwaya kuma an ce shi (Yũsufu) ya ɗauke wani mutum mutumi ne na zĩnãri (gunki) ya karairaya shi. Don haka 'yan'uwansa suke jingina sãta a gare shi.
Suka ce: "Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa. Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa."
Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa.* Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta."
* 'Yan'uwan Yũsufu sun yanke tsammãnin sãmun Binyãminu daga sharĩ'a, sun kõma sunã gãnãwa a tsakãninsu. Sai dai waɗannan ɗiyansu ne domin su, suna Masar.
"Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba."
Ya ce: "Ã'a, zukatanku sun ƙawãta wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyãwo, akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã ɗaya (Yũsufu da 'yan'uwansa). Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima."
"Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu* da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar Allah fãce mutãne kãfirai."
* Anan Yãƙũbu yã bayyana irin ilmin da Allah Ya sanar da shi, cewa Yũsufu yanã nan da ransa, kuma sun yi kusa su sãdu da jũna.
Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: "Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. "*
* Wannan ya nũna ba a haramta sadaka ba ga Annabãwan da suka gabãta, sai ga Annabinmu Mahammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, shĩ da danginsa na kusa aka hana wa cin sadaka.
Saka ce: "Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa."
Kuma, a lõkacin da ãyari* ya bar (Masar) ubansa ya ce: "Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba."
* Yãƙũba da jĩkõkinsa. Yanã gaya musu, cewa yanã shãƙar ƙanshin Yũsufu, su kuma suna jingina shi ga ruɗewar tsũfa dõmin rabonsa da Yũsufu shħkara talãtin da biyar zuwa Arba'in.
Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?"
Suka ce: "Yã ubanmu!* ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure."
* Ɗiyan Yãƙũbu sunã iƙrãri da laifinsu, sunã neman Allah Ya gãfarta musu gaba ɗaya. Ubansu yanã jinkirta nema musu gãfara gun Allah har a lõkacin asuba kõ kuwa daren Jumma'a dõmin ya yi rõƙo a lõkacin karɓar addu'a. Wannan yã nũna anã iya neman mai albarka kõ wani mutum yayi wa wani mutum Addu'a.
Sa'an nan a lõkacin* da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: "Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu."
* Yũsufu ya sãdu da ubansa da uwarsa. A Larabci anã rinjãyar da uba a kan uwa, a ce ubanni biyu, kuma ga Hausa anã rinjayar da wa a kan uba, a ce uwãye biyu.
Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada.* Kuma ya ce: "Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, Shĩ ne Masani, Mai hikima."
* Sujada idan ta zama da umurnin Allah ne ga kõwa, to, ba ta da laifi duk yadda take, amma idan an yi ta bã inda Allah Ya ajiye ta ba, to, tã zama kãfirci. A Musulunci gaisuwa da dũƙãwar kai haram ce, waɗansu Malamai sun ce idan ba ta kai ga rukũ'i ba, makarũhi ce, amma idan ta kai ga rukũ'i tã zama harãmun ga duka mãlamai, wãtau ijmã'in Malamai sun haramta dũƙãwar da ta kai ga rukũ'i.
"Yã Ubangijina* lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
* Yũsufu yanã addu'a a ƙarshen rãyuwarsa, yanã neman Allah Ya cika masa da imãni.
Wannan daga* lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci.
* Ƙarfafãwa da ƙãrin tambĩhi daga abin da sũrar ta ƙunsa, daga nan har zuwa karshenta.
Ka ce: "Wannan ce hanyãta;* inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."
* Bin hukuncin Allah kamar yadda ƙissar Yũsufu ta nũna cewa, a ƙõwane hãli mutum ya kasance akwai yadda Allah Ya yi umurni a wannan hãlin da a bĩ Shi, wanda ya bi umurnin Allah, to, zai ɗaukaka a dũniya kuma Allah bã zai tõzartar da lãdarsa a Lãhira ba.
Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta?
Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke so, kuma bã a mayar da azãbarMu daga mutãne mãsu laifi.
Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.
Salin ng mga Kahulugan ng Marangal na Qur'an - Salin sa Wikang Hausa ni Abubakr Gumi - Indise ng mga Salin
Salin ng mga Kahulugan ng Marangal na Qur'an sa Wikang Hausa. Isinalin ito ni Abubakr Mahmoud Gumi. Inilathala ito ng King Fahd Glorious Quran Printing Complex sa Madinah Munawwarah, imprenta ng taong 1412 H. Isinagawa ang pagtatama nito sa pangangasiwa ng Sentro ng Rowad sa Pagsasalin. PInapayagan ang tumingin sa orihinal na salin sa layuning magpahayag ng pananaw, magsiyasat, at patuloy na paglinang.
Contents of the translations can be downloaded and re-published, with the following terms and conditions:
1. No modification, addition, or deletion of the content.
2. Clearly referring to the publisher and the source (QuranEnc.com).
3. Mentioning the version number when re-publishing the translation.
4. Keeping the transcript information inside the document.
5. Notifying the source (QuranEnc.com) of any note on the translation.
6. Updating the translation according to the latest version issued from the source (QuranEnc.com).
7. Inappropriate advertisements must not be included when displaying translations of the meanings of the Noble Quran.
Mga Resulta ng Paghahanap:
API specs
Endpoints:
Sura translation
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/sura/{translation_key}/{sura_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified sura (by its number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114)
Returns:
json object containing array of objects, each object contains the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".
GET / https://quranenc.com/api/v1/translation/aya/{translation_key}/{sura_number}/{aya_number} description: get the specified translation (by its translation_key) for the speicified aya (by its number sura_number and aya_number)
Parameters: translation_key: (the key of the currently selected translation) sura_number: [1-114] (Sura number in the mosshaf which should be between 1 and 114) aya_number: [1-...] (Aya number in the sura)
Returns:
json object containing the "sura", "aya", "translation" and "footnotes".