《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。 * - 译解目录

XML CSV Excel API
Please review the Terms and Policies

含义的翻译 段: (27) 章: 玛仪戴
۞ وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ ٱبۡنَيۡ ءَادَمَ بِٱلۡحَقِّ إِذۡ قَرَّبَا قُرۡبَانٗا فَتُقُبِّلَ مِنۡ أَحَدِهِمَا وَلَمۡ يُتَقَبَّلۡ مِنَ ٱلۡأٓخَرِ قَالَ لَأَقۡتُلَنَّكَۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِينَ
Kuma karantã musu* lãbãrin ɗiya biyu** na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne."
* Ƙuraishawa ko kuwa al'ummarka. ** Ɗiyan Ãdamu, biyu, Ƙãbĩla da Hãbĩla. Asalin maganar kamar yadda aka ruwaito, mãtar Ãdamu, Hauwa'u, tana haifuwar namiji da mace a kowane ciki, wajen aure sai a shirɓata dõmin bãbu wasu mutãne sai su. Sai Ƙabĩla ya ƙi yarda a bai wa Hãbĩla 'yar'uwarsa, har Ãdam ya sanya su yin baiko da abin sana'arsu. Ƙãbĩla manõmi ne, ya bãyar da munãna daga kãyan nõmansa, shi kuma Hãbĩla ya bãyar da rãgo mai kyau dõmin sana'arsa kiwo ne. Sai wuta ta sauko ta ɗauki rãgon Hãbĩla, alãmar karɓa. Wannan kuwa ya ɗauki Ƙãbĩla ga tunãnin kashe shi. Laifi guda yana sabbaba wasu laifuka mãsu yawa.
阿拉伯语经注:
 
含义的翻译 段: (27) 章: 玛仪戴
章节目录 页码
 
《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。 - 译解目录

古兰经豪萨文译解,艾布·拜克尔·麦哈穆德·朱米翻译。由拉瓦德翻译中心负责校正。附上翻译原文以便发表意见、评价和持续改进。

关闭